Kungiyar Alkalan Kotunan Majistare ta Kasa reshen Jihar Gombe ta koka kan irin tarin matsalolin da mambobinta ke fuskanta, musamman na rashin abubuwan more rayuwa.
Shugaban Kungiyar reshen Jihar Gombe, Muhammad Tukur Jungudo ne ya bayyana hakan a lokacin da kungiyar su ta shirya wa Alkalan kotunan Majistare da suka yi ritaya da wadanda suka samu canjin wajen aiki a Jihar liyafar karramawa a Gombe.
Ya ce an bar kotunansu a baya, ba kamar yadda takwarorinsu na sauran Jihohi suke ba wajen rashin ofisoshi da gidajen kwana da motocin hawa da kuma kin basu rancen sayen motocin da na kujeru da sauran su.
“Ina iya tunawa yadda mai shari’a Becky Samuel ta yi ta fadi-tashi wajen ganin shugaban Karamar Hukumar Funakaye ya samar da makewayi a Kotun Majistaren da ke garin Bajoga, sannan shi ma Mai Shari’a Abubakar Ahmad Daba, ya yi amfani da kudinsa wajen gina makewayi a wannan kotun, dukkansu a lokacin da suke shari’a a lokuta daban-daban a kotun,” inji shi.
Shugaban ya kuma ce har yanzu wasu kotunan Majistarena Jihar na fama da matsalar makewayi, duk kuwa da irin muhimmancinsa ga kotunan.
Ya kuma ce Alkalan ne suke nemawa kan su bashin bankuna don sayen ababen hawa wanda idan ba haka ba sai dai su rika shiga motocin haya ko su hau Achaba dan zuwa wajen aiki.
Hakan ya yana da matukar hatsari a garesu.
Da yake tsokaci kan korafe-korafen nasu, Alkalin-alkalan Jihar na riko Mai Shari’a Mu’azu Pindiga, ya ce alkalan da suka yi ritayar suna da sauran karfi da gudunmawar da za su bayar.
Mai Shari’a Pindiga ya jinjina wa kungiyar Alkalan bisa shirya gagarumar liyafar, inda ya ce hakan abu ne mai kyau.
Da take jawabin godiya a madadin wadanda suka yi ritayar, Mai Shari’a Becky Samuel ta yabawa kungiyar tasu saboda karramar.
Alkalan da suka yi ritayar da wadanda suka samu canjin wajen aikin da aka karrama sun hada da Mai Shari’a Dija Abubakar Kole da Abubakar Ahmad Daba da Becky Samuel da Nana A’isha Bappa da Lilian Dorothy Oteri da kuma Obel Yaji.