Dan wasan ƙwallon kafar nan dan asalin kasar Portugal da yanzu yake buga wa kungiyar Al-Nassr ta Saudiyya wasa, Cristiano Ronaldo, ya ce takun-saƙar da ya daɗe yana yi da Lionel Messi, ya zo karshe.
Cristiano, wanda ya taba lashe kambun Ballon d’Or har sau biyar ya kuma ce kwallayen da ya taba ci har sau 850 gagarumar nasara ce gare shi.
Sai dai ya ce dabin wanda suka dade suna fafatawa da dan wasan na kungiyar Inter Miami kuma ɗan asalin ƙasar Argentina tsaftatacce ne.
Ya kuma ce masoyansa ba sai sun tsani juna ba kafin su yi adawa a tsakaninsu.
Ronaldo ya dai bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a Oeiras da ke kusa da Lisbon, babban birnin Portugal a ranar Laraba gabanin fara gasar zakarun Turai.
Ya ce, “Adawar da ke tsakaninmu mai tsafta ce, ba na ganin ta a matsayin wani abu, saboda ta kare. Ma i tsafta ce, kuma masu kallo sun ji dadin ta.
“Duk wanda yake son Ronaldo da sai ya ki Messi ba, haka su ma masoyansa ba sai sun ki ni ba, saboda kowa gwani ne. Mun yi iya bakin kokarinmu. Kuma za mu ci gaba da yi. Ana girmama mu a duk fadin duniya. Wanna kuma shi ne Abu mafi muhimmanci,” in ji Ronaldo.