✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tankar mai ta yi bindiga, ta kone shaguna a Gombe

Gidajen mai da shaguna da dama sun kone kurmus yayin da tankar mai ta kama da wuta.

Shaguna da dama dauke da kayan kudi sun kone yayin da wata mota tankar mai ta kama da wuta a wani gidan mai a Jihar Gombe.

Lamarin ya faru ne bayan Sallar Magriba a gidan man NNPC da ke daura da Tashar Mota ta Dukku a yakin Tudun Wada a jihar.

Gidajen mai da shaguna da ke kusa da gidan man da motar ta kama da wuta duk wuta ta cinye su, wanda hakan ya jefa masu kasuwanci da wajen cikin zullumi.

Zuwa lokaci da muke hada wannan rahoto ba a samu labarin rasuwar wani a sanadin gobarar tankar man ba.

Ha wa yau, jami’an kashe gobara na jihar na ci gaba da kokarin kashe wutar.