A wannan Lahadin Allah Ya yi wa Mai Martaba Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya OON rasuwa.
Sarkin ya rasu ne bayan ya shafe shekaru 47 kan gadon sarauta, wanda kuma shi ne Sarki mafi daɗewa kan karagar mulki a tarihin Masarautar Ningi.
Wata sanarwa da sakataren Masarautar Ningi Alhaji Usman Sule Magayakin Ningi ya fitar ta ce za a yi wa Sarkin jana’iza da misalin karfe 4:00 a fadarsa da ke cikin garin Ningi.
An haifi Alhaji Danyaya a shekarar 1936, kuma ya samu gogewa a fannoni daban-daban kafin hawa gadon sarauta a shekarar 1988.
Ya yi makarantar firamare ta Ningi a tsakanin shekarar 1941 zuwa 1946, sannan ya yi karatun sakandare a Bauchi daga 1946 zuwa 1951 kafin ya wuce Makarantar Kula da Tsaftar Muhalli ta Kano a shekarar.
Daga nan kuma ya tafi Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda ya sami shaidar difloma a fannin harkokin tafiyar da ayyukan gwamnati.
Ya kasance mamba na Majalisar Masarautar Ningi daga 1956 zuwa 1960, mai ba da shawara ga Ma’aikatar Lafiya daga 1958 zuwa 1959 kuma memba na Majalisar Mulkin Lardi na Ningi daga 1954 zuwa 1956.
Sarki Danyaya ya kasance mashawarci kan ayyukan ’yan sanda da gidajen yari daga 1959 zuwa 1960, inda aka naɗa shi Hakimin Lardi da kuma Sarautar Chiroman Ningi.
Ya yi aiki a Hukumar Tallace-Tallacen Arewacin Nijeriya a matsayin Mataimakin Shugaban Kasuwanci, daga baya ya zama Mataimakin Manaja mai kula da Gusau da Kauran Namoda a shekarar 1968.
Sai dai saboda kwazonsa, ba a jima ba ya zama Manaja a Daffon da Dalar Gyada na Maiduguri a shekarar 1969, kuma a shekarar 1970 aka nada shi Manaja mai kula da Gombe da kuma Biu.
Sai dai an yi masa canjin aiki a shekarar 1974, kuma daga ƙarshe ya zama mai kula da shiyyar Yola, Mubi da Mambila.
A shekarar 1976 ce aka nada shi manajan rikon yanki mai kula da Hukumar Kasuwancin Jihohin Arewa maso Gabas.
Saboda gogewarsa, ya zama Shugaban Kwamitin Rarraba kadarori tsakanin Hukumomin Tallace-Tallacen Binuwai da Filato.
Mamba ne mai himma a Kungiyar Jama’atu Nasrul Islam kuma mamba a kwamitocinta na Kudi da kwamitin tara Zakka.
Ya kasance memba a Majalisar Jihohi ta Kasa mai wakiltar Majalisar Sarakunan Jihar Bauchi daga 1979 zuwa 1983, kuma ya zama shugaban riko na Hukumar Daraktocin a Rusasshen Bankin Inland Nigeria Plc daga shekarar 1988 zuwa 1991.
Ya kuma yi aiki a matsayin Darakta na Hukumar Raya Kogin Hadejia-Jama’are tsakanin 1989 zuwa 1991.
Bayan haka, Sarkin ya kasance mamba a taron tsarin mulki na kasa tsakanin 1994 zuwa 1995.
Haka kuma, ya kasance mamba a kwamitin sarakunan gargajiya na masu hangen nesa daga 1996 zuwa 1997.
Ya kasance Shugaban Hukumar Rijistar Ma’aikatan Lafiya ta Muhalli ta Najeriya (EHORECON) tun daga shekarar 2004.
An karrama Sarkin da lambar yabo ta kasa ta Jami’in Hukumar Neja, (OON).
Sarki Yunusa ya kuma rike mukamon Amirul Hajj na Jihar Bauchi a 2022.
Za a daɗe ana tuna shi saboda dagewarsa da faɗar gaskiya da adalcinsa da kuma son jama’arsa. Allah Ya ji ƙansa Ya gafarta masa.