✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tankar mai ta kama da wuta a hanyar Kaduna-Zariya

Takar makare da man fetur ta fadi ne a kusa da wani gidan mai

Da misalin karfe 1 na ranar Talata ce wata tankar mai da ke shake da man fetir ta fadi a kusa da gidan man NNPC a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Lamarin da ya faru dab da Gadar Kwangila da ke unguwar Dan Magaji a Zariya, ya tsayar da zirga-zirgar sufuri a babban hanyar.

Zuwa yanzu jami’an hukumar kashe gobara shiyyar Zariya na can sun dukufa wurin kashe wutar da ta tashi daga man fetur din da motar ke dauke da shi.

Wani ganau ya mai suna Malam Usman ya shaida wa Aminiya cewa lokacin da lamarin ya faru an fito da wasu yara a kone da aka garzaya da su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika domin kula da lafiyar su.

Jami’an hukumar kashe gobara na fafutukar kashe wutar da da tashi a kan hanar Kaduna-Zariya
Wutar da ta tashi bayan motar da ke makare da mai ta fadi
Mutane su yi dafifi sun kallon wutar da ta tashi daga motar man fetur din.
Wasu daga cikin ‘yan kallo a gefen motar masu kashe gobara da ke aiki a wurin.