Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka (AU) ta taya Emmanuel Macron murnar sake lashe zaben Shugaban Kasar Faransa da aka gudanar ranar Lahadi.
Shugaban kungiyar, Moussa Faki Mahamat ne ya aike da sakon a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Litinin.
Moussa ya ce, “Ina aike wa da sakon taya murna da farin ciki ga Emmanuel Macron kan lashe zaben Shugaban Faransa da ya yi a karo na biyu.
“Ina farin cikin ci gaba da yin aiki tare wajen gina kyakkyawar alaka tsakanin Afirka da Faransa, da ma nahiyar Turai baki daya,” inji Moussa Faki.
Shugaba Macron dai ya lashe zaben na 2022 ne bayan ya samu sama da kaso 58.54 na kuri’un da aka kada, yayin da ya doke babbar abokiyar hamayyarsa, Marine Le Pen, wacce ta sami 41.56 na kuri’un, kamar yadda sakamakon da Ma’akatar Cikin Gidan Kasar ta fitar.
A shekarar 2017 ma, Macron da Marine sun gagara a zaben, inda nan ma Macron din ya yi nasara da kaso 66.1 na kuri’un. (NAN)