Tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya musanta rahoton da ake yadawa cewae EFCC ta gayyace shi.
Obi ya ce har yanzu bai samu sammaci daga EFCC ko wata hukumar yaki da rashawa ba.
- Budurwa da bindige saurayi don ya ki sumbatar ta
- Za a binciki dan sandan da ya ‘kada kuri’a’ a zaben APC na Kano
Sai dai ya bayyana cewa kamar yadda kowa ya gani a intanet cewar hukumar na neman shi, shi ma haka ya gani.
Obi, cikin wata sanarwa da hadimarsa kan kafafen watsa labarai, Valentine Obienyem, ta fitar ta musanta labarin da ke yawo a intanet.
Ta ce, “Obi har yanzu bai samu shaidar takardar sammaci daga EFCC ba, kamar yadda ya karanta a intanet.
“Daga abin da ake yadawa shi ne an tura takardar sammacin zuwa ofishin da ya bari ne, kuma yanzu ba ya ofishin kuma babu wata takarda da aka turo masa.”
Kazalika, sanarwar ta bayyana Obi a matsayin dan kasa na gari mai bin doka, kuma zai martaba duk wata gayyata da za a yi masa daga kowace hukuma.