Tsohon ɗan Majalisar Wakilai daga Jihar Kano, Faruk Lawan, ya fito daga gidan yari bayan kammala zamam wankafin shekara biyar kan laifin karbar cin hanci.
A ranar Talata aka sallami Faruk Lawan daga Gidan Yarin Kuje da ke Abuja, inda aka tsare shi bayan samun shi da laifin karbar cin hancin Dala 500,000 da kotu ta yi a shekarar 2021.
Kotu ta kama shi ne da laifin neman cin hancin Dala miliyan uku daga fitaccen attajiri kuma shugaban kamfanin Zenon Oil, Femi Otedola, a shekarar 2012.
- Babban layin lantarkin Arewa ya sake ɗaukewa
- Diyyar N100bn: Matatar Ɗangote ta janye ƙarar da ta maka NNPCL
Faruk Lawan ya tsinci kansa a Gidan Yarin Kuje ne bayan da kotu ta same shi da laifin nema da kuma karbar cin hancin Dala 500,000.
Dan majalisar ya aikata laifin ne a lokacin da tsohon dan majalisar ke jagorantar kwamitin binciken bakalar tallafin man fetur.
A watan Janairun 2024 ne Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin da aka yanke masa na zaman shekara biyar a gidan yari kan laifin karbar na-goron.
Bayan fitowarsa daga gidan yari, Faruk Lawan ya ce, “Yau an bude wani sabon babi a rayuwata, da fitowata daga Gidan Yarin Kuje, kuma ina godiya ga Allah da Ya ba ni wanna dama.
“Na gode wa Allah da Ya bar ni a raye cikin koshin lafiya domin sake haduwa da iyalaina da abokan arziki. Ina matukar godiya game da hakan.