Kungiyar Taliban mai iko da Afghanistan ta zargi Amurka da kawo yamutsi a wurin jigilar kwashe dubban ’yan Afghanistan da sauran kasashen ketare da yanzu haka suka yi cirko-cirko a filin jirgin saman Kabul.
Wani jami’in Taliban, Khan Mutaqi ya sanar a ranar Lahadi cewa abin mamaki ne a ce duk da karfin ikon da Amurka ke da shi a duniya amma ta kasa kawo daidaito a filin jirgin saman Kabul.
- Ambaliya ta yi ajalin mutum 26, ta rusa gidaje 2,026 a Kano
- ’Yan bindiga sun sace basarake a Zamfara
Jami’in na Taliban ya ce a cikin sassan kasar Afghanistan akwai zaman lumana, filin jirgin saman Kabul ne kawai ke cikin rudani.
Haka na zuwa ne a daidai lokacin da Kungiyar Tarayyar Turai EU ke gargadin cewa mai yiwuwa su gaza kwashe kowa daga kasar cikin lokacin da ake bukata.
Kusan mako guda bayan da kungiyar Taliban ta dare kan karagar mulki, dubban mutane na ci gaba da kokarin barin Afghanistan a cikin yanayin jigilar jiragen sama da ya zama daya daga cikin mafi wahala a tarihi.
Hotunan bidiyo sun nuna yadda mutane cikin zafi da tirmitsitsin tare da iyalansu ciki har da kananan yara ke shafe sa’o’i suna jiran sojojin Amurka su basu damar shiga filin jiragen sama na Hamid Karzai da ke birnin Kabul domin ficewa daga Afghanistan.
Batun kwashe mutanen dai na ci gaba da daukar hankulan mutane, inda a baya-bayan tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ya soki Shugaba Joe Biden da yi wa Amurka abin kunya dangane da kwaso mutanen da ke cikin hadari a Afghanistan.
Haka ma dai lamarin yake a nan Jamus, inda wasu ke nuna rashin jin dadinsu kan yadda Jamus din ta nuna kasala wurin kwaso mutanenta a kankari.
Ma’aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon ta ce kawo ranar Asabar mutane 17,000 aka kwashe daga Kabul tun bayan da Taliban ta kwace iko da kasar.
A kan haka ne kungiyar ’Yan Jaridu ta kasa da kasa RSF, ta bukaci Shugaba Biden ya tsara shiri na musamman domin kwashe ’yan jaridar Afghanistan da ke cikin hatsari daga birnin Kabul da ke karkashin ikon Taliban.
RSF ta ce a halin yanzu Amurka ta damu ne kawai da kwashe ’yan kasarta da tsoffin ma’aikata daga Afghanistan.
Kungiyar ’Yan Jaridun ta Duniya ta ce yanzu haka ta samu daruruwan takardun bukatar taimako daga ’yan jaridar Afganistan, galibinsu mata, wadanda ke cikin firgici da fargaba.
’Yar Afghanistan ta haihu a cikin jirgi
Wata ’yar Afghanistan ta haifi jaririya ’yan mintuna bayan sauka a sansanin sojan saman Amurka na Ramstein da ke Jamus ranar Asabar.
Cikin wani sakon Twitter, rundunar sojan Amurka ta ce matar ta fara nakuda ne a cikin jirgin soja na C-17 ana tsaka da tafiya bayan sun tsere daga kasar.
Jirgin ya taso ne daga wurin da ya yi zango a Gabas ta Tsakiya zuwa Jamus.
“Matukin jirgin ya sassauto kasa domin ya kara yawan iska a cikinsa, abin da ya taimaka aka ceci rayuwar uwar jaririyar,” a cewar sakon.
Ya kara da cewa an kai uwar da jaririyarta wani asibiti da ke kusa jim kadan bayan sun sauka kuma suna cikin koshin lafiya.
Ya zuwa yanzu, an kwashe dubban ’yan Afghanistan daga kasar zuwa kasashen Turai da na Gabas ta Tsakiya saboda gudun mulkin Taliban.
Amurka ta fara kwaso mutanenta da jiragen fasinja
Amurka ta bayar da umarnin amfani da jiragen dakon fasinjoji goma sha takwas cikin gaggawa don kwaso mutane daga Afghanistan.
Wata sanarwa da ta fito daga ma’aikatar tsaron Amurkar ta ce jiragen ba za su je Kabul ba amma za a yi amfani da su wajen daukar mutanen da aka dauke daga Kabul aka kai su wasu sansanonin sojojin Amurka a Gabas ta Tsakiya.
Haka kuma, sanarwar ta ce wannan zai ba jiragen soji damar mayar da hankali kan dakon mutane daga Kabul zuwa sansanonin.