✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Talauci ya sa Darakta ya kashe kansa a Kogi

Wani babban jami’i a Hukumar Malamai ta jihar Kogi da ya kai matakin darakta mai suna Edward Soje ya kashe kansa ta hanyar rataye kansa…

Wani babban jami’i a Hukumar Malamai ta jihar Kogi da ya kai matakin darakta mai suna Edward Soje ya kashe kansa ta hanyar rataye kansa a wata bishiya a garin Lakwaja.
Aminiya ta gano cewa an sami gawar ma’aikacin na lilo a sakale da bishiya a bayan kasuwar barikin soja na Chari Maigumeri da ke garin Lakwaja.
Wata majiya da ke kusa da iyalansa ta bayyana cewa kafin aukuwar lamarin ma’aikacin gwamnatin na fuskantar kalubalen rashin kudi.
Aminiya ta gano cewa lamarin ya auku ne kwana goma da matar marigayin wanda suka yi aure kimanin shekaru 17 ba tare da samun haihuwa ba ta haifi ’ya’ya uku a wani asibiti da ke garin Abuja.