Me ke kawo makanta? Makanta nau’i kala nawa ce? Ana gadon ta? Tana da magani? Ana warkewa sarai?
Amsa: Matsaloli daban-daban a ido su suke kawo makanta. Cutuka tun daga na shi idon kansa da na jiki za su iya taba idon su kawo makanta. A wasu lokuta ma akan iya haifar jariri da matsalar makanta, amma kusan ba gada ya yi ba, sai dai ko idan mahaifiyarsa ta sha wani abu da zai bata masa idon tun a ciki.
Cutukan da suka fi kawo makanta a duniya baki daya sune na yanar ido, sai ciwon gilakoma, sai ciwon gira, wato tirakoma, sai tsufa, wato mutuwar ido saboda tsufa, sai ciwon suga da hawan jini, wadanda su kuma matsalolin jiki ne amma sukan taba ido. Akwai kuma kari sai kansar ido a yara, wadda ita ma kan iya kawo makanta a ido mai ciwon. Bugu da kari za a iya yin hadari a bugu a ido, idon ya tsiyaye. Ka ga wannan ma zai iya kawo makanta a ido daya.
Magance matsalar makanta ya danganta da abinda ya jawota. ‘Yan kalilan din da akan magance su sune makantar yanar ido, da ta kari akan madubin ido, wadanda da an yi tiyata an cire yanar ko karin shikenan sai gani ya dawo sarai kamar da, ko ma ya fi da.
A yanzu dai binciken kimiyya ya yi nisa akan neman dabarun dawo da gani a sauran matsalolin, inda a yanzu akan iya dasawa kwakwalwa wani irin madubi ya rika aika mata sakonnin gani a maimaikon idanu.
Irin labaran nan da za ka ji ana cewa idan aka sa wa mutum idanun akuya ko na wata dabba ganin zai dawo duk shaci-fadi ne ba a haka a gaske. Ko an yi wa mutum dashen wani ido na tangaran sai dai don a cike ramin idon ba wai domin a dawo da gani ba.
Makanta ba a gyara ta da gilashi. Matsalolin ido da akan gyara da tabarau su ba makanta ba ne, tangarda ce karama ta rashin gani tangararas, wadda da an saka gilashi take gyaruwa. Da fatan ka fahimta.
Idona ke ciwo, sai na je likitan ido aka duba aka ce ina da ciwon gilakoma. An bani magunguna amma an ce sai an yi tiyata. Don haka na tarbi ciwon da wuri. To shi ne nake neman karin haske da shawara
Daga Malama Aisha
Amsa: Bayan ciwon yanar ido, ciwon gilakoma shi ne na biyu a duniya wajen kawo makanta. A wannan ciwo, ruwan ido ne ke taruwa ya ki tafiya inda ya kamata har ya kumbura kwayar idon. Da ma kamata ya yi a ce duk bayan wani dan lokaci ido na zuke ruwan cikinsa, ya maye shi da sabo. To idan rariyar zuke ruwan ta samu matsala, ruwan kan taru ya ki tafiya, hakan kuma kan kumbura kwayar idon daga ciki. Idan kwayar ido ta kumbura kuma to gani zai fara dusashewa, ta yadda mahangar idon ba za ta yi aiki sosai ba.
Bakar fata mu ne mutanen da muka fi kowa kamuwa da wannan ciwo, yawanci kuma wadanda suka manyanta. Alamar da mutum zai fara gani ita ce kawai sai ya ga kamar an sa labule a ido daya an rufe ganinsa. Da fari rufewar ganin rabi ne amma idan ciwo ya yi nisa sai ganin ya rufe ruf a idon da matsalar take, kafin dayan ma ya kamu. Ba kamar hakiya da yana ba, wannan ciwo duka idanu biyu yakan kama, sai dai yawanci ba a lokaci guda ba.
Hanyar kiyaye makanta daga wannan ciwo ba ta wuce ta yawan zuwa auna ido a kai-a kai ba, sa’annan kuma duk wanda ya fara gani kamar ana sa labule a idonsa, dole ya garzaya asibiti cikin sauri a duba, idan tiyata ce ta kama a yi, kada abin ya yi nisa.
To kin ji bayani Malama, da fatan za ki ba da hadin kai duk abinda ya kamata a yi, a yi, kafin a zo a ce an makara. Allah sa a dace.
Menene ke jawo wani lokacin idanun mutum ya rika fitar da kwantsa ko hakan wata matsala ce?
Daga Nasiru Kainuwa Hadejia
Amsa: A’a ba lafiya ba ce ido ya rika fitar da kwantsa Malam Nasiru. Kwantsa ai diwa ce, kuma duk inda aka ga diwa da alama akwai taruwar kwayoyin cuta. Kwayoyin cuta da suka fi sa kwantsa a ido sune na bacteria da na birus. Kuma ko wane da maganinsa. Don haka idan mutum yana ganin kwantsa a idonsa ko da ciwo ko kaikayi ko babu, dole a duba a gani a asibiti ko yana bukatar magunguna.
Da gaske ne inki ko ruwan biro yana iya sa ciwon sankara ko kansa?
Daga Saratu Y., Pandogari
Amsa: A’a a kimiyyance babu wasu masana da suka danganta ruwan biro da ciwon kansa. Don haka ba kanshin gaskiya a wannan zance, shaci-fadi ne kawai.
Me ke sa wa idan aka mini allura sai wurin ya rika yi mini ciwo?
Daga S. Haruna
Amsa: Bai kamata idan aka maka allura wurin ya ci gaba da zafi sosai har ma ya fi allurar zafi ba. Ga alama wanda yake maka allurar bai kware sosai ba, ko ma bai kamata ya yi allura ba. Ka san akwai ‘yan karambani ko a asibiti akwai masinjoji wadanda saboda karambani sukan iya yin wannan barna. Don haka dai duk lokacin da za a maka allura ka tabbata sabon sirinji ne, kuma an goge fatar wurin da ruwan magani kafin a tsikara maka, don kada wurin ya yi diwa.