Wata tanka makare da man fetur ta kone kurmus a kan titin Legas zuwa Benin da yammacin Laraba.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Legas, Mista Busayo Araroba, ya ce motar ta kifa kasa ne sakamakon gudun ganganci da direbanta yake yi.
- ‘Duk dan kasar wajen da muka kama yana kada kuri’a zai dandana kudarsa’
- Babu gudu ba ja da baya a kan ranakun zaben 2023 – Yakubu
Araroba, ya ce hadin guiwar jami’an hukumar kashe gobara na Akure da Okitipupa sun yi kokarin kashe wutar ba tare da ta tsallaka wani wuri ba.
Kazalika, ya ja hankalin direbobin tankar mai da suke mayar da hankali da matakan tuki, duba da yanayin abin da suke daukowa.
Har wa yau, jami’in ya ce ba a samu asarar rai ko daya ba.
Araroba, ya bukaci jama’ar Jihar da su mayar da hankali wajen kiran hukumomi a duk lokacin da suka ci karo da sani abu da ke bukatar dauki musamman a wannan lokaci na zafi da ake ciki.
A cewarsa hukumar kashe gobara ta jihar na rokon mutane da suka gaggauta kiran wayoyin hukumar na ko ta kwana musamman a lokutan da aka samu rahoton tashin wuta ko gobara.