✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Takarar Gwamnan Kaduna: Kotu ta kori karar Sani Sha’aban

Alkalin kotu, Mai Shari'a Mohammed Garba Umar, ya bayyana cewa kotun ba ta da hurumin sauraron karar.

Babbar Kotun Tarayya ta yi watsi da karar Muhammad Sani Sha’aban da ke kalubalantar zaman Sanata Uba Sani dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna a Jam’iyyar APC.

A ranar Juma’a kotun da ke zamanta a Kaduna ta sanar da hakan bayan karar da Muhammad Sani Sha’aban a shigar yana kalubalantar zaman Uba Sani dan takarar jam’iyyar na kujerar.

Da yake sanar da hakan, alkalin kotu, Mai Shari’a Mohammed Garba Umar, ya bayyana cewa kotun ba ta da hurumin sauraron karar.

Kotun za ta yanke hukuncin ne bayan ta dage zamanta na ranar Alhamis zuwa ranar Juma’a.

A watan Mayun bana ne Jam’iyyar APC ta sanar da Sanata Uba Sani a matsayin dan takararta na kujerar Gwamnan Jihar Kaduna.

Madugun zaben fitar da gwanin, Anachuna Henry, ya sanar a lokacin cewa dalaget 1,275 ne suka yi rajistar zaben, inda ya ce daga cikinsu an tantance guda 1,245, sannan guda 1,235 suka kada kuri’a,  wadanda daga ciki kuri’a 39 suka lalace.

A cewarsa, Sanata Uba Sani ya samu kuri’a 1,149, sai Bashir Abubakar ya zo na biyu da kuri’a 37, yayin da Muhammad Sani Sha’aban ya samu kuri’a 10.

Yadda rikicin ya samo asali

Tun kafin zaben na fid-da-gwani, an yi ta kai-komo tsakanin ’yan takara, amma a lokacin gwamnati ta fi karkata kan Sanata Uba Sani da Muhammad Sani Dattijo.

Wannan ya sa APC a Jihar Kaduna ta shiga rudani, inda ta nemi ta zage biyu: magoya bayan Dattijo da magoya bayan Uba Sani.

An sha tambayar Gwamna El-Rufai a kan magajinsa, amma ya ki cewa uffan.

Sai dai a wani zama da aka yi a ranar 5 ga Mayun bana, Gwamna El-Rufai tare da sauran na kusa da shi sun amince da Uba Sani a matsayin dan takararsu.

Zaman ya kuma aka amince da Dattijo ya maye gurbin Sanata Uba Sani a matsayin dan takarar Sanatan Kaduna ta Tsakiya, ita kuma Mataimakiyar Gwamna, Hadiza Balarabe Sabuwa, ta ci gaba da kasancewa a matsayinta.

Wannan lamari ya haifar da kwanciyar hankali da murna a tsakanin magoya bayan APC a jihar, ganin an samu maslaha.

Sai dai a daidai a lokacin da ake murna, ashe an yi kitso da kwarkwata, inda ba da jimawa ba Muhammad Sani Sha’aban ya fito ya ce shi bai san da wannan zancen ba, domin ba a yi shawara da shi ba, sannan ya nanata cewa yana kan bakarsa ta takara.

Hakan ya sa aka koma gidan jiya, inda magoya bayan jam’iyyar suka sake rabewa biyu — magoya bayan hukuncin gidan gwamnati da magoya bayan Sha’aban.

A haka aka je har aka fara shirye-shiryen zaben fid-da-gwani, inda kafin zaben, Sani Sha’aban ya ce bai amince da tsarin ba, kasancewar bai san daliget din da za su yi zaben ba.

Bayan sanar da sakamakon zaben fid-da-gwanin, Sha’aban ya kalubalanci zaben, inda ya ce bai amince ba kuma a cewarsa ya yi duk mai yiwuwa wajen ankarar da uwar jam’iyyar game da bukatar a yi abin da ya dace, amma aka ji.

Wannan ne ya sa dan takarar ta garzaya kotu, inda ya kalubalanci tsarin fitar da daliget din da zaben da tsarin zaben.

‘Sulhun’ Uba Sani da Sha’aban

A ranar 1 ga Yuni ne Sanata Uba Sani ya kai ziyara gidan Muhammad Sani Sha’aban, inda suka tattauna a kan batun siyasa, musamman jami’iyyarsu ta APC.

Jim kadan bayan fitowa daga tattaunawar ce kafafen yada labarai suka yada cewa an samu maslaha, kuma Sha’aban ya janye kararsa.

Sai dai ana cikin murnar hakan ne Alhaji Sani Sha’aban ya fito ya karyata lamarin, inda ya ce yana nan a kan bakarsa na a tabbatar masa da hakkinsa a kotu.

%d bloggers like this: