✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taribo West ne dan wasan da ya fi ba ni wahala—Henry

Taribo bin mutum yake yi ko’ina babu daga kafa a cewar Henry.

Tsohon dan wasan Faransa, kuma tsohon dan wasan Arsenal, Thierry Henry ya ce a duk ’yan wasan bayan da ya fuskanta a lokacin da yake taka leda, babu wanda yake matukar takura masa kamar tsohon dan wasan bayan Najeriya, Taribo West.

Tsohon dan wasan wanda ya buga wa Arsenal da Barcelona, kafin ya yi ritaya ya zama mai horarwa ya ce, West yana matsa masa lamba matuka idan sun hadu a wasa.

Henry wanda yanzu shi ne Mataimakin Kocin Beljiyum ya ce, “Idan an ce batun wanda yake takura maka a wasa akwai iri biyu.

“Akwai wanda ba ka son buga wasa da shi. A nan zan ce Paul Scholes.

“Amma idan kana batun wanda ya fi takura min a ’yan wasan baya, zan ce Taribo West.

Taribo West

“Saboda lokacin yana Kungiyar Auderre, bin mutum yake yi ko’ina ka je,” a cewar Henry.

Henry yana magana ce kan lokacin da yake taka leda a Monaco, West kuma yana Auderre ta Faransa.

Bayan Henry ya koma Jubentus, sun ci gaba da haduwa da West wanda ya koma Kungiyar Inter Milan ta Italiya, inda suka ci gaba da karawa.