An naɗa Alhaji Haruna Yunusa Danyaya a matsayin sabon Sarkin Ningi.
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ne ya amince da naɗin Haruna Danyaya, wanda shi ne babban ɗan marigayi Sarkin Ningi da ya rasu a matsayin sabon Sarkin Ningi na 17 mai daraja ta ɗaya.
Bayanin haka na ƙunshe cikin sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai, Kwamared Mukhtar Muhammad Gidado ya fitar a ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce “gwamnan ya yi amfani da ikon da sashe mai lamba Cap. 24 na 3 (1) na dokokin Jihar Bauchi ta Nijeriya ta ba shi kan naɗin Sarakuna na shekarar 1991
“Haka kuma nadin ya yi daidai da shawarwarin da masu zaɓen sabon sarki suka bayar.
“An miƙa sanarwar naɗin sabon sarkin a wata takarda mai ɗauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin Bauchi, Barista Ibrahim Muhammad Kashim.”
Sanarwar ta ce, “Gwamnatin Jihar Bauchi ta nuna amincewarta da yadda sabon sarkin zai ci gaba da ayyukan da mahaifinsa da Allah ya yi wa rasuwa yake yi wajen samar da haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba a Masarautar Ningi da Jihar Bauchi baki ɗaya.
Sanarwar ta kuma ba da tabbacin cewa gwamnati za ta ci gaba da jajircewa wajen tallafa wa masarautu a jihar domin “suna taka muhimmiyar rawa wajen wanzar da zaman lafiya da ci gaban al’ummarmu.”
Gwamna Bala ya yi addu’ar Allah Ya jikan marigayi Sarki Ningi, yana kuma mai miƙa gaisuwar ban girma da addu’o’in samun lafiya, tsawon rai da samun nasarar sabon sarkin.
Sabon Sarkin Ningi, Alhaji Haruna Yunusa Danyaya, an haife shi ne a garin Ningi a shekarar 1956 kuma kafin yanzu shi ne Chiroman Ningi.
A Lahadin makon jiya ce Allah Ya yi wa mai martaba Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya rasuwa a birnin Kano.
Rasuwar Sarkin ta girgiza jama’ar Jihar Bauchi da Nijeriya baki ɗaya.
Sarkin wanda ya rasu yana da shekara 88 a duniya, ya bar babban giɓin da zai yi wuyar cikewa, kasancewarsa ɗaya daga cikin sarakuna masu daraja ta ɗaya kuma ɗaya daga cikin sarakuna mafiya daɗewa a karagar mulki da ake girmamawa a kasar nan.