A duk lokacin da na dubi yadda al’amura suke tafiya a karkace, a dagule, a cabalbale, sai in rasa ta ina za mu fara magana kan yadda za a gyara Nijeriya.
Shin masu mulkin ne suke bukatar gyara ko mu talakawa? In masu mulkin ne su ne za su gyara kansu da kansu ko su wane ne za su gyara su?
Ga fahimtata, mutum bai cika gyara kansa da kansa ba, wannan ita ce falsafar rayuwa, kuma hakan ne ya sa Allah Yake aiko manzanni da annabawa domin su jagoranci irin wannan gyara.
Don haka kamar yadda masu mulki suke gyara wa talakawa zama idan muka karkace, muka fandare, muka lalace, su ma fa masu mulkin nan in suka karkace, suka fandare, suka lalace, tilas ne a samu wani yunkuri na talakawan wajen ganin an mayar da su kan hanya.
A irin wannan fasali ne ake samun juyin mulki ko juyin juya-hali.
Yanzu kuma sai aka samu hanya mafi sauki ta yin wannan gyara wato ta hanyar zabe da kada kuri’a.
Na san wani zai ce babu abin da talaka zai iya wajen sauya shugabanni ko gyara su ta hanyar zabe.
Ga masu irin wannan tunani suna cewa ai ba zaben talakwan ne ake ba su ba, a’a wani gungun mutane ne suka yanke hukunci a kan zaben su dora wanda suke so.
Eh haka ne, kuma a’a ba haka ba ne. A matsayina na talaka dan siyasa na ga abubuwa da yawa da suka sa na canja tunani game yadda al’amura suke tafiya a kasar nan.
Kuma na fahimci cewa gyaran nan fa ba na wani mutum guda ba ne. Babu shugaban da zai zo ya gyara Nijeriya shi kaɗai. To wane ne zai gyara ke nan?
Daga dan abin da na fahimta a gwargwamayar da muka yi a siyasa, na lura cewa gyaran nan fa wajibi ne ya faro tun daga kan mu talakawa a unguwanni da ƙauyuka da karkara da biranenmu.
Kuma gyaran nan ba a fagen siyasa da mulki ba ne kawai, a’a a kowane fage ne na rayuwa.
Wajibi ne mu koma kan kyawawan al’adu da dabi’unmu na kowa ya zama makiyayi a cikin al’umma.
Batun uba ko uwa ne kaɗai za su sa ido a kan ’ya’yan da suka haifa da muka mayar abin tinkaho a yau, shi ne abu na farko da ya fara ruguza tsarin zamantakewarmu, daga nan abubuwa suka ci gaba da lalacewa har hakan ya mamaye dukkan fannonin rayuwarmu.
Yau in matsala ta taso maimakon mu taru a tsakanin makwabta ko mutanen unguwa da kauyukanmu mu gyara, sai kowa ya kama gabansa yana jiran wani can daga nesa ya zo ya gyara mana.
Bari in dauki bangaren da na fi sani wato siyasa. Da yawan mutane sukan dauki matsalar kasa gaba daya su dora wa Shugaban Kasa ne.
Wasu kuma su dauki na jiha kacokan su dora wa Gwamna. Abin tambaya shin wadannan shugabanni biyu sun san komai da komai ne?
Shin za su zauna ne a kowane lungu da sako don ganin al’amura suna tafiya yadda ake so?
Misali idan aka samu sabani a jam’iyya ko kungiya a matakin unguwa me zai hana mutanen unguwar su warware matsalar a tsakaninsu?
Idan ta gagara ne kawai za a je ga matakin dagaci ko mazaba. Haka idan matsala ta faru a mazabar dagaci mu zauna mu sasanta ko mu gyara sai in abu ya gagara za mu je ga kasar hakimi, haka za mu rika bin lamarin har zuwa jiha.
In ya so a bar hedikwatar jam’iyya ko kungiya ta kasa da warware matsalolin da suka taso a jihohi. Amma haka muke a yanzu?
Matsalar unguwa tana iya tabarbarewar da wani lokacin sai an hada da hedikwatar jam’iyya ko kungiya ta kasa, kai wani lokaci ma har gaban shugaban kungiya na kasa ko dan takarar Shugaban Kasa ko ma Shugaban Kasar za a je.
Haka lamarin yake a abin da ya shafi zabar wakilan jama’a a siyasa ko a sauran harkokin rayuwa.
Sai ka ga tun daga kan malaman unguwa da limamai da masu sarauta da attajirai, babu wanda za a iya zuwa gabansa a sasanta ko a gyara wata matsala da ta taso, sai an tsallaka zuwa gaba, in kuma na rikici ne a je ga ’yan banga ko ’yan sanda, wadanda akasarinsu ko dai jahilai ne ko kuma ba kininku ba ne, sun fito ne daga wasu al’adun da ba irin naku ba.
Sannan idan muka tura wani ya wakilce mu a gwamnati, shin wakilci nagari muke nema daga gare shi, ko kuwa su muke ya debo ya ba mu?
Me zai hana duk wanda muka zaba ko aka nada mana mu nuna masa bukatun layi ko unguwa ko kauye ko birninmu?
Misali idan matsalar unguwa ta ruwan sha ne, ya zamo abu na farko da za mu mika mu tsaya mu ga an yi shi ne samar mana da ruwan.
Idan dam muke bukata a kauyenmu, nan ma mu yi tsaye hakan ya tabbata.
Masu buƙatar hanya su yi haka, masu bukatar takin zamani su yi haka, masu bukatar rijiyar burtsatse su yi haka, masu bukatar rijiyar kankare su yi haka.
Wallahi idan muka fara bin wadannan dabaru za mu gyara abubuwa da dama cikin kankanin lokaci.
Amma mu tsaya muna ta ɗora wa Shugaban Kasa ko Gwamna da sauran shugabanni laifin tabarbarewar al’amura hakan ba zai yi mana magani ba.
Tilas a samu yunƙuri na gaskiya daga talakawa. Kuma wannan yunkuri zai samu ne idan muka koma kan turbar magabatanmu na cire kwadayi da hadama da neman tara abin duniya.
Mu tsaya tsayin-daka, mu nuna shugabanci nagari muke so a tsakaninmu, tun daga layuka da unguwanni da garuruwanmu.
Mu tsaya mu fifita bukatun al’umma a kan bukatun daidaikunmu. Idan muka dauki wannan salo, duk wani mai mulki zai ji tsoronmu, ya rika yi mana abin da ya dace.
Mu tuna Allah ba zai saukar da mala’iku su zo su gyara mana abubuwan da suka lalace ba. Mu ’yan Nijeriya da muka bata ne za mu gyara.
Mun gwada jam’iyyu daban-daban da tsare-tsare iriiri tun daga samun mulkin kai a 1960, amma kullum cewa muke gara jiya da yau.
Ba tsarin ba ne kawai mai laifi, har da mu masu gudanar da shi. Don haka lokaci ya yi da za mu koma cikin hayyacinmu, mu dubi inda muka gaza mu faro gyara daga wurin.
Mu yi juyin juya-hali a dabi’u da halaye da ayyukanmu, ta yadda za mu iya turjiya, mu dake wajen jan daga da duk wani ko wasu miyagun shugabanni da ’yan korensu a ciki da wajen kasar nan domun mu iya gyara kasar nan.
Dalhatu Bakoji (Malam Bako APC), ya rubuto ne daga Unguwar Dim, Bauchi, Jihar Bauchi kuma za a iya samunsa ta: 07066385283