Wata motar dakon mai dauke da gas har lita 44,000 ta kama da wuta tare da yin bindiga akan babban titin Legas zuwa Ibadan.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Asabar akan gadar Odetola dake jihar Legas.
- Tankar mai ta yi bindiga, ta kone shaguna a Gombe
- Mutum biyu sun kone kurmus a hatsarin tankar fetur
- Gobarar tankar mai ta janyo asarar dukiya a Legas
- Gwamnan Legas, Sanwo-Olu ya kamu da COVID-19
Wani ganau ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da daya daga cikin tayoyin motar ta kama da wuta.
A cewar sa, direban bai san tayar ta kama da wuta ba sai da aka ja hankalinsa a kan hakan.
Tuni dai Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da takwarar ta ta Jihar Legas (LASEMA) suka dukufa har suka sami nasarar kashe wutar.
Rahotanni sun ce a lokacin da abin ya faru, direban ya yi yunkurin jan motar baya amma hakan ta ki yuwuwa, inda dole ya fice a guje domin tsira da rayuwarsa.
Daga nan ne dai motar koma baya inda ta daki wata motar dakon kaya, wacce nan take ita ma ta kama wuta, da wata karamar mota.
Shugaban hukumar NEMA reshen jihar Legas Ibrahim Farinloye, ya ce ba a samu asarar rai ko daya ba a gobarar.
Shi kuwa shugaban hukumar LASEMA) Dakta Olufemi Oke-Osanyitolu, ya ce har yanzu ba a kai ga tantance adadin asarar da aka yi a gobarar ba.