✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tallafin mai: Dole ’yan Najeriya su yi murna —Kungiyar Kwadago

NLC ta kuduri aniyar fara gagarumar zanga-zanga da zarar gwamnati ta kara kudin mai.

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta bayyana dakatar da yunkurin Gwamnatin tarayya na janye tallafin man fetur a matsayin abun farin ciki ga ’yan Najeriya.

Da yake zanta wa da menam labarai, Shugaban kungiyar Reshen Jihar Kano, Kabiru Ado Minjibir, ya ce abun a yi murna ne saboda cire tallafin zai haifar da karin tsadar man fetur wanda hakan zai jefa miliyoyin mutane cikin tsaka mai wuya.

Minjibir, ya yi wannan jawabi ne yayin da yake yi wa mambobin kungiyar bayani dangane da yadda gwamnati ta yi mi’ara koma baya game da janye kudurin karin kudin mai.

Aminiya ta rawaito yadda Kungiyar Kwadago ta Najeriya Reshen Jihar Kano tare da hadin gwiwar kungiyar ’yan kasuwa suka shirya shiga babbar zanga-zangar da aka shirya yi wa Gwamnatin Tarayya kan batun karin kudin man fetur.

Kungiyoyin sun shirya sanya kafar wando daya da gwamnatin ne a kan shirinta na kara kudin man fetur da kuma janye tallafi a kansa, wanda aka dade ana tirka-tirka a kai.