✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Taliban ta haramta wa mata zuwa wuraren shakatawa

Gwamnatin Taliban ta haramta wa mata zuwa wuraren shakatawa da sauran wuraren nishadi a fadin kasar Afghanistan. Kakakin hukumar Hisbah, Muhammad Akif Muhajir, ne ya…

Gwamnatin Taliban ta haramta wa mata zuwa wuraren shakatawa da sauran wuraren nishadi a fadin kasar Afghanistan.

Kakakin hukumar Hisbah, Muhammad Akif Muhajir, ne ya bayyana haka a hirarsa da ya yi da wani gidan rediyo a kasar, a kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

Muhajir ya ce, sama da watanni 14 zuwa 15 suna kokarin samar da yanayin da mata a kasar za su iya fita zuwa wuraren shakatawa a bisa tsarin Musulunci amma hakan ya faskara.

“Abin takaici ne masu wadannan wurare ba su ba mu hadin kai yadda ya kamata ba, su ma matan ba sa son su sa hijabi kamar yadda ya kamata, don haka muka yanke wannan hukunci,” in ji kakakin Hisban.

Kusan duk matan kasar na daura mayafyi ko hijab in za su fita, wasu kuma ba sa sanya nikabi, wasu kuma sanyawa.

Gwamnatin Taliban ta dage sai matan su rika rufe jikinsu baki daya a duk lokacin da za su fita bainar jama’a.

Gwamnatin Taliban na shan suka daga gwamnatocin kasashen Turai, kan cewa, sai ta sauya matsayin da ta dauka, wanda a cewarsu tauye hakkin mata ne.