✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taliban ta haramta yi wa mata auren dole a Afghanistan

Mutane sun fara nuna damuwa kan yadda Taliban ke danne hakkin mata a kasar Afghanistan

Gwamnatin Taliban ta kafa sabuwar doka da ta haramta yi wa mata auren dole a kasar a Afghanistan.

Sabuwar dokar da gwamnatin ta fitar ta kuma hana tilasta wa mata yin aure, tare da yin bayani kan mallakar dukiya ga macen idan mijinta ya rasu.

Sai dai kuma dokar ta umarci mata da su zauna a gida ba tare da zuwa makaranta ba, ko fitowa a shirye-shiryen gidajen talabijin a kasar.

Mutane da dama a kasar sun shiga damuwa tare da kokawa kan yadda suka ce dokokin Taliban din suke danne hakkokin matan kasar.

Tun bayan da Taliban ta karbi jagorancin kasar a watan Agusta, take fito da sabbin dokoki da suka shafi yadda mutanen kasar za su gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.