An bukaci sabbin shugannin kananan hukumomi Jihar Sakkwato su rika gudanar da taruka da suka shafi sha’anin tsaro a jihar wadda ke cikin jihohin da suke fuskantar matsalar tsaro a yankin Arewa maso Yammancin Najeriya.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar ne ya ja hankalin sabbin shugabannin, yana mai bukatar su rika gabatar masa da sakamakon tarukan tsaron da suke yi don sanin matakan da gwamnatin jihar za ta dauka.
- An fara farautar ’yan bindigar da suka kashe ’yan sanda a Taraba
- Watan Azumi: Za a rage farashin kayan abinci da kashi 75
- A shirye muke a kashe mu kan ceto ’ya’yanmu —Iyayen dalibai ga El-Rufai
- Har yanzu APC ‘hatsin bara’ ce —Ganduje
“Hanya daya za mu inganta harkar tsaro shi ne mu rika tafiya tare da kowa.
“Ku kawar da bangaranci, ku yi shugabanci nagari tare da tafiya da kowa,” inji Tambuwal a wajen bikin rantsar da sabbin shugannin kananan hukumomin, a ranar Laraba.
Kazalika, ya umarci su da sa gaskiya da amana a cikin shugabancinsu.
Sannan ya gode wa jama’ar jihar da suka fito wajen zabar mutanen da za su shugabance su, tare da jinjina wa masu sarautun gargajiya kan ba da hadin kai a yayin zaben.