Babi na Goma Sha Tara: Abin da ake so ga wanda ya yi mutuwar fuju’a (auke) a yi masa sadaka da bayanin biyan bashi ko alwashi ga mamaci:
457. An karbo daga Isma’il ya ce: “Malik ya ba ni labari daga Hisham daga babansa daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), cewa: “Lallai wani mutum ya ce da Annabi (SAW) cewa: “Hakika uwata an karbi ranta ina tsammanin da ta samu ikon magana da ta yi wasiyya da yin sadaka. Shin zan iya yin mata sadaka? Ya ce: “Na’am, ka yi mata sadaka.”
458. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga dan Shihab daga Ubaidullahi dan Abdullahi dan Abbas (Allah Ya yarda da su), cewa: Lallai Sa’ad dan Ubadah (Allah Ya yarda da shi), ya nemi fatawar Manzon Allah (SAW) sai ya ce: “Lallai uwata ta mutu, akwai alwashi a kanta, shin zan iya biya mata? (ya ce, na’am, kamar yadda ya taba gabata).”
Babi na Ashirin: Shaidarwa a cikin sadakar wakafi ko sadaka kadai:
459. An karbo daga Ibrahim dan Musa ya ce: “Hisham dan Yusuf ya ba mu labari ya ce, dan Juraij ya ba su labari ya ce, Ya’ala ya ba ni labari cewa: “Lallai shi ya ji Ikramah bawan dan Abbas yana cewa: “dan Abbas ya ba mu labari cewa, lallai Sa’ad dan Ubadah (Allah Ya yarda da shi), dan uwa ne ga kabilar Sa’idah. Ya ce: “Mahaifiyata ta rasu lokacin ba ya nan, sai ya tafi ga Annabi (SAW) ya ce: “Ya Manzon Allah! Lallai mahaifiyata ta rasu, amma ni ba na gida. Shin zai amfane ta da wani abin da zan yi sadaka da shi a gare ta? Ya ce, “Na’am,” ya ce, “Lallai ni, ina shaida maka gonata da ke Makhraf na bayar da ita sadaka a gare ta (dominta).”
Babi na Ashirin da daya: Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ku bai wa marayu dukiyarsu kada ku gauraya mummuna da mai kyau, kuma kada ku ci dukiyarsu hade da dukiyarku…har zuwa karshen aya cewa: “Ku auri abin da ya yi muku dadi daga mata…” (k:4:2-3):
460. An karbo daga Abu Nu’aman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Urwatu dan Zubair ya kasance yana bayar da labari cewa: “Lallai shi ya tambayi A’isha (Allah Ya yarda da ita), game ayar nan cewa: “In kun ji tsoron ba za ku yi adalci bisa ga marayu (mata) ba, to ku auri abin da ya yi muku dadi daga mata….”(k:4:2-3). Ya ce, “Ita ce marainiyar da take gidan mai kula da ita, sai ya yi kwadayin aurenta saboda kyanta da dukiyarta. Kuma yana son ya aure ta bisa kankanen matsayi na sadaki sai aka hana game da haka wato aurensu face bisa adalci gare su wajen cikar sadakin. Domin haka aka umarta da auren wadansunsu daga mata. A’isha ta ce: “Sa’an nan mutane suka rika neman fatarwar Manzon Allah (SAW) bayan haka.” Sai Allah Madaukaki Ya saukar da cewa: “Suna neman fatarwaka cikin mata (marayu), ka ce: Allah zai ba ku fatawa cikinsu- ta ce: “Sai Allah Ya bayyana komai cikin wannan aya cewa: “Lallai idan marainiya ta kasance kyakkyawa kuma mai dukiya kuma suka yi kwadayin aurenta, ba su yi nufin riskar da ita bisa sunnarta ba wajen cika sadakinta. Amma idan ta kasance wadda ba a kaunarta don karacin dukiya da kyu sai su kyale ta (rabu da ita), su nemi wata daga mata.” Ya ce, “Kamar yadda suke barinta (kyale ta) lokacin da ba su son ta (kaunarta), don haka ba su da ikon aurenta idan suka yi kwadayin aurenta saboda dukiya da kyanta, face idan za su yi adalci wajen cika sadakinta kuma za su ba ta hakkokinta.”
Babi na Ashirin da Biyu:
Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ku jarraba marayu har sai sun isa aure, idan kun fahimci shiriya (daga gare su) ku mika musu dukiyarsu, kada ku ci bisa barna da gaugawar haka kafin girmansu. Kuma wanda yake wadatacce, to ya kame kansa, kuma wanda yake fakiri, to ya ci gwargwadon yadda ya kamata. To idan kun mika musu dukiyoyinsu sai ku shaidar a kansu. Kuma Allah Ya kasance Mai bincike. Maza suna da rabo daga abin da iyaye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, kuma mata suna da rabo daga abin da iyaye biyu da mafi kunsantar dangi suka bari daga abin da ya karanta daga gare shi ko kuwa ya yi yawa, rabo yankakke (rabo isasshe).” (k:4: 6-7).