Gwamnatin Tarayya ta ce tana harsashen za ta iya kashe Naira biliyan 900 wajen biyan kudaden tallafin mai a shekarar 2022.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da take kokarin yin kasafin kudin da ya kai kimanin Naira tiriliyan 13.91 a shekarar mai zuwa.
Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare, Hajiya Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan ranar Alhamis a yayin taro kan Tsare-tsaren Kashe Kudade na Matsakaicin Zango na 2022 zuwa 2024 wato MTEF/FSP.
Ta kuma ce za a sami gibin kaso 3.05 cikin 100 a kan kasafin bana.
“Jimlar ainihin kasafin kudin shine tiriliyan 11.90, amma idan ka hada da sauran hanyoyin shigowar kudade na gwamnati zai koma tiriliyan 13.91, sabanin tiriliyan 13.58 na 2021. Amma a 2023, kasafin zai koma tiriliyan 15.45, sai tiriliyan 16.77 a 2024. Sai dai a 2022, za mu sami gibin kaso 3.05 cikin 100, ko da yake ci gaba ne in aka yi la’akari da yadda aka sami gibin kaso 3.91 a 2021,” inji ta.
Ministar ta kara da cewa, “Samar da kudaden kasafin kudin zai kunshi cefanar da wasu kadarorin gwamnati da kuma ciyo bashi daga cibiyoyin kudi a ciki da wajen kasa domin cike gibin Naira tiriliyan 5.62 a 2022 da kuma makamancin wannan adadin a 2023. Kaso 50 cikin 100 na basussukan za a ciyo su ne a cikin gida, ragowar 50 din kuma daga ketare.
“Amma ya zama wajibi mu cire tallafin mai saboda kusan dukkan kasashe makwabtanmu mu ke biya wa tallafin, ba wai Najeriya kawai ba.
“’Yan tsirarun mutane ne suke da motocin hawa a Najeriya, mafi yawancin talakawan da ya kamata su amfana da tallafin, motocin haya suke hawa. Kusan gaba daya ma basa amfana da shi ta kowacce fuska,” inji Ministar.
Sai dai ta ce Gwamnatin Tarayya na duba yuwuwar fito da wani tsari da zai rage wa wadanda cire tallafin zai shafa radadin cirewar.
“Mun san wasu za su sha wuya in muka cire, wanne tanadi muka yi musu? Me za mu samar wa ’yan kasa? Saboda haka muna lissafin in muka kashe Naira biliyan 900, ba karamin amfani zamu iya yi da su ba.
“Makarantu da asibitoci nawa za ka iya ginawa? Babu dabara sam in muka ci gaba da biyan wadannan kudaden da sunan tallafi,” inji ta.