✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambayoyin Duniyar Ma’aurata (4)

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga…

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da masu karatu suka aiko:

 

Shin ya halatta ga mutum ya ga yarinya a Facebook ya ce yana sonta kuma in ya halatta mene ne ladubban neman aure a Facebook?

 

Amsa

Neman aure ta Facebook ya halatta in har an bi dukkan kaidojin shari’a kuma an kauce wa irin fitinun da ke tattare da wadannan kafofi na sadarwar zamani. Ga ladubban neman aure ta Facebook da ma sauran kafofin sadarwar zamani.

1. Ta yaya mutum ya ga ita wacce yake son ya aura din? Daga sunanta kadai, ko daga hotunan da take yadawa ne ko kuwa daga irin bayanan da take wallafawa ne a bangon sadarwarta? Dukkan wadannan hanyoyi ba wanda zai bayyana halinta cewa ta kirki ce ko akasin haka ba. Don tana wallafa bayanai masu kyau ba shi ke nuna ta kirki ba ce, haka kuma don tana sa hotunanta araha kowa ya kalla ba shi ke nuna ta banza ba ce. Da yawa akwai wadanda suke wallafa bayanan karuwa da tunatarwa amma su ba su amfani da bayanan, rayuwarsu akasin haka ce. Haka kuma duk da cewa yawanci mata suna wallafa hotunansu ne don su burge a yaba musu a ce sun yi kyau, akwai kuma masu yi da niyyar fitina da batarwa, akwai kuma ’yan kadan da suke yi kawai saboda shiga yayi, ko kuma saboda rashin sani ba su  san illa ko haramcin yin haka ba.

2. To ko ma ta wace hanya mutum ya ga wacce ya ji ya kamata ya nemi aurenta a Facebook din, abu na farko da zai fara yi shi ne Istikhara don neman zabi da jagorancin Allah Madaukakin Sarki a cikin wannan al’amari da yake da niyyar zartarwa a rayuwarsa. Yin Istikhara zai samar da albarka kuma ya kade tsautsayi da fitina daga cikin wannan al’amari cikin yardar Allah.

2. Bayan yin Istikhara sai ya yi bincike ta Facebook din ya gano halayyarta da dabi’unta a wadannan kafofi da irin shafukan da take bi da irin guruf-guruf da take ciki da abokai da kawayenta na wadannan kafafe da yadda take hulda da su. Sannan in ya samu cikakken suna da unguwarsu. Daga bayanan da suke shafukanta zai iya bincike na zahiri game da gidansu da zuriyarsu da sauran duk abin da mai neman aure ya kamata ya bincika a hakika. In ya gamsu da binciken nasa sai ya je mataki na gaba.

3.To daga nan ta yaya mutum zai isar da niyyarsa ga wannan baiwar Allah da ya gani a Facebook? Hanya mafi dacewa sai ya duba bangaren ’yan uwa na shafinta in akwai wani daga cikin ’yan uwanta maza a hade da shafin sai ya yi masa magana wanda shi ne zai yi masa jagora zuwa ga mataki na gaba. In kuma babu, to sai yi aika mata dan gajeren sako cewa yana bukatar lambar wayar magabatanta don ya nemi izininsu ya gabatar da kaina gare ki da neman aure.

Amsar da ya samu ita zai yi aiki da ita a mataki na gaba. In kuma bai samu ba zai iya maimaita sakonsa har sau 3, daga nan sai ya dakata. In ya samu hadin kai daga ita ko wani daga cikin ’yan uwanta da ya samu damar magana da shi, to sai a ya ci gaba da zartar da sauran ladubban neman aure kamar yadda suke.

Abubuwan Kiyayewa:

Kulla alakar soyayya da yarinya ta Facebook ko wata kafa, a yi ta hira da ita ana aika mata kalaman soyayya ita ma tana aikowa haramun ne kuma kusantar zina ce, babbar alkaba’ira ce da ya wajaba dukkan Musulmin da ya damu da lahirarsa, da abin da za a rubuta masa a littafinsa na zunubi ya guje wa aikatawa.

 

Sai mako na gaba insha Allah da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a koyaushe, amin.