✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (1)

Tambaya: Shin wajibi ne ga mai iko duk shekara sai ya yi aikin Hajji, ko kuwa sau daya ne yake wajibi? Amsa: Ba dole ba…

Tambaya: Shin wajibi ne ga mai iko duk shekara sai ya yi aikin Hajji, ko kuwa sau daya ne yake wajibi?

Amsa: Ba dole ba ne sai an yi duk shekara, na wajibi sau daya ne a rayuwa. Koda kuwa mutum yana da iko, ba ya zama dole a kansa, kamar yadda ya zo a cikin Hadisai da dama cewa Manzon Allah (SAW) ya tara mutane ya yi musu Huduba ya kwadaitar da su kan aikin Hajji. Sai wani Sahabi mai suna Akara’u dan Habis ya mike ya ce: “Ya Ma’aikin Allah shin duk shekara sai an yi? Sai ya ce: “A’a, da na ce eh da sai ya zama wajibi, sau daya ake aikin Hajji).

Tambaya: Wanda ya zo don yin Umara shin dole ne sai ya yi Hajjin wannan shekara? Saboda muna jin mutane suna fadar hakan shin gaske ne?

Amsa: Wannan kuskure ne, babu wanda ya fadi hakan cikin Malaman Musluunci.

Tambaya: Shin ya Halatta ga yaran da ba su kai shekara bakwai ba su yi dawafi tare da mahaifansu?

Amsa: Ya Halatta su yi haramar Hajji ko ta Umara, ko da ba su kai shekaru bakwai ba, kamar yadda ya zo a kissar matar nan Khas’imiyah wacce ta dauko karamin yaro da ke cikin shimfidar goyo (shawul) ta ce: ya Ma’iakin Allah (SAW)! Shin wannan zai iya yin Hajji? Ya ce: “kwarai kuwa amma ladan naki ne.” Ta nan aka gane cewa Umarar yaron da bai kai shekaru bakwai ba ta halatta, kuma yana iya yin Hajji da dawafi amma a matsayin nafila.

Tambaya:  Mace ce take da ’ya’ya ’yan shekaru 9 zuwa 20, kuma tana da miji ya yi Hajji amma ita ba ta yi ba, tana kuma da da balagagge, Shin Hajji ta hau kanta?

Amsa: Na’am idan tana da iko, tana da dukiya za ta iya zuwa Makka ta dawo ba tare da bashi ba, ba tare da rokon mutane ba, Hajji ya wajaba a kanta a kowane hali. danta zai iyi tafiya da ita Hajjin, amma idan talaka ce Hajji bai hau kanta ba, saboda Allah (SWT) yana cewa: “Allah Ya wajabta aikin Hajji a kan mutane ga wanda ya samu iko.” Surar Ali Imran: 97. Iko shi ne guzuri da abin hawa, a zamanin yanzu kuma guziri da kudin jirgi, idan kuma ba ta da komai to Allah ba Ya dora wa mutum abin da ba zai iya ba, wannan ana magana ce a kan Hajjin farillah.

Tambaya: Shin wajibi ne miji sai ya yi Hajji ko Umara da matarsa?

Amsa: Ya kamata ya yi Hajji da ita, ya kyautata mata amma babu batun dole, ba dole ne sai ya yi Hajji ko Umara da ita ba, kawai dai kyautatawa ce daga gare shi, ya kamata ya yi hakan, amma idan bai yi ba, ba ya da wani laifi.

Tambaya: Mene ne hukuncin wanda ya yi Hajji ko Umara ta hanyar kudin giya, saboda ba ya da wasu?

Amsa: Abu ne sananne cewa Annabi (SAW) ya yi bayani kan wannan tambayar inda yake cewa: “Hakika Allah idan ya haramta abu sai ya haramta cin kudinsa”  Shin giya haramun ce? Amsar ita ce ‘eh’ babu tantama cewar haramun ce. Sai mu ce matukar dai haramun ce, to kudinta ma haramun ne, saboda Annabi (SAW) ya ce “Allah idan Ya haramta abu sai Ya haramta kudinsa.” Don haka cin kudin giya ko amfani da su bai halatta ba. Kamar yadda mushe yake haram bai halatta a yi amfani da nama ko kitsansa ba.

A TAkAICE: Cin kudin giya haramun ne, idan hakan ta faru dole ka tuba ka yi istigfari, idan ka yi tuba na gaskiya ana sa ran Allah zai yi maka afuwa Ya gafarta maka, ita kuwa tuba tana da sharuddai uku:

– Na farko: Yin nadama kan abin da aka aikata.

– Na biyu: Ka kudurce cewa ba za ka kuma sake yin abin ba.

– Na uku: Ka yi bakin ciki kan abin da ka aikata, ka kuma nisanci aikata makamantansa.

Tambaya: Ni ma’aikacin gwamnati ne, amma tsawon shekara 20 ban yi aikin Hajji ba, yanzu kuma aiki ya yi min yawa ba zai yiwu in bar wajen aikina ba, shin zan iya wakilta wani ya yi min aikin Hajji?

Amsa: Matukar dai kana da karfi kuma za ka iya yin aikin Hajji, kamata ya yi ka nemi izini wajen shugabanninka, ka fada musu cewa har yanzu ba ka yi Hajjin wajibi ba, babu shakka za su ba ka dama sai su sa wani ya kula da aikinka, saboda Hajjin wajibi dole ne ga mai iko, don haka bai halatta ka aika wani ya yi maka ba, bayan kana da ikon yi.

Tambaya: Ina daukar nauyin Hajjin mahaifana daga garin Riyad duk shekara ina kashe sama da Riyal 3000 don a yi musu Hajji. Sai na samu wani mutumin Makka zai yi musu Hajji da Umara a Riyal 2000, shin hakan ya halatta kuma wanne ne ya fi?

Amsa:  Idan a Riyad din ka samu mutumin kirki mai tsoron Allah da zai yi cikakken Hajji, ina gani kamar zai fi saboda abin da aka fi bukata shi ne mutumin kirki nagari, ya karbi abin da yake ganin zai ishe shi har ya gama aikin Hajjinsa, ina ganin babu laifi, kuma Allah zai karba Ya ba ka lada.

DSP Imam Ahmad Adam Kutubi 

Zone 7 Police Headkuaters Wuse Zone 3, Abuja, 08036095723