✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taki na taka talakawa manoma

Manoma a sassan kasar nan sun koka kan yadda kamfanoni da dillalan taki da jami’an gwamnati suka jawo karancin takin Buhari da aka yi alkawarin…

Manoma a sassan kasar nan sun koka kan yadda kamfanoni da dillalan taki da jami’an gwamnati suka jawo karancin takin Buhari da aka yi alkawarin sayar wa manoma a kan Naira 5,500 kowane buhu a bana.

Wani manomi a garin Saminaka da ke Jihar Kaduna Alhaji Bello Aminu Saminaka ya bayyana wa Aminiya cewa, kamfanonin da aka bai wa kwangilar sarrafa takin Buhari da dillalan takin ne suka kawo karancinsa. 

Ya ce ya yi amfani da wannan taki kimanin buhu 600 kuma takin ya yi kyau a gonakinsa. Kuma ya ce ya sayi takin ne da wuri don haka bai shiga matsalar tsadar takin ba. 

Alhaji Bello Saminaka ya ce yanzu ’yan kasuwa sun tayar da farashin takin a yankin Saminaka zuwa Naira 6,500 maimakon Naira 5,500 da aka ce a sayar. 

 Alhaji Bello Saminaka ya ce abubuwan da suka tayar da farashin takin su ne dillalan takin da kamfanonin da aka bai wa kwangilar sarrafa takin inda suka hada baki suka kawo matsala. 

Ya ce sakamakon hadin baki da suka yi sai kamfanonin da suke sarrafa takin suka rage yawan takin da suke sarrafawa a daidai wannan lokaci da manoma suke bukatar takin, don haka ya yi karanci. 

“Idan dillali ya biya kudi sai ya yi kwana da kwanaki ba a fitar masa da takin ba. Su kuma ma’aikatan gwamnati da suke aiki raba taki saboda sun ga ana bukatarsa sai suka sanya Naira dubu 60 ga kowace tirelar taki,” inji shi. 

Ya ce hanyar magance matsalar ita ce gwamnati ta sanya ido a kan kamfanonin da aka bai wa aikin sarrafa takin. A tabbatar suna yin taki sosai, masu raba takin kuma su tsaya su yi tsakani da Allah su rika raba wa dillalai takin kamar yadda ya kamata. 

Ya ce ya kamata gwamnati ta tabbatar cewa  ba ta kashe kudinta a banza ba, da niyar tallafa wa talakawa manoma, amma wadansu marasa kishin kasa suna yi mata zagon kasa. 

Shi kuwa Ahmed Abdullahi da ke Unguwar Bawa a karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna cewa ya yi ya sayi takin Buhari a kan Naira 7,000, maimakon Naira 5,500 da gwamnati ta ce a sayar. 

Alhaji Ahmed Abdullahi ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya, inda ya ce Gwamnatin Tarayya ta zo da takin don tallafa wa manoman kasar nan a kan Naira 5,500, kuma manoma sun fara jin dadin takin, domin ya yi musu amfani. Saboda manoman da suka yi amfani da takin a gonakinsu sun ga kyansa domin wata gonar ma zubin taki daya za a yi mata. 

“Da farko na sayi buhu 50 na takin na zuba a gonakina kuma sun yi kyau sosai, amma da na koma sayen takin sai aka ce mini ya tashi daga Naira 5,500 zuwa Naira 7,000, na buga lambar wayar da ke buhun takin domin fada musu sai na ji ba ta tafiya. Saboda na matsu domin na gwada takin na ga ingancinsa, dole haka na sayi takin a kan Naira 7,000 kowane buhu,” inji shi.  Ya ce ’yan kasuwa ne suka kawo matsalar takin, domin su ne suka hada baki da kamfanonin da suke yin takin. Sai ya yi kira ga gwamnati ta sanya ido kan takin don ganin ba a sake samun matsala ba. 

Malam Alhassan Sale Galadanci, wani fitaccen manomi da ke kauyen Galadanci a karamar Hukumar Kiyawa, ya ce manoma a yankin da ya fito suna fuskantar matsala kan yadda ake sayar da takin zamanin a bana. Ya ce duk da ana samun takin a farashin Gwamnatin Tarayya na Naira 5,500 a wasu wurare, amma ba kamar shekarun baya ba, inda ake ba manoma taki babu wata wahala ta hanyar tura musu ta waya. Ya ce amma yanzu ma’aikatan gwamnati da masu kudi da manyan ’yan kasuwa ne suke saye takin ba ya isa hannun kananan manoma. Ya ce a dakunan ajiye taki da gwamnati ta tanada taki na nan makare sai dai karamin manomi ba zai iya samun takin kai-tsaye ba, sai ya bi ta hannun ma’aikatan gwamnati. 

Malam Alhassan Galadanci ya ce a baya yana samun buhun taki 20 zuwa 30, amma bana da kyar ya samu buhu hudu saboda ba ya da kudi. Ya ce akwai alamun manoma da dama za su fadi a daminar bana domin da dama ba su samu takin ba.

Shi kuwa Malam Abdullahi Muhammed Rahama, mazaunin kauyen Rahama a karamar Hukumar Dutse a Jihar Jigawa cewa ya yi ana sayar da takin ne a kan farashi uku. Akwai na Naira, 5,500 da na Naira 7,500 da kuma na Naira 8,500 kowane buhu kuma manoma ba sa samunsa a farashin gwamnati.

Malam Abdullahi ya ce manoma da yawa za su yi asara saboda takin ya fi karfinsu ga kuma talaucin da jama’a ke fama da shi. Ya ce yana amfani da taki buhu 30 a gonakinsa hudu, amma a bana bai zuba koda buhu 5 ba. Ya ce da dama cikin manoman kauyansu sun koma amfani da takin kashin shanu da toka.

Ya ce akwai bukatar Gwamnatin Tarayya ta rage farashin takin daga Naira 5,500 zuwa Naira 2,500, saboda takin shi ne karfin noma kuma yana neman ya fi karfin talaka. Ya ce a duk shekara yana noma akalla buhu 150 na amfanin gona, amma bana ba ya jin zai iya noma buhu 40 saboda rashin takin da kuma rashin kudin sayensa.

Daga Jihar Kano, wakilinmu ya ruwaito cewa shirin Gwamnatin Tarayya na wadata manoma da takin zamani an rarraba shi zuwa manyan rumbunan ajiye taki da ke kananan hukumomin jihar kuma a farashin Naira 5,500 kowane buhu. Manoma da dama da Aminiya ta zanta da su sun nuna gamsuwa da shirin gwamnatin Shugaba Buhari na wadata kasa da abinci duk da cewa ana samun batagari suna yin zagon kasa ga shirin sayar da takin.

A garin Waddau da ke karamar Hukumar Dawakin Tofa, wani manomi mai suna Alhaji Idris Adamu Dungurawa ya ce abin da Gwamnatin Tarayya ta yi wa manoma a wannan damina ya yi kyau, musamman yadda aka samar da taki wadatacce kuma aka kayyade farashi. Ya ce manoma sun amfani shirin samar da takin, inda ya ce “Idan aka ci gaba da shirin kasar nan za ta wadata da abinci kuma manoma za su rubanya noman da suke yi.”

A tsokacin Alhaji Musa Sani, wani manomi daga karamar Hukumar Ungogo ya ce shirin da aka yi na hadin gwiwa a tsakanin jihohi da Gwamnatin Tarayya zai zamo alheri ga manoman kasar nan musamman ganin cewa gwamnatin Shugaba Buhari tana daukar matakan bunkasa noma da kiwo, kuma manoman an samar musu hanyar wadata su da taki wanda shi ne babbar matsalarsu a duk shekara. Sai ya roki Gwamnatin Tarayya ta kara hada hannu da kamfanonin takin zamani domin ganin ana samun taki a ko’ina domin aikin rani da damina.

Binciken da wakilinmu ya gano cewa akwai batagari da suke gurbata takin da Gwamnatin Tarayya ta kawo suna yin jabunsa amma hukumomin tsaro sun dukufa wajen zakulo ire-irensu domin hukunta su.

Daga Zariya, wani manomi a kauyen Karau-Karau da ke karamar Hukumar Zariya, Malam Isa Khalid ya ce ya samu takin buhu hudu a karamar hukumar kan Naira 6,175 kowane buhu duk da ya cika dukan ka’idojin da aka nema na ya ba da takardar shaidar zama dan kasa ko katin zabe tare da cike wata takarda. “Saura a kasuwa na saya, shi ma na gwamnati ne, amma a kan Naira 6,500.

Wani manomi mai suna Malam Ibrahim Yusuf wanda ke da gona a Unguwar Majeru ya ce, bai samu takin gwamnati ba, amma ya saye shi a kasuwa kan Naira 6,600 kowane buhu. Ya ce duk tallafin da aka ce za a ba manoma bai samu ba kuma yanzu haka ya sayi taki buhu 16.

Wani mai sayar da taki da ya ki ya ambaci sunansa ko a dauki hotonsa ya shaida wa Aminiya cewa, za su iya sayo takin a hannun gwamnati su sayar da shi a kan farashin da ta tsara, amma duk da wannan yarjejeniyar da aka yi da su da jami’an gwamnati abin ya gagara domin su kansu suna samun takin daga hannunsu a kan Naira 5,800 kuma su biya kudin lodi da mota da sauransu. “To idan ka yi lifsafi sai ka ga kudin ya yi sama don haka wani ke sayarwa Naira 6,500, wani Naira 6,600,” inji shi.

Wani manomi a Jihar Gombe, Malam Ali Garba, ya tabbar wa Aminiya cewa ba su ga takin na damina ba, takin da suka samu tun na noman rani ne. Ya ce wanda suka samu na noman ranin yana da gauraye wanda manoma da dama suka koka saboda rashin kyansa. Ya ce amma da ’yan jarida suka fallasa hakan sai aka janye shi aka kawo mai kyau.

Manomin ya ce Gwamnatin Tarayya ta sa farashin takin a kan Naira 5,500 amma yanzu a kasuwa ya fi haka saboda babu mai sa ido a kan farashin. Malam Ali Garba, ya ce takin yana samuwa ne a makare a wasu lokuta wanda bai cika amfanar kananan manoma ba.

Shi kuwa Ibrahim Muhammad, cewa ya yi a daminar bana ba su ga takin Gwamnatin Tarayya ba, kuma wata majiya ta ce ba za a sayo takin ba saboda rashin kudi. Ibrahim Muhammad, ya ce sai dai suna fata Allah Ya kawo wa manoman dauki domin akwai matsala a yanayin kawo takin har ya isa ga manoma.

Sai ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya cewa idan ta kawo takin ta sanya ido saboda wadansu ’yan kasuwa suna gurbata shi kuma ana kara farashinsa.

Daga Hussaini Isah, Jos

Aminiya: A halin da ake ciki takin da Gwamnatin Tarayya ta kawo don sayarwa ga manoman kasar nan, ana ta koke-koken cewa farashin takin ya tashi kuma ana gurbata shi a wasu wurare, yaya kake kallon lamarin?

Farfesa Dadari: Takin Najeriya da gwamnatin Buhari ta kawo daga kasar Marako, mun san cewa mai inganci da nagarta ne, wanda babu algushu a cikinsa. Da aka kawo takin aka bai wa dillalan takin da za su rika sarrafawa suna sayar wa  manoman Najeriya, sai aka sanya musu ribar Naira 500 a kowane buhu aka ce su sayar da takin Naira 5,500. Ni kaina na sayi taki kan wannan farashi na Naira 5,500. Amma yanzu abin ba haka yake ba, farashin buhun takin ya kai Naira 6,500 zuwa sama. 

 Ana tsamanin dillalan ne suka bata harkar takin, don haka gwamnati ta cire dillalan  domin ba su da amfani. A je a samo mutane na kwarai masu imani da tsoron Allah  a mika musu wannan harka. Domin dama wadannan dillalai ’yan baranda ne. Hatta lambar wayar da aka sanya a jikin buhun takin, aka ce a rika kira ana bayyana abin da ake yi, sun toshe layin lambar, ko an kira ba ta shiga. 

 Babu shakka akwai jan aiki a gaban ’yan Najeriya, don haka ya zama wajibi ga  kowa ya taimaka wajen kawo sauyi kan wannan hali da muka shiga. 

Mu dai mun yarda gwamnatin Buhari ta zo da manufa mai kyau kan wannan taki, domin takin an saya an gwada kuma an ga ingancinsa. Amma da tafiya ta yi nisa sai dillalan suka hada baki suka lalata harkar. Don haka gwamnati ta cire su, ta kawo mutane na kwarai.

  Aminiya: A kwanakin baya Ministan Gona ya kaddamar da shirin fitar da doya daga kasar nan zuwa kasashen waje yaya kake ganin shirin?

Farfesa Dadari: Wani lokaci Ministan Gona yana soki-burutsu kan aikin noma a Najeriya. Yana fadar abin da bai riga ya tantance ba, kan aikin noman. Kayayyakin amfanin gona da ake fitar da su daga kasar nan a da, yanzu ana fitar da su? A da ana fitar da auduga da gyada daga kasar nan, yanzu ba a fitar da wadannan kayayyaki saboda rashin tallafi.

 Yanzu  Minista ya baro maganar doya. Yanzu doyar da ake ci a kasar nan, har ta ishi ’yan Najeriya? Doya  nawa ake nomawa a Najeriya yanzu? Yanzu tsohuwar doya akwai ta Naira 1,500 guda daya. Ana fitar da abinci ne idan an noma shi ya wadata a kasa. To ka ce a fitar da doya zuwa waje alhalin doyar nan tafi karfin talakan Najeriya. Ba mu ce kada a fitar da doya daga kasar nan ba, amma kafin a fitar da ita, a tabbatar ta wadata a kasar. Kuma ba maganar doya ce kadai za a rika fitarwa daga Najeriya ba, a dubi kayayyakin da manoman Najeriya suke nomawa a inganta su, a samu wanda za a ajiye a cikin kasa, kuma a samu wanda za a fitar zuwa waje. 

Aminiya: Duk da noman nan da ake cewa an yi a daminar bana, a ’yan kwanakin nan ana rade-radin cewa an shigo da masara daga kasar waje, me za ka ce kan wannan magana?

Farfesa Dadari: Shigo da masara da ake cewa an yi zuwa kasar nan, saboda wanda ya fito da tsarin bunkasa noma a Najeriya ne baya nan. Don haka komai zai iya faruwa za a damu Mukaddashin Shugaban kasa cewa ya shigo da abinci. Kuma masu cewa ana yunwa a Najeriya, don haka a shigo da abinci ’yan adawa ne. Su masarar ma ba sa cin ta suna da abincin da suka riga suka tara wanda suka sayo daga waje wanda zai kai su shekara da shekaru. Idan har an shigo da masara kasar nan, to gwamnati ta yi kuskure. Gwamnati ta daina sauraron masu kukan cewa cewa akwai yunwa a Najeriya. Domin ’yan adawa ne masu irin wannan koke-koken karya. 

 Aminiya: Ganin yadda aka rungumi noma a daminar bana wadanne matakai kake gani ya kamata gwamnati ta dauka don kare amfanin gona da jama’a suka noma?

Farfesa Dadari: Idan Allah Ya kawo wannan amfanin gona kuma aka same shi a yalwace, babban abin da gwamnati za ta yi, tunda tana da niyar alheri ga al’ummar Najeriya shi ne ta saye rarar amfanin gonan kan farashin da manoma ba za su cutu ba. 

Aminiya: Yaya kake ganin shirin gwamnati na A Daidaita Sahu?

Farfesa Dadari: Gwamnatocin da suka gabata sun riga sun lalata abubuwa a kasar nan, sun yi sama-da-fadi. Don haka idan har za a  gyara wannan barna dole ne kowa sai ya ji jiki.  Bana Allah Ya ba mu ruwa wanda ya yi daidai da noma a kasar nan, domin a bana ana yin ruwa da tsabta da tsari, yadda zai taimaka wa amfanin gona ya yi kyau. Kuma  sakamakon darajar da amfanin gona ya yi a Najeriya, yanzu kowa ya rungumi noma. 

 Don haka babu shakka gwamnatin Buhari ta samu nasarori masu yawa, a shirinta na A Daidaita Sahu. Nasara ta farko da gwamnatin ta samu shi ne canja alkiblar siyasar Najeriya. Yanzu ’yan Najeriya za su zabi mutum ne ba jam’iyya ba. Haka gwamnatin ta samu nasarar tarwatsa ’yan Boko Haram. Yanzu sai dai ka ji suna kai harin sunkuru. Bayan haka a wannan gwamnati ana kama barayin gwamnati kuma an hana satar kayan gwamnati. Sannan wannan gwamnati ta samu narasa kan bunkasa harkokin noma.