✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambayoyi da amsoshin likita game da kiwon lafiya

Na ga bayaninka a kan majinar makogwaro da makaki a wuya. To ni na je asibiti ya fi a kirga amma idan na ji sauki…

Taswirar kwayoyin halittar mahaifaNa ga bayaninka a kan majinar makogwaro da makaki a wuya. To ni na je asibiti ya fi a kirga amma idan na ji sauki sai wannan makaki ya dawo da kuma atishawa sosai. Meye karin bayani?
Daga Yusuf, Kura
Amsa: E, a wasu mutanen ba kwayoyin cuta ba ne ke kawo makakin wuya, kwayoyin cikin iskar gari kamar iskar hunturu ko kurar kara ko hayaki ko kurar titi, duka suna da wasu abubuwan da ka iya jawo wa wasu makakin, ta yadda ko an ba su maganin kashe kwayoyi zai taimake su ne kawai na dan wani lokaci kafin abin ya sake dawowa. Game da bayaninka na cewa kana yawan atishawa ma duka idan aka hada za a iya cewa kai ba kwayoyin cuta ne ke sa maka naka ba, abin da ake kira allergy ne ga dukkan alamu. Don haka idan ka sake komawa za ka iya fada wa likitanka wannan bayani domin ya canza maka magunguna. Kai kamata ma ya yi ka ce likitan ya tura ka bangaren likitocin makogwaro wato ENT su lelleka su ga ko za su ga wani abu.
Sai shawara da watakila ba kowa zai ba ka ba, ta gudun duka abin da ka san zai iya tasar maka da wannan allergy. Duk inda ka shiga ka ji atishawa na taso maka to ka gane wurin ka kuma rika kiyaye shiga. Misali, shakar hayaki ko shakar kura ko shiga cikin karmami da dai sauransu. Idan daya daga cikinsu na sa maka atishawa, to fa dole ka kiyaye.
Likita, ko shin hawan jini yana kawo ciwon zuciya?
Daga Suraj Legas
Amsa: kwarai kuwa, hawan jinin da ya dade a jikin mutum ba a gano ba yana iya tabo sassa da dama na jikin dan Adam, ya yi musu lahani. Wadannan sassa su ne zuciya da ido da koda da kwakwalwa.
Amma hakan na faruwa ne idan hawan jinin ya dade a jikin mutum ba a sauko da shi ba ko kuma mai shi ya dade bai sha magani ba. Idan aka ce jini ya hau, ana nufin zuciya na aikin da ya fi karfinta ke nan saboda tsukewar da magudanan jini na sassan jiki kan yi, wanda sai zuciya ta yi da gaske kafin ta buga jini zuwa sassan jiki.
Ciwon hawan jini wato ‘hypertension’ shi ne kan gaba wajen kawo ciwon zuciya a kasar nan. Yakan kama kowa, mace ko namiji, har ma da yara duk da cewa na yara bai cika faruwa kamar na manya wadanda suka ba arba’in baya ba.
Hawan jini kan sa wa zuciya lahani ta hanyoyi da dama. Yakan iya sa tsokar naman zuciya ta kumbura, musamman bangarenta na hagu, bangaren da kan buga jini zuwa sauran sassan jiki saboda karfin aikin da zuciyar take yi, (kamar irin kwanjin hannu da masu daukar nauyi kan yi) ko ya sa tsagewar babbar magudanar jini da ta bar zuciyar, ko ya rikita tsarin yadda zuciya ke bugawa ko kuma ya sa zuciyar ta tsaya da aikin ma gaba daya, wato ya kawo bugun zuciya.
Wasu idan sun kammala wanka sai su yi amfani da soson wankan su wanke takalmansu da shi, shin ko akwai wata illa da hakan ke kawowa ga lafiyar mutum ko kuwa?
Daga Ba Ka Soyayya da Hussaini Binanchi
Amsa: E, kwarai kuwa za a iya samun matsalar ciwon fata ko kurajen fata mana idan wata kwayar cutar da aka kwaso da soson wanka ta hau fatar jiki, tun da shi takalmi datti da kwayoyin cuta yake kwasa. Irin wannan ba ya daya daga cikin abubuwan da za a sa a matsayin turba ta tsabta sai dai ko ta kazanta. Don haka kamata ya yi a ware wa takalmi abin wanke shi daban, ba soson wanka ba.
Ina da matsalar faduwar gaba. In dai zan ji karar wani abu komi kakantarsa ko leda ce sai gabana ya fadi kuma na ji shi har kwakwalwata. Ko za a yi min bayanin abin da ke janyo hakan?
Daga Maman Aiman G/Dutse
Amsa: E, akan samu mutane masu irin wannan matsala ta yawan tsoro a cikin al’umma kuma mata matsorata sun fi maza yawa. Akwai tsoro da fargaba na yau da kullum daidai gwargwado amma idan aka samu suka yi yawa sukan zama ciwo. Alamomin da za a ce kuwa tsoro ya fara zama ciwo sune na wadanda kika lissafa, wato tsorata a kan abin da bai-kai-ya-kawo ba da jin faduwar gaba da jin cewa abin ya fara taba kwakwalwa. Wadannan duka na nufin sai kin garzaya ga likitan kwakwalwa a nan asibitinku na Dawanau a kara yi miki tambayoyi, idan an ga kina bukatar taimako a fara ba ki magani kafin ki fara jin sauki.
Ina so a yi mini karin bayani a kan sankon ka. Ko shin da gaske ne idan mai juna biyu tana yawan lasar ludayin miya ko kuma tana yawan shan zuma su ma suna haddasa sankon.
Daga Maryam Aliyu
Amsa: A’a, wadannan duk shaci-fadi ne da kuma camfin Hausawa. Wasu ma sukan kara da cewa arziki ko ilmi sukan sa sanko. A kimiyyance abin da ke kawo sanko shi ne gado. Idan iyayen mutum ko kakanni suna da sanko to ana kyautata zaton shi ma mutumin zai yi sankon. Sa’annan kuma ana kyautata zaton wahala ta yau da kullum ma za ta iya sa sanko, watakil ko wahalar neman arzikin ko ta neman ilmin. Wannan irin wahalar rayuwa har furfura ma takan sa. Wadannan su ne abin da aka sani game da sanko ba wancan bayani naki ba.
A duk lokacin da tarmani ko cinnaka ya cije ni, akalla nakan kwana biyu wurin yana mini kaikayi. Likita wai mi ke sa haka?
Daga Rabi’a Muhammadd Kebbi
Amsa: kwarai kuwa, ai shi cizon tarmani ko cinnaka yana dauke da wata guba ne mai sinadarin acid, ta yadda dole wurin da aka ciji mutum ya fara zafi ya dan kumbura kuma, a wasu lokutan a wasu mutanen ma har borin jini sosai yake sa musu. To, idan yana sa borin jini shi ne za a damu, domin sai an yi sauri an garzaya asibiti amma idan kaikayi kawai yake yi da dan kurji, to a daure a ba shi kwana daya zuwa biyu, zai baje ya daina zafi, wato gubar za ta bi jini ta narke kuma idan radadin ya tafi, shi ke nan ita gubar ba za ta kawo illa ba.

LAFIYAR MATA DA YARA

Ciwon Daji Na Bakin Mahaifa

Ina son ka yi mana cikakken bayani a kan ciwon daji na mahaifa, musamman alamominta da ta yadda mutum zai gane yana dauke da ita saboda hadarinta. An ce idan ya kama mace ba ta sani ba har sai ta watsu ko’ina sannan ake sani.
Daga Sameera Y. Gusau
Ciwon kansa ko ciwon daji wani shu’umin ciwo ne da ke iya kama sassa daban-daban na jikin dan Adam. Babbar matsala ce a cikin al’umma saboda yawan kawo jinya da rashe-rashen rayuka. Wasu ana iya kare kai daga kamuwa da su, kamar na bakin mahaifa, wasu kuma ba a iya kare kai.
Wadanda za su iya kamuwa: Ciwon daji na bakin mahaifa ya fi kama mata wadanda suka ba shekaru hamsin baya. Bayan shekaru kuma sai yawan auri-saki da yawan haihuwa. Wato matar da ta shiga gidan aure fiye da biyar ko ta yi ’ya’ya fiye da goma tana cikin hadarin samun wannan ciwo. An tabbatar kuma mata masu zaman kansu sun fi sauran mata kamuwa, sakamakon wata kwayar cuta da suke dauke da ita, wato birus da ake kira Human Papilloma birus. Wannan kwayar cuta ita ma an tabbatar tana sa bakin mahaifa ya rikide ya kamu da ciwon daji.
Alamun Ciwon: Farkon ciwon yana zuwa da alama daya ce kawai, wato zubar jini kamar na al’ada a matar da ta dade da daina al’ada, kamar a mata wadda ta ba shekaru hamsin baya. Idan ciwon ya yi nisa akwai ciwo da kumburin mara, rashin cin abinci da rama. Mace ta dashe tayi fari fat saboda karancin jini a jiki.
Hanyoyin Kariya: Babbar hanyar da ake hana kamuwa da wannan kwayar cuta dai ita ce ta kame kai sai an yi aure, musamman ga mata masu zaman kansu. Su kuma mata wadanda suka ba hamsin baya ko kuma suka samu haihuwa fiye da yara goma za su iya kare kansu daga ciwon daji na bakin mahaifa ta hanyar zuwa screening duk bayan shekaru biyu wato akalla sau daya a shekara biyu a asibiti, sashen mata wato sashen Gynae.
A wannan screening ko tantancewa, ana gwajin kwayoyin halittun bakin mahaifa don a ga ko sun fara rikidewa. Ana iya gano irin wannan ciwo na bakin mahaifa a wannan gwaji. Kuma da an gano shi akwai magani tun kafin ciwon ya yi nisa. Wato idan dai aka gano ciwon da wuri to za a iya maganinsa amma idan aka gano bayan ya riga ya yadu, to kusan babu magani kuma ciwon zai yadu ya tafi sauran sassan jiki ya galabaitar da mace kafin daga baya ya yi sanadin halaka ta. Akwai santa-santa na yin wannan gwaji kusan a kowane babban asibiti a biranen garuruwan kasar nan.