Kungiyar Taliban wadda ta kwace iko a kasar Afghanistan, ta nemi gwamnatin Pakistan ta haramta wa Amurka amfani da sararin samaniyarta.
Mukaddashin Ministan Tsaro na gwamnatin Taliban, Mullah Mohammad Yaqoob, ya nemi makwabciyarsu Pakistan ta daina bari Amurka na amfani da sararin samaniyarta tana kai hari da jirage marasa matuka cikin kasarsa.
- Yadda wani dattijo ya yi auren fari bayan shafe shekara 74 a duniya
- An dakatar da matuka jirgi saboda bai wa hammata iska a sararin samaniya
A watan jiya ne Amurka ta harba wani makami mai linzami da jirgi maras matuki, wanda ya kashe shugaban kungiyar al-Qaeeda, Ayman al-Zawahiri a Kabul.
Mullah Yaqoob ya ce: “A bayanan da muka samu, Amurka ta yi amfani da sararin samaniyar Pakistan suka shiga Afghanistan.
“Muna son su daina bayar da wannan dama ga magautanmu.”
Minista a Ma’aikatar Harkokin Wajen Pakistan, Bilawal Bhutto-Zardari, ya ce a iya bincikensa Amurka ba ta yi amfani da sararin samaniyarsu ba wajen kai harin da ya yi ajalin al-Zawahiri.
Ita ma gwamnatin kasar ta musanta hannu ko masaniya kan harin da ya yi sanadin mutuwar jagoran na al-Qaeeda.
Sai dai Kakakin Hukumar Leken Aissiin Amurka, Ned Price, ya ki cewa uffan a kan lamarin.