✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Talauci na kara hauhawa a Najeriya

A wani rahoto da Bankin Bunkasa Afrika (AfDB) ya fitar, ya nuna cewa mummunan talauci ya karu a Najeriya. Kamar yadda ya ce, yawan al’ummar…

A wani rahoto da Bankin Bunkasa Afrika (AfDB) ya fitar, ya nuna cewa mummunan talauci ya karu a Najeriya. Kamar yadda ya ce, yawan al’ummar da ke rayuwa cikin talauci ya karu daga kashi 65.5 cikin 100 a 1996 zuwa kashi 69 cikin 100 a 2010. Bayan haka ma, rahoton ya bayyana yadda ake samun rashin daidaito wajen yadda ake rarraba adadin dukiyar da kasa ke samu zuwa ga al’ummar kasa.
Duk da cewa gwamnati ta musanta gaskiyar wannan rahoto, to amma sakamakon rahoton bai saba da dukkan wasu rahotanni irinsa da aka taba samu ba a sakamakon nazari da bincike. Gwamnatin Tarayya ta yi Allah-wadai da rahoton AfDB amma kuma abin mamaki, sai ga shi Babban Bankin Najeriya ya fitar da kwatankwacin irin wannan rahoton, sannan kuma Cibiyar kididdiga Ta kasa, ta fitar da rahoton da ya fi dukkan wadannan na baya muni.
A yayin da gwamnati ke musanta wannan rahoto, su kuwa al’umma ba su ga hikimar yin haka ba, musamman idan aka yi la’akari da yadda tattalin arzikin kasar nan ke kara tabarbarewa. Wani abin takaici ma shi ne, yadda rahoton ya tabattar kuma ya nuna yadda kananan yara ke cikin matsalolin rayuwa daban-daban a kasar nan, yadda yunwa da rashin ingantaccen abinci ke kawo masu nakasu wajen rayuwa. A wasu kasashen da suka ci gaba, sai da suka tsaro shirin ciyar da yara abinci a makarantu, domin dai gwamnati ta taimaka wajen sama masu ingantaccen abinci mai gina jiki.
Wace irin gwamnati ce wannan, wacce za ta ware dinbin kudi wajen abincin manyan jami’anta, sannan ta ware kaso mafi tsoka wajen gina zauren shakatawar jami’anta, amma ta kasa yin abin kirki wajen bunkasa ci gaban al’ummarta? Lallai kam lokaci ya yi da gwamnati ya kamata ta kawo karshen wannan tabargaza da lalata dukiyar cal’umma. Idan mun kara duba rahoton, ya kara bayanin cewa Najeriya kasa ce mai dinbin arziki amma al’ummarta kuma matalauta ne tutur. kasa ce wadda gibi tsakanin attajirai da matalauta sai kara fadi yake yi. Haka ma rayuwar ’yan kauye da mazauna birane take ta kara bambanta sosai. Duk gwamnati da ke son hana yaduwar talauci a kasa kuma take son dakile rige-rigen da mazauna karkara ke yi zuwa birane, ya zame mata wajibi ta tashi tsaye wajen yin adalci wajen rarraba arzikin kasa yadda ya dace, tsakanin al’ummarta da kuma tsakanin birane da karkara. Haka kuma rahoton dai ya sake bayyana irin yadda ake samun rashin daidaito ta fuskar rarraba tattalin arziki tsakanin al’ummun birane da na karkara, wanda haka ya tabbatar da cewa gwamnatin na fifita killace dukiya fiye da mayar da hankali wajen kula da jin dadin al’umma. Zahiri dai abin da haka ke nunawa shi ne, a yayin da gwamnatin kasa ke kara azircewa, su kuma al’umma suna kara talaucewa. Babban kuma abin da wannan tsari ya haifar shi ne, ya samar da tsirarun ’yan kasa masu dinbin dukiya, wadanda ba su yin wani yunkuri wajen bunkasa dukiyar, ta yadda sauran al’umma za su amfana. Haka kuma a sakamakon wannan tsari, gwamnatin ta zama marar kula da talakawanta, kuma ba ta nuna jinkai wajen tallafar al’ummarta.
Abin fahimta a nan shi ne, duk da yadda gwamnati da jami’anta suka kai matuka wajen rashin amincewa da rahoton nan na bankin AfDB, babu yadda suka iya karyata ingancin rahoton a zahiri. Hasali ma, maimakon karyatawa sai ma gaskiyar rahoton ta kara bayyana karara. Wani abin lura a kasar nan shi ne, al’amarin barace-barace da neman maula, wanda aka sani kawai ga almajirai da sauran nakasassu, yanzu ya zama ruwan dare, inda za ka ga katti majiya karfi kuma lafiyayyu, masu ilimi, amma suna bara da maula. Haka kuma, abin kyama ne yadda rashin aiki ya ta’azzara a kasar nan, yadda a duk shekara, dubban daliban da ake yayewa a jami’o’i ke ragaita babu aikin yi a tituna. Babu kasar da ke son ci gaba da za ta sanya ido ta ga haka na faruwa a cikin al’ummarta. Irin yadda talauci ya yi katutu ga al’ummar kasar nan, wani abin juyayi ne, kuma wata balahira ce da ke neman dulmiyar da kasar nan zuwa ga halaka. Don haka ya dace a yi maza a shawo kan al’marin tun kafin a makara.
Ya dace gwamtai ta yi maza ta shigo da ingantattun shirye-shiryen bunkasa tattalin arzikin kasa, ta fito da tsari da shirye-shiryen samar da ayyukan yi da dubarun rarraba arziki ga ’yan kasa daidai yadda ya dace, ta yadda za a magance talauci. Ta haka ne kawai kasa za ta bunkasa kuma al’ummarta ta bunkasa cikin jin dadi da walwala.