✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tarihin tashe a kasar Hausa

Tarihin tashe, asalin kalmar, muhimmancinsa da sauran abubuwan da ya kamata ku sani,

Tashe wata al’ada ce da ake gudanarwa daga kwana 10 na biya na watan Ramadan har zuwa daren sallah.

Masu tashe, yawancinsu kananan yara, cikin shiga ta ban dariya, sukan zaga kwararo-kwararo a unguwanni da kasuwanni suna nishadantar da mutane da abubuwan barkwanci da ba’a da dai sauransu domin debe musu gajiyar azumi.

A yayin da aka shiga lokacin gudanar da tashe, ’yan sanda sun takaita yin sa saboda wasu dalilai.

Aminiya ta binciko muku asali da tarihi da sauran muhimman abubuwa game da wannan al’ada da ke gudana a cikin watan Ramadan mai alfarma, a kasar Hausa.

Asalin kalmar tashe

Masana sun bayyana cewa asalin tashe ana yin sa ne da dare, kuma bakuwar al’ada ce da malam Bahaushe ya samu daga baya.

Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza malami ne a Sashen Koyar da Harsunan Najeriya a Jami’ar Usmanu Danfodio da ke Sakkwato.

Ya bayaya wa Aminiya cewa, “Kalmar tashe ta samo asali ne daga a tashi, wato a tashe su daga barci.”

Tarihin tashe

Ita dai wannan al’ada a cewar Farfesa Bunza, ba a san bahaushe da ita ba sai bayan zuwan Musulunci kasar Hausa.

Tashe “Ya samu tarihin Bahaushe ne a watan azumi na Ramdan; wannan ya nuna bakon abu ne, domin gabanin zuwan Musulunci babu,” inji shi.

Ya ce masana al’ada na ganin tashe ya samo asali ne daga Daular Andalus, “Can ne Musulmi suka kusa kusanta da al’adu, domin da kidin taushi da tashe duk daga can suka samo asali.”

Dalilin yin tashe

Farfesa Bunza ya bayyana cewa asalin makasudin yin tashe shi ne a tayar da mutane daga barci su yi sahur a watan azumin Ramadan.

“Har yanzu [a Daular Andalus] suna yin tashen, wanda za a tayar da mutane da dare domin su samu su yi sahur.”

Daga baya “Abin ya koma wasan yara na jan hankalin jama’a da faranta musu rai da debe musu gajiya da takaici da wahala.”

Tashe a al’adar Bahaushe

A kasar Hausa akan fara yin tashe ne a 10 na tilas, wato kwana 10 na biyu cikin watan Ramadan domin sanya wa mutane nishadi.

Bahaushe ya kasa watan azumin Ramadan zuwa gida kuna: 10 Na Marmari, 10 Na Wuya, da kuma 10 Na Dokin Sallah.

Malamin ya bayyana cewa Bahaushe ya zabi 10 Na Wuya a matsayin lokacin fara tashe.

“10 Na Marmari Bahaushe ya ga bai ma kamata a yi tashe a lokacin ba, sai an shiga 10 Na Wuya, lokacin an dan fara gajiya da azumin.

“Saboda haka sai a rika yin tashe ana sa mutane fara’a da farin ciki, su kuma suna ba da kyauta da sadaka.”

Muhimmancinsa

Game da hikima da kuma amfaninsa, Farfes Bunza ya ce tashe kan nuna duk yanayi da mutane suke ciki a shekarar, kuma akwai darasi a cikinsa.

“Su yaran suna kokarin su bayyana halayya da duk wani yanayi da mutane suke ciki.

“Da za a saurari tashen yaran za a ga manyan maganganu ne da manya suka sa musu a baki.

Ya ce, “Cikin tashe ana gina wa yara kunya, kokari, kwazo, son gaskiya, son juna da sauransu.”

Tasirin tashe

“Malamai sun gaya mana cewa tashe shi ne musabbabin samuwar wasu fitattun mawakan kasar Hausa; daga wakokin tashe suka samu shahara, maza da mata.

“Saboda haka tashe wani abu ne na sada zumunci da kokarin lurar da mutane [irin] halin da ake ciki, da yadda ya kamata a fuskance su.

“Don yanzu ga shi nan na ga wata yarinya tana tashe a kan bilicin, ba mamaki a samu wata kuma tana tashe a kana ta’addanci.

“Mu nuna wa mutane cewa ta’addanci fa ba zai yiwu ba, dole mu zauna lafiya; saboda haka yaran nan karatu ne suke mana mai zurfi.”

An ji kunya: Hana tashe a Kano

Da yake tsakoci kan haramta tashe da dare a Jihar Kano, malamin jami’ar ya ce “Amma dai hukuma ta ji kunya da ta hana wa yara yin tashe da dare,” ganin cewa jihar, “ita ce cibiyar da ake akasarin nazarin abubuwan da ake yi na Hausa; kuma Kano tana rike da al’adunmu manya-manya.

“Ai tashen yara shi ne tashe kuma sakon da suke aikawa ya fi muhimmanci ga barin shi. Ba su ne musabbabin ta’addanci ba.”

“Abin da ya kamata shi ne a yi amfani da yaran su nuna munin ta’addanci, su nuna muhimmancin samun walwala musamman a kasa irin Kano inda tattalin arziki suke bunkasa.

“Da an sa wa yara ido da sun fito da hanyoyin tashen zaman lafiya da yawa a Kano da ba a san da su ba.”

Ba mu hana tashe ba -’Yan sanda

Sai dai kuma Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta bayyana cewa ba ta hana yi tashe gaba daya a jihar.

Kakakin Rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce, “Ba hana tashe aka yi ba [gaba daya]; tashe irin wanda yara kanana suke yi da rana ko da safe a gidan iyayensu da makwabta, ba a hana wannan ba, haka kuma wanda ‘yan mata suke yi.”

Ya bayyana wa Aminiya cewa tashen dare ne aka haramta a jihar, saboda bata-gari kan shiga rigar ’yan tashe su aikata miyagun laifuka.

“Tashen da ake yi da dare, wanda yawanci da ma ’yan daba ne suke fakewa da wadannan tashe, suna fitowa da makamai,” shi aka harmata, inji shi.

Ya shaida wa shirin Najeriya a Yau wanda Aminiya take gabatarwa a intanet cewa a irin lokacin da masu tashen dare suke gudanarwa, ’yan daba, “Suna fitowa da makamai, za ka gan su daruruwa — da ma sun fito ne kawai domin fashin kayan mutane, sata da yin ta’adi.

“Ko motoci mutane suka samu a kan titi suna farfasawa; Wannan ne ya sa daga bayanan da aka samu aka dakatar da irin wannan nau’i na tashe,” kamar yadda ya bayyana.

Hakan na zuwa ne dai bayan Aminiya ta kawo rahoto a ranar Litinin cewa Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta haramta yin tashe, bisa hujjar bata-gari, kamar masu kwacen waya kan fake da shi domin aikata barna a cikin al’umma.