✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Taliban ta yi gargadi kan sanya wa Afghanistan takunkumi

Taliban ta ce takunkumin na iya haifar da barazana ga sha'anin tsaro.

Gwamnatin Taliban a Afghanistan ta gargadi manyan kasashen duniya  game da matakan da suka dauka na sanya mata takunkumin karya tattalin arziki.

Taliban ta ce hakan zai iya kara tsananta matsalar tsaro baya ga kara yawan ’yan gudun hijira da za su bazu zuwa wasu kasashe.

Ministan Harkokin Wajen Afghanistan, Amir Khan Muttaqi ne ya shaida wa wakilan kasashen yammacin duniya hakan a tattaunawarsu a Doha, babban birnin kasar Qatar.

Ya kara da cewa gurgunta gwamnatin Taliban ba Afghanisatan kadi zai shafa ba, domin kuwa zai kara matsalar tsaron da duniya ke fuskanta.

A watan Agustan da ya gabata ne Taliban ta hambarar da gwamnatin  Shugaba Ashraf Ghani mai samun goyon bayan Amurka wanda ya kawo karshen rikicin shekara 20 da Afghanistan ta yi fama da shi.

Sai dai matsalolin rashin kudin shiga sun dabaibaye kasar musamman bayan kulle mata asusun ajiya da manyan kasashen suka yi da kuma katse tallafin da take samu.

Har wa yau, kokarin Taliban na dawo da zaman lafiya a kasar na fuskantar babbar barazana daga mayakan IS.

Matsalar tattalin arziki kuma na ci gaba da tsananta sakamakon takunkumin manyan kasashen duniya a kan kasar, wanda ya haddasa karanci kudi a ilahirin bankunan Afghanistan.

Ministan harkokin wajen Afghanistan, a yayin zantawarsu a Doha ya ce matukar kasashen duniyar na bukatar zaman lafiyarsu, dole su janye takunkuminsu a kan Afghanistan wanda zai ba ta damar tafiyar da harkokinta musamman al’amuran da suka shafi tattalin arziki.

Muttaqi ya roki kassahen su bai wa kasarsa damar tafiyar da harkokin kudi a bankuna baya ga sahale ayyukan agaji don ceto kasar daga durkushewa.