Tambaya: Mene ne hukuncin mutumin Makka wanda yake so ya yi Umara, zai yi harama daga gidansa ne ko sai ya je Tan’im ko Ja’aran zai daura harami?
Amsa: Bai halatta ya yi harama daga gida ba, idan ya yi haka sai ya yi yanka (fidiya), sai dai ya yi harama daga Hillu, domin ko a ina bangaren gidansa yake abin da ake so shi ne ya fita wajen gari ya yiwo harama daga can.
Tambaya: Mu mutanen Makka ne, mun saba kowane watan Ramadan muna yin Umara amma daga gidajenmu muke daukar Harama, sai kuma mu tafi Tan’im mu dauki niyya, shin hakan da muka yi ya yi ko dole sai a Tan’im za mu daura Harami ?
Amsa: Abin da kuka yi ya yi babu laifi, matukar cewa ba ku yi niyyar Umara ba sai a Hallu, to hakan ya halatta, insha Allah babu laifi.
Tambaya: Matata ta zo daga Gabas da dadewa ba ta yi Umara ba, sai yanzu take so ta yi, shin sai na mayar da ita inda Mikatinsu yake ta yi Harama, ko ta yi Haramarta a Makka tunda a nan muke a zaune ?
Amsa: Idan lokacin da ta shigo ba ta shigo ne da niyyar yin Umara ba, saboda a nan kuke a zaune, to, idan za ta yi Umara ba sai ta koma wajen Mikatinsu na asali ba, sai kawai ta yi Harama daga Tan’im, tunda daga baya ta yi niyyar Umarar, sai kawai ta yi a Tan’im wajen da yanzu ake kira da Masallacin Nana A’isha.
Tambaya: Idan muka zo daga garinmu muka yi Umara, bayan mun huta sai muke so mu sake yin wata Umarar alhalin muna cikin Makka, shin a gidajenmu na Makka za mu yi Harama ko a Tan’im ko a wajen Mikatimmu na asali ?
Amsa: Maimaita Umara a lokaci guda bai halatta ba, sai dai ku yawaita Dawafi da Sallah da addu’a, a maimakon mai-maita Umara. Mutukar ka zo daga garinku ka yi Umara daya ta Ramadana ta isar maka.
Amma idan ka zo ka yi Umara ba ta Ramadana ba, sai ka so ka zauna ka samu ta Ramadana, babu laifi kan hakan sai dai ba za ka yi Harama daga gidanka ba, sai ka yi Harama daga Tan’im ko Ja’aranata, ko daga Arafa, wato ka fita bayan gari ka samu tafiyar wasu ’yan mila-milai. Amma wajen da ya fi maka kusa shi ne Tan’im, ka yi Haramarka daga can ka zo ka yi Umara, wannan muna magana ne idan dama ba ka zo don yin Umarar Ramadana ba ce. A fahimta idan ta Ramadana ce ba za a sake yin wata ba, domin sahabbai ba sa maimaita Umara sai dai su yi ta Dawafi suna Sallah suna adduo’i da karanta Alkur’ani.
Tambaya: Shin wanda ba a kewayen kasar Makka yake ba, zai zo a jirgi ya Halatta ya yi Harama a cikin jirgin idan an zo saitin inda Mikati yake?
Amsa: Kwarai ya halatta idan ya zo saitin inda Mikati ya ke a yi Harama, sai dai dole ne, sai ya yi wanka tun a garinsu idan ya zo saitin Mikatin sai ya yi niyya ya kama fadin Labbaika. Amma kamata ya yi ya tube kayansa ya sanya Hirami, da ya zo saitin wajen sai ya yi niyya, hakan ma shi ne ya fi. Domin idan ya ce sai ya zo wajen zai yi komai to kafin ya farga jirgi ya yi tafiya mai nisan da ya wuce wajen Mikatin.
Tambaya: To Idan kuma mutum ya yi niyya kafin a zo wajen Mikati fa?
Amsa: Hakan ya halatta, sai dai ba’a so. Amma in ya yi niyya ce don tsoron kada a wuce bai sani ba wannan babu komai.
Tambaya: Idan mutum ya taho ta Gabas zai zo Makka don Umara a ina zai dauki Harama?
Amsa: Zai dauki Harama ce idan ya zo saitin Mikati, idan kuma a jirgi yake sai ya yi wanka a kasarsu ko a Riyad ko ma dai a ina ne abin nufi shi ne : A yi wanka a tsabtace jiki a sanya turare Sunnah ne, idan ka hau jirgi in an kusanci Mikati sai ka sanya harami, da an zo inda Mikati yake sai ka yi niyya ka fara fadin LABBAIKA….., idan ma ka yi niyyar kafin a karaso Mikati don gudun kada a wuce saboda saurin jirgi wannan babu komai. Sayyidina Umar (RA) yakan ce da wadanda ba su wuce ta wajen Mikati ba: “Ku duba ku kirdadanci inda yake a kan hanyarku.” Buhari ne ya rawaito
Tambaya: Mun yi niyyar yin Umara daga gida inda ba kasar Saudiyya ba da muka zo filin jirgin Zaharan sai muka yi Harama, daya daga cikinmu kuwa tun a jirgi ya yi Hamarsa, wadansu kuma sai da aka sauka a filin jirgi, amma ba mu yi raka’a biyun da ake yi in za a yi Harama ba yaya hukuncin haka?
Amsa: Babu laifi domin raka’a biyun da ake yi in za a yi Harama ba tilas ba ce, idan ka yi ta, ya fi kyau, in kuwa ba ka yi ba, ba ka da wani laifi. Haramarka ta yi, kuma da wanda ya yi Harama tun a cikin jirgi da wanda sai da aka zo filin jirgi duk Haramarsu ta yi. Muna fatan Allah Ya karba.
Tambaya: Ni dalibi ne dan shekara ashirin da daya, yau kwanana uku da zuwa daga Amurka, na yi yawo a jirgi daga nan zuwa can har na iso Jiddah ba ni da Harami. Da yamma na tafi Makka a gajiye da gari ya waye sai na tafi Da’ifa don in dauki Harama a can mene ne hukuncin hakan?
Amsa: Babu laifi abin da ka aikata ka yi daidai, matukar ka zo ne don yin Umara to ka tafi inda Mikatinka yake shi ne abin da shari’a ta ce. Amma da a ce zuwan da ka yi ba ka zo ne don yin Umara tun asali ba, sai bayan da ka isa Makka sannan ka yi niyyar yin Umara sai ka yi Haramarka a Tan’im, Umararka ta yi muna fatan Allah Ya karba.
Tambaya: Mutanen gida guda ne suka sauka a Mina amma ba su yi Harama ba, mutum biyu a cikinsu suka tafi Makka don samar musu masauki, daga baya suka dawo Mina suka je suka yi wanka suka yi Harama. Yaya hukuncin wadancan mutum biyun yake inda suka shiga Makka ba su yi Harama ba, sannan suka dawo Mina suka yi Harama a can?
Amsa: Wato ke nan sun koma wajen da ya kamata a ce daga can suka yiwo Harama, babu komai kan hakan kuma hakan ma da suka yi shi ne abinda ya fi dacewa.
Tambaya: Mace ce ta zo Makka ta wuce Mikati ba tare da niyyar yin Harama ba, saboda ba ta da isasshiyar lafiya, yanzu kuma tana Makka, a ina ya kamata ta yi Harama don yin Umara?
Amsa: Matukar cewa ba ta shigo da niyyar Umara ba wata larurar ce ta kawo ta, to babu komai a kanta. Idan kuma daga baya ta yi niyyar yin Umara, sai ta yi Haramarta a Tan’im, amma idan tun farko Umara ce ta kawo ta, to a baya mun fadi cewa dole sai ta dawo inda Mikati yake ta yi Harama, idan kuwa ta yi Harama daga Makka, to sai ta yi yanka.
DSP Imam Ahmad Adam Kutubi
Zone 7 Police Headkuaters Wuse Zone 3, Abuja, 08036095723