✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambaya ba amsa

Wani sabon malami ne aka kawo shi wata makarantar sakandare, domin ya koyar da Tarihi. Shigarsa aji ke da wuya sai ya ce wa wani…

Wani sabon malami ne aka kawo shi wata makarantar sakandare, domin ya koyar da Tarihi. Shigarsa aji ke da wuya sai ya ce wa wani dalibin: “Tashi tsaye, shin wa ya kashe Murtala Ramat Muhammad?” dalibin ya ce: “Malam, ban sani ba wallahi.” Sai ya tambayi dalibi na biyu, shi kuma sai ya ce: “Malam, ranar da aka kashe shi ban zo makaranta ba.” dalibi na uku kuma ya ce: “Wallahi ni sabon zuwa ne makarantar nan.” Malamin ransa ya vaci, sai ya kirawo shugaban makarantar ya gaya masa abin da ya faru, sai shugaban makaranta ya tambayi ’yan ajin ga baki dayansu, suka ce ba su sani ba. Sai shugaban makaranta ya juwo, ya ce wa malamin: “Kai malam, ka tabbata da gaske a nan ajin aka kashe Murtala Ramat Muhammad?”

Daga Malam Babaji Na Ummi Hadeja, 08108484300