Rasuwar Mai martaba Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya a ranar Lahadin da ta gabata a birnin Kano, ta girgiza jama’ar Jihar Bauchi da Nijeriya baki ɗaya.
Sarkin wanda ya rasu yana da shekara 88 a duniya, ya bar babban giɓin da zai yi wuyar cikewa, kasancewarsa ɗaya daga cikin sarakuna masu daraja ta ɗaya kuma ɗaya daga cikin sarakuna mafiya daɗewa a karagar mulki da ake girmamawa a kasar nan.
Marigayi Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya Sarki mai fada-a-ji, kuma uba ne dattijo, sauran mazan-jiya da ake dogaro da su wajen samun shawarwari da shiryarwa a masarautun Nijeriya.
An shaidi marigayi Sarkin da kasancewa mutum mai fadar gaskiya cikin hikima da tattausar murya, tare da fadar gaskiya ba tare da tsoro ko shakka ba, inda yake haɗa wa mutum da cewa ka yi haƙuri iya gaskiyar ke nan.
Sarkin Ningi wanda ya je asibiti a kasar Saudiyya, ya dawo Nijeriya bayan shafe kwanaki a can, da ya iso Kano a kan hanyarsa ta dawowa gida Ningi, sai aka lura jikinsa ba ƙarfi sosai, inda aka nemi ya kwana biyu a Kano, ya huta ashe a can ajalinsa yake.
Ya rasu ne bayan ya shafe shekara 46 a kan karagar mulki.
Sarki Yunusa Danyaya ya zama Sarki mafi daɗewa a kan karagar mulki a tarihin Masarautar Ningi.
An haife shi a 1936, inda ya halarci makarantar firamare ta Ningi a tsakanin 1941 zuwa 1946, sannan ya yi makarantar sakandare ta Bauchi daga 1946 zuwa 1951 kafin ya wuce Makarantar Kula da Tsaftar Muhalli ta Kano a 1951.
Daga nan ya tafi Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, inda ya samu shaidar difloma a fannin harkokin tafiyar da ayyukan gwamnati.
Ya kasance mamba na Majalisar Masarautar Ningi daga 1956 zuwa 1960, sai Mai ba da Shawara ga Ma’aikatar Lafiya daga 1958 zuwa 1959 kuma mamba na Hukumar En’e ta Ningi daga 1954 zuwa 1956.
Sarki Yununsa Danyaya ya kasance mashawarci kan ayyuka ’yan doka da gidajen yari daga 1959 zuwa 1960 kuma an nada shi hakimi da sarautar Chiroman Ningi, inda ya fara tafiyarsa ta sarauta.
Ya yi aiki a Hukumar Tallace-tallace ta Arewacin Nijeriya a lokacin a matsayin mataimakin shugaban kasuwanci, daga baya ya zama mataimakin manaja, mai kula da Gusau da Kauran Namoda a 1968.
Ƙwazonsa ya sa aka naɗa shi Manajan Daffon Tara Dalar Gyada a Maiduguri a 1969 kuma a 1970 aka nada shi Manaja Mai kula da Gombe da Biu. An yi masa canjin aiki a 1974, kuma a karshe ya rike Yola da Mubi da Mambila.
A 1976, an nada shi rikon Manajan Yanki Mai kula da Hukumar Kasuwanci ta Jihohin Arewa maso Gabas.
Saboda gogewarsa, ya zama Shugaban Kwamitin Rarraba Kadarori a tsakanin hukumomin tallace-tallace na Binuwai da Filato.
Mamba ne a Kungiyar Jama’atu Nasril Islam kuma mamba a kwamitocinta na kudi da Babban Kwamitin Tara Zakka.
Ya zama mamba a Majalisar Jihohi ta Kasa mai wakiltar Majalisar Sarakunan Jihar Bauchi daga 1979 zuwa 1983 kuma ya zama Shugaban Riko na Hukumar Daraktocin Rusasshen Bankin Inland Nigeria Plc a tsakanin 1988 zuwa 1991.
Ya yi aiki a matsayin Darakta a Hukumar Raya Kogin Hadeji-Jama’are a tsakanin 1989 zuwa 1991.
Bayan haka, Sarkin ya zama mamba a Taron Tsarin Mulki a tsakanin 1994 zuwa 1995 kuma mamba a Kwamitin Sarakunan na Kwamitin Dattawa a tsakanin 1996 zuwa 1997.
Ya zama Shugaban Hukumar Rajistar Ma’aikatan Lafiyar Muhalli ta Nijeriya (EHORECON) tun daga shekarar 2004, Sarki Yunusa ya kuma rike mukamin Amirul Hajj na Jihar Bauchi a 2022.
An karrama marigayi Sarkin da lambar yabo ta kasa ta OON.
Garin Ningi ya cika makil da jama’a daga ciki da wajen masarautar, wadanda suka halarci jana’izar marigayi Sarkin Yunusa Danyaya.
Babban Limamin Ningi, Dokta Muhammad Umar ne ya jagoranci Sallar Jana’izar Sarkin da aka gudanar a fadar Ningi, wadda ta samu halartar dubban jama’a da suka haɗa da Gwamnan Jihar Bauchi, Alhaji Bala Abdulkadir Mohammed da tsofaffin gwamnonin Bauchi Alhaji Ahmadu Mu’azu da na Jigawa, Alhaji Sule Lamido da Sanata Abdul Ningi da Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu da Sarkin Dutse, Alhaji Hamim Nuhu Sunusi da ’yan majalisar dokoki na tarayya da ta jiha da sauransu.
Da yake miƙa ta’aziyya ga al’ummar Masarautar Ningi da ’yan uwa, Gwamna Bala Mohammed ya ce, marigayin ya yi rayuwa ta sadaukar da kai, kuma ya ba da shawarwari da jagoranci na uba domin zaman lafiya, hadin-kai da ci-gaban jihar.
Gwamna Bala Mohammed ya bayyana marigayi Sarkin a matsayin uba, wanda ya nuna mafi girman darajar shugabanci wajen samar da hadin-kai da ci gaba, ba a Masarautar Ningi da Jihar Bauchi kadai ba, har da kasa baki daya.
Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Alhaji Ahmad Mu’azu ya ce, Sarkin uba ne kuma aboki gare su lokacin da suke mulki, domin yakan taka wa gwamna birki, ya faɗa masa gaskiya in ya ga zai yi kuskure ko da abin da zai fada ba zai yi wa gwamnan dadi ba.
Sarkin Dutse Alhaji Hamim Nuhu Sunusi ya ce, duk abin da ya dame shi, idan ya fada wa Allah sai kuma ya zo ya nemi Mai martaba Sarkin Ningi ya warware masa, saboda shi uba ne gare shi kuma ya san tsakaninsu da mahaifinsa.
Gwamnonin Jihohin Arewa a karkashin jagoancin Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Inuwa Yahaya sun yaba kyawawan halayayen Sarkin a duk inda ya samu kansa, musamman yadda yake amfanar al’ummomin jihohin Bauchi da Gombe da Nijeriya baki daya.
Gwamnonin sun bayyana marigayi Sarkin da mai kishin Ningi da a kullum ke faɗa musu cewa, an bar Ningi a baya, ana raya wasu alƙaryu, don haka a kula da Ningi kuma duk lokacin da za a assasa wani abu na ci-gaba a Ningi ko makaranta ko asibiti, yakan ɗauki filinsa na kansa ya bayar, in kuma wani jami’i aka tura aiki, Sarkin kan rike shi da girma da daraja.
Al’ummar masarautar sun ce, rasuwar tasa ta bar Masarautar Ningi da Jihar Bauchi da Nijeriya da wani gurbi da ba za a iya maye shi ba.
Sun bayyana Alhaji Yunusa Danyaya a matsayin mutum mai son zaman lafiya, hikima da sadaukar da kai wajen kyautata rayuwar al’ummarsa.
Sun ce a tsawon sarautarsa, ya nuna misali nagari wajen jagoranci, ya samar da hadin kai da ci gaba a Masarautar Ningi.
Kuma ya kare martabar Musulunci da ciyar da addini gaba.
Za a daɗe ana tunawa da marigayi Sarkin saboda ƙwazo da kishi da ƙaunar al’ummarsa da kuma himmarsa wajen son zama lafiya da kwanciyar hankali, uba ga kowa, kuma mai karfin hali.
Mutane da dama da suka tofa albarkacin bakinsu sun roki Allah Madaukakin Ya gafarta wa marigayin, Ya kuma bai wa iyalansa da al’ummar masarautar da Jihar Bauchi hakurin jure rashinsa da aka yi. Allah Ya ji kansa, Ya sa ya huta.