Tambaya: Mene ne hukuncin wuce Mikati ba tare da Harama ba,?
Amsa: Hakan ya halatta, matukar cewa ba ka zo ne da niyyar yanka ba, ya halatta ka shiga Makka ba tare da Harama ba, idan ka zo ne ba da niyyar Umara ko Hajji ba, kawai dai ka zo ne don wani dalili naka kamar neman ilimi ko duba mara lafiya, ko kasuwanci, kai ko ma a ce hanya ce ta biyo da kai, wannan babu komai a kanka. Wanda dole sai ya shiga da Harama shi ne wanda ya zo don aikin Hajji ko Umara, idan ya wuce ba tare da ya yi Harama ba, to sai ya zubar da jini, ma’ana sai ya yi yanka.
Tambaya: Ni mutumin kasar Sa’udiyya ne ina aiki a wajen kasar, a watan azumi na zo, iyalaina suna Jiddah, na fara sauka a wajensu na yi kwana uku, daga baya na yi Haramar yin Umara, shin ina da laifi?
Amsa: Wannan zuwa ka zo ne don iyalanka, sai bayan ka je gida sannan ka yi niyyar yin Umara, yin haka babu laifi, sai ka yi Harama a Jiddah kamar yadda mutanen Jiddah za su yi.
Tambaya: Ni ma’aikaci ne ina aiki a Riyad, sai na zo Jiddah don yin fasfo, bayan na gama abin da nake sai na yi niyyar yin Umara, na yi Harama daga Jiddah, bayan kwana uku na sake yin wata Haramar don yi wa mahaifiyata Umara, na yi Harama daga Mikatin Nana A’isha, sai kuma na yi niyyar yi wa mahaifina da ma wadansu mutane daban Umara, tare da cewa mahaifina da mahaifiyata sun rasu, shin abin da na yi niyya ya halatta?
Amsa: Babu laifi don ka yi musu matukar cewa ba ka yi niyyar Umara ba sai a Jiddah ba a Riyad ka yi ba, wata matsala ce ta kawo ka,wadda da ka gama kuma ka yi niyyar Umara wannan babu laifi. Amma maimaita Umara daga Tan’im ko waninsa wannan bai halatta ba, saboda Sahabban Annabi (SAW) ba sa maimaita Umara, idan son zo Umara daya kawai suke yi ta ishe su, kai mai ka yi daya sai ka shagalta da dawafi kamar yadda Sahabbai da Tabi’ai suke yi, irin su dawusu da Adda’u da wadansunsu.
Tambaya: Na zo a jirgi daga Riyad, na yi niyyar idan an zo Mikati zan yi Harama amma sai barci ya dauke ni, ban farka ba sai da aka zo Jiddah yaya zan yi?
Amsa: Idan ka riga ka yi harama daga baya, to sai ka yi yanka, idan kuma ba ka yi Harama ba sai ka koma inda Mikati yake wato Sailu ko Wadi Mahra, ka yi harama a can babu komai.
Tambaya: Na zo daga Riyad a jirgi amma ban yi harama ba, sai na yi harama a Jiddah na yi Umara, da na tambaye ka sai ka ce da ni sai na sake yi harama ko in yi yanka, na tafi Saylu na yi wata haramar a can na sake wata Umarar ta biyu, shin wancan yanka ta farko da ban yi ba ta saraya daga kaina ko kuwa?
Amsa: Ka ce ka zo daga Riyad da niyyar yin Umara sai ka yi harama a Jiddah, ka yi Umararka, ka ce na ce da kai, ka je ka yo harama daga Saylu. A’a dan uwa ni ban ce maka ka yi harama a Saylu ba. Matukar a Jiddah ka yi Harama sai ka yi yanka, kai koda a Saylu ka yi Harama sai ka yi yanka in dai ka shiga Makka ba tare da Harama ba. Ina ma laifin a ce Mikati ka tafi ka yiwo harama a can da babu komai. Amma in dai a Jiddah ka yi harama yanka ya kama ka, koda bayan wannan Umarar ka yi Umara dubu ana dai bin ka wancan yanka, amma da a ce ka shiga ne babu niyya daga baya sai ka fito ka tafi Mikati ka yi harama wannan ya yi, babu laifi.
Tambaya:A shekarar da ta wuce na yi tafiya daga Riyad zuwa Jiddah don yin Umara sai na manta Hiramina, yayin da na yi niyyar yin Harama sai na rasa abin da zan daura a matsayin Hirami, sai da na shiga garin Jiddah na sayo wani Hiramin, sannan na yi Umarata shin ina da laifi?
WANI KUMA YA CE: Ni kuma na zo ne ba ni da Hirami sai da na sauka a Jiddah na yi harama a cikinta shin sai na yi yanka?
Amsa: Ai! Da ka yi Hirami da kayanka, misali ka yi amfani da rawaninka a matsayin riga, kayanka kuma a matsayin mayafi ai da babu komai, ko kuma da ka yi niyyarka ta harama in ya so daga baya sai ka je ka sayi Hiramin. Amma matukar ba ka yi niyyar harama ba sai da ka shiga Jiddah, to, sai ka yi yanka, saboda ka wuce Mikati ba tare da harama ba. Abu ne da aka sani cewa idan ka zo ba ka da komai za ka iya yin Hirami da rawaninka da tufafinka (hakan) ya isar maka.
Tambaya: Na yi Hajji amma ban san takamaiman inda mikati yake ba, sai na yi harama a tsakanin Makka da Madina, sai bayan na koma Riyad da na tambayi wani dalibi sai ya ba ni fatawar cewa in yanka tunkiya a Makka. Ni kuma na ba shi uzirin cewa zuwa Makka ta yi nisa ga shi kuma ni ba mai iko ba ne, sai ya ce in yi azumin kwana goma a jere, sai na yi azumin shin hakan ya isar?
Amsa: Gaskiya ce, yanka ya kama ka wanda dole sai a Makka za ka yi shi, amma da ka ce ta yi nisa sai ya ba ka fatawar ka yi azumi. Wannan kuskure ne, babu wani azumin kwana goma da za ka yi matukar kana da ikon yin yanka. Sai dai idan ba ka da iko, to babu laifi don ka yi azumi. Da ma wanda ba ya da abin da zai yi yanka shi aka bai wa damar yin azumi. Amma idan kana da iko, dole ka je ka yi yanka ko kuma ka tura da kudin wani ya yanka maka ya rabar maka da naman.
Tambaya: Shin mace tana da wasu kebabun kaya ne da za ta yi harama da su, kuma mene ne hukuncinta idan ta yi harama da fararen kaya?
Amsa: Mace da namiji matsayinsu daya ne wajen harama. Bai halatta ta yanke farce ba, bai halatta ta fitar da gashin kanta ba, bai halatta ta rufe fuskarta ba idan ta yi harama, sai dai idan ta ji tsoron kada maza su dame ta da kallo. Amma game da launin kayan da za ta yi harama da su ba a kebe wasu kaya na musamman ba, za ta iya harama da kowane irin kaya, kore ko fari ko baki, ko ma dai wane launi ne, kawai dai ba a so ta yi harama da kayan ado wadanda za su ja hankali, domin wajen Allah ta zo kamata ya yi ta yi shiga ta kankan da kai.
Tambaya: Shin ya halatta mace ta yi harama alhali tana sanye da kayan ado?
Amsa: Babu laifi mace ta yi harama tana sanye da zobe ko a hannunta akwai wani abu na zinare, haramarta ta yi sai dai ana so ta rufe shi kada ta bayyana adonta.