✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

480. An karbo daga Abul yaman ya ce: “ Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Adda’u danYazid laithiyu ya ba ni labari…

480. An karbo daga Abul yaman ya ce: “ Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Adda’u danYazid laithiyu ya ba ni labari cewa; lallai Aba Sa’id Khudri (Allah Ya yarda da shi), ya ba shi labari ya ce: “An ce ya Manzon Allah! Wasu mutane suka fi fifita? Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Mummunin da ke yaki da ransa da dukiyarsa domin daukaka kalmar Allah,” sai suka ce: “Sa’an nan sai wanne kuma? Ya ce: “Da mumminin da ke bisa tsaunin don ibadar Allah daga tsaunuka yana jin tsoron Allah, kuma yana kyale mutane bisa cutarsa (Ma’anar shine mutumin da ke cudanya da mutane masu cutarwa amma kuma shi mutanen sun kubuta daga cutarsa, yafi muminin da baya cudanya da mutane).”

  481. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Sa’id danMusayyib ya ba mu labari cewa; lallai Abauraiara ya ce: “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Misalin mai jihadi (yaki) domin daukaka kalmar Allah, saboda haka Allah shine mafi sanin wanda ke jihadi domin daukaka kalmarSa (Allah). Kuma Allah Ya alkawarta ga mai jihadi domin daukaka kalmarsa ko dai ya karbi ransa ya shigar da shi Aljanna, ko kuwa ya komo da shi lafiyarsa lau tare da lada ko ganimar yaki.”

  BABI NA UKU:-

  Addu’a da yin jihadi da bayanin shahada ga maza da mata. Umar ya ce: “Ya Allah! Ka azurta ni da yin shahada a cikin garin ManzonKa (SAW).”

  482. An karbo daga Abdullahi danYusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Is’hak danAbdullahi dandalhat daga Anas danMalik (Allah Ya yarda da shi), cewa: Ya ji shi yana cewa: “Manzon Allah (SAW) ya kasance yana shiga ga Ummi Hara’mi diyar Milhan sai ta rika bashi Abinci. Kuma ita Ummi Hara’mi tana karkashin (auren) Ubbad danSamit ne, sai Manzon Allah (SAW) ya shiga gare ta, ta ba shi Abinci, sai ta rika kallon (cire) kwarkwata bisa kansa, har sai Manzon Allah (SAW) da ya yi barci sa’an nan ya farka sai ya rika dariya ta ce: “Na ce, me ya sanya ka dariya ya Manzon Allah? ya ce, “Wasu jama’a ta na gani mayaka domin daukaka kalmar Allah suna hayewa (ketara) a kan jirgi bisa wannan kogi don yakar wasu, (kamar) sarakuna bisa kujeru, ko ya ce, misalin sarakunan masu kujeru. Is’hak ne ya yi shakka, ta ce: “Sai na ce, “Ya Manzon Allah! Ka roki Allah ya sanya ni cikinsu, sai Manzon Allah (SAW) ya yi mata addu’a. Sa’an nan  ya sake sanya kansa ya yi barci ya farka yana mai dariya. Na ce, “Me ya sanya ka dariya ya Manzon Allah! Ya ce, “Wasu mutane na gani cikin mafarki daga jama’a masu yakin domin daukaka kalmar Allah kamar dai maganar farko.” Ta ce, “Na ce, ya Manzon Allah! Ka rokan mini Allah ya sanya a cikinsu,” ya ce, “Ke kina daga cikin na farkon,” Ana nan haka sai ta hau jirgin ruwa a zamanin mulkin Mu’awiyya danAbu Sufiyan sai aka kayar da ita daga kan dabbarta lokacin da ta fito daga kogin ta halaka (shahada).”