✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Taliban za ta soma sayen makamashi daga Rasha

Taliban ta kammala kwangilar sayen alkama, gas da mai daga Moscow.

Gwamnatin Taliban na kan matakin karshe na tattaunawa a birnin Moscow, kan batun kwangilar sayen man fetur da gas daga kasar Rasha.

Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito mai magana da yawun Ma’aikatar Tattalin Arzikin Afghanistan, Habiburahman Habib yana tabbatar da hakan a ranar Litinin.

Ya sanar cewa wata tawaga ta Ma’aikatar Kasuwanci ta kasar Afganistan ce ta ziyarci birnin Moscow, inda ta kammala kwangilar samar da alkama, gas da mai.

Ya zuwa yanzu gwamnatin Moscow ba ta yi martani ba, amma wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da Amurka ke kokarin shawo kan sauran kasashen duniya da su daina amfani da man Rashar.

Amurka da sauran kasashen Yamma sun cije kan aniyarsu ta dakile kudaden shigar man da Moscow ke amfani da shi wajen mamaye kasar Ukraine.

A halin da ake ciki dai kasashen Rasha da Afghanistan wadda Taliban ke jagoranta, na fuskantar takunkumin tattalin arziki daga gwamnatocin kasashen duniya ciki har da Amurka.