Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya sha alwashin rushe kauyen Remon a Jihar, wanda ya zamo maboyar bata-gari.
Hakan na zuwa ne bayan rahoton bincike da jaridar Daily Trust ta wallafa a ranar Lahadi, inda a ciki ta tona asirin irin ayyukan ta’adancin da ake yi a yankin.
- Buhari zai gana da duk Sanatoci 109 a daren Talata
- Majalisa ta ki amincewa da Onochie zama Kwamishinar INEC
Da misalin karfe 11:30 na safiyar Talata, Gwamna Tambuwal ya ziyarci kauyen, inda ya ce mazauna yankin na zaune ba bisa ka’ida ba.
A ranar Asabar ne dai jami’an tsaro suka yi wa kauyen na Remon kawanya inda suka kama mutum 100 da ake zargi da aikata laifuka.
Jami’an tsaron da suka jagoranci kai samamen sun hada da na NDLEA da kwastam da na hukumar kiyaye hadurra da DSS da NSCDC da kuma ’yan sanda.
Rahotanni sun ce samamen wanda aka fara shi da misalin karfe biyar na yamma ya shafe kusan sa’o’i biyu.
Tuni dai aka tisa keyar wadanda ake zargin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuffuka na shalkwatar ’yan sanda domin fadada bincike.
Wakilinmu da ya ziyarci shalkwatar ya ce daga cikin wadanda ake zargin har da mata.
Kakakin ’yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Sanusi Abubakar wanda ya tabbatar da kai samamen ya ce wadanda aka kama sun kai mutum 144 sannan sun kuma kama miyagun kwayoyi masu dimbin yawa.
“Za mu binciki dukkansu, kuma duk wanda muka gano yana da laifi za mu gurfanar da shi a gaban kuliya,” inji kakakin.