✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Talauci da rashin aikin yi ne dalilan matsalar tsaro a Najeriya —Obi

Dole mu fuskanci matsalar da muke gani a yau.

Dan takarar Shugaban Kasa a karkashin Jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya danganta talauci da kuma rashin aikin yi a matsayin dalilan matsalar tsaro da ke ci gaba da ci wa kasar nan tuwo a kwarya.

Obi ya ce duk kasar da ta bar talakawanta cikin talauci, dole jama’arta su fuskanci kalubale na zaman kashe wando da ke haifar da matsaloli musamman irin na tsaro da ake fuskanta a kasar nan.

Dan takarar ya bayyana haka ne a wajen babban taron da Cocin Christ ya shirya a kan masu takarar shugabancin kasa ranar Litinin a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.

Tsohon gwamnan na Jihar Anambra ya ce a halin yanzu akwai ’yan Najeriya miliyan 100 da ke fama da rashin aikin yi.

A cewarsa, “Babu yadda za a yi a samu mutum miliyan 100 da suke rayuwa cikin talauci a kasa ba tare da an fuskanci matsaloli ba, muna da mutane masu rayuwa cikin talauci fiye da China da Masar idan aka hada su wuri guda.”

Ya ce, “Dole mu fuskanci matsalar da muke gani a yau, saboda kashi 35 zuwa 40 na ‘yan kasa ne kawai ke da aiki, idan aka kwatanta da mutum miliyan 120 da ya kamata a ce suna da aiki, mutum miliyan 40 kawai suka samu wannan dama.

“Muna da mutum miliyan 80 da ya kamata a ce suna da aiki a wannan kasa amma ba su da shi.

“Illar hakan shi ne, muna da kasa amma ba ta aiki. Najeriya a matsayin kasa ba ta aiki. Saboda idan muka yi batun mutum miliyan 80 marasa aikin yi, kashi 70 daga cikinsu matasa ne wadanda ba su da abun yi.

“Kasar ba ta yin komai, ba ta aiki. Abu daya da kasar ke yi shi ne rarrabawa. Kowa na neman abin da zai raba,” inji shi.

(NAN)