✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Tambayoyi 10 da Shugaba Buhari zai amsa da kansa

Tamaboyin da idan Buhari ya masa su ’yan Najeriya za su sauyi a zahiri kuma su shaida

Tabbas idan ka ji korafi akwai rashin gamsuwa kamar yadda in dai ka ji tambaya akwai abin da ya shige wa mutum duhu.

Assalamu Alaika Ya Shugaba Muhammad Buhari. Shugaban Najeriya.

Duba da ya yanayin yadda lamarin tsaro da sauran harkokin rayuwa, wadanda sai da rai da lafiya ake batunsu suka kara tabarbarewa a Najeriya, musamman a Arewa; Yadda batun ta’addanci da zullumin kai farmaki a garuruwa da hanyoyi da wajajen noma da sauran wuraren neman halak (kasuwanni) suka kara jefa rayuwar takala cikin kunci, sune dalilan rubuta wannan wasika ‘Kai-Tsaye’ cikin girmamawa gare ka.

Abin da ya sa wannan wasika ta zama ‘Kai-Tsaye’ kuma da sigar tambaya gare ka ya Shugaban Najeriya Muhamnadu Buhari shi ne: Mu dai a Musulunci mun kwana da sanin cewa akwai abin da aka yarda wani zai iya yi a madadin wani, yayin da wani lamarin kuma kowa sai dai ya yi wa kansa, ma’ana wani ba ya wakiltar wani.

Haka kuma, su kansu a abubuwan da ake iya bada wakilcin matukar akwai abin da ya shiga duhu tsakanin wanda aka aika wa wakilin da kuma wakilin, akwai damar tafiya kai tsaye zuwa ga wanda ya bada wakilcin, wannan shi ne dalilin neman wannan amsar daga gare ka, ya shugabanmu, Muhammadu Buhari, domin kai ne wanda al’umar Najeriya muka damka wa mmanar jagorantar mu.

Mai Girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ka san cewa kowane dan Adam gajiyayye ne kuma ajizi ne — yakan dada himma ko ya rage a al’amuran rayuwa.

Hakan ya sa nake da yakinin cewa amsa wadannan tambayoyi guda 10 da kanka, ko ba komai wata hanya ce da za ka san matsayin da kake wanda mu kuma ’yan Najeriya za mu fa’idantu wajen ganin sauyi a zahiri yayin da Allah Ya ba ka ikon amsawa kanka-da-kanka wadannan tambayoyi wadanda ba sa bukatar wakilcin wani mukarrabinka.

Ga Tambayoyin daya-bayan-daya, wadanda Allah Ya sa ni ban yi su da kudurin izgili ko wata boyayyiyar manufa ba, face ganin al’amuran kasa sun gyaru, wadan da kuma nake fatan za su samu duba na tsanaki.

  1. Ya Shugaba Muhammadu Buhari, anya kuwa kana iya tuna yadda a baya kafin mu zabe ka, ka dinga kushe shugabannin baya saboda abin da mu da kai (a lokacin0 muka yarda cwea sakaci ne wajen iya jagorancin ’yan Najeriya?
  2. Anya kuwa kana tuna yadda ka dinga bibiyar ’yan Najeriya domin mu yarda za ka iya share mana hawaye har muka aminta muka ba ka amanar kanmu da ta rayuka da dukiyoyinmu da hakkin kare mutuncinmu a 2015?
  3. Shin kana iya tuna rahotannin yadda tsofaffi da mata masu juna biyu da wadansu daga cikin marasa lafiya a gida da asbitoci suka rarrafa suka je suka wuni a layin zabe cikin kishurwa da yunwa da zafin rana domin zabar ka?
  4. Anya kuwa Kana iya tuna yadda talakawan Najeriya suka ki ci, suka ki sha, suka sayen kati da kudadensu domin aika maka da tallafin kudi domin ka kai ga nasara a zaben 2015?
  5. Kana iya tuna yadda rashin lafiya wadda tana kan kowa ta same ka, jim kadan bayan an zabe ka, talakawan da suka zabe ka suka kasa zaune, suka kasa tsaye a gidajensu da makarantunsu da masallatai da majalisu dare da rana suka dinga yi maka addu’a domin ka samu lafiya ka futar da su daga takaici?
  6. Ya Shugaba Buhari, a matsayinka na Musulmi, kana iya tuna kalaman da ke cikin rantsuwar kama mulki da ka saba lokutan rantsar da kai a Abuja da sauran jawaban da kayi a ranar?
  7. Shin ka ma yarda kuwa cewa Najeriya da ’yan Najeriya musamman talakan Arewa na cikin mawuyacin hali da zullimi sabodra rashin tsaro?
  8. Shin kana sane da cewa yin tattaki domin jajantawa da yin sannu hadi da addu’a ga wanda ke cikin damuwa ko da ba zai samu waraka ba abu ne mai dadi ga wanda ke cikin irin wannan hali? A lokacin ka kwanta rashin lafiya a Landan talakawa sun yi ta yi maka addu’a har da yin yanka da bada sadaka, wanda na san a lokacin in da a ce birnin Landan kamar nisan Jakara zuwa Gauron Dutse yake, da duk da ba za a ba su damar ganin ka ba, da sun yi dafifi a garin da kake jinya domin nuna alhini, amma ga shi yanzu kai jirgi kawai za ka hau ka je ka jajanta wa Katsinawa da Sakkwatawa da sauran gururuwan Arewa amma abin ya faskara.
  9. Har ila yau, a matsayinka na Musulmi wanda ya samu tarbiyyar kasar Hausa, ya yi makarantar addini kamar yadda duk Musulmi ke yi, anya ka yarda cewa akwai hisabi bayan mutuwa kuma a cikin hisabin za a tambaye ka duk abin da ka yi da ma wanda ka ki yi wanda a dalilin hakan rayukan mutane da mutuncinsu suka salwanta?
  10. Shin sai yaushe kake zaton alkawura da kuma kyawawan kudurori da ka zawarci kuri’un ’yan Najeriya da su sa zu cika; In kuma kai kanka ya yanke tsammani — abin ya fi karfinka — to yaushe za ka yi wa ’yan Najeriya bayani kai tsaye saboda mu san mataki na gaba?

Wadannan su ne tambayoyin, kuma kana iya kallon su a matsayin tuhumar da in dai Allah Ya ba ka iko ka iya amsawa da kanka kuma ka dauki matakin da ya dace yanzu-yanzu to kuwa nan take mu ma za mu ji amsar a jikinmu da kuma ganin amsar da idanunmu, domin amsar tambayoyin kamar yadda nace, a aikace ’yan Najeriya za mu gani.

Allah Ya ba ka ikon dubawa da na daukar matakin da ya dace a kan lokaci.

Kowane dan kasa da iyakacin aikin da kundin mulki ya sahale masa, wannan shi ne nawa hurumin, a matsayina na dan jarida mai fatan ganin kasata, Najeriya ta kyautatu.

– Kwamred Salisu Ismail Kabuga
[email protected]
+2348052529040
12/12/2021.