Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya fito fili ya bayyana niyyarsa ta sake tsayawa takara a shekarar 2019 ne saboda ya rufe bakin tsanya, “domin mutane suna ta maganganu a kan cewa zan sake tsayawa ko b azan tsaya ba a zabe mai zuwa.’’
Kakakin shugaban Femi Adesina ne ya ruwaito Shugaba Buhari yana fadin haka a lokacin da karbi bakuncin shugaban cocin Angalika ta duniya Akbishop na Canterbury Justin Welby a Landan.
Shugaban ya yi nuni da cewa, “na bayyana niyyar sake tsayawa takarar kafin in bar kasar ne saboda surutai ya yi yawa, shi ya sanya na ce bari in raba gardama.’’
“Akwai abubuwa da dama a gabanmu da suka kamata mu mayar da hankali a kansu, kamar tsaro da yaki da cin hanci da rashawa da tattalin arziki da noma, da sauransu da yawa. Don haka bai kamata mu bari harkar siyasa ta dauke mana hankali ba. Mafi yawan ’yan Najeriya sun gamsu da abubuwan da muke yi, shi ya sanya zan sake tsayawa takara,’’ inji Shugaba Buhari.
Wakilanmu sun ji ra’ayoyin jama’a ciki har da ’yan siyasa da jam’iyyun adawa kan wannan mataki da Shugaban kasar ya dauka:
‘Abin da ya sa Buhari ba zai so ya bar gwamnati yanzu ba’
Dokta Suleiman Amu Suleiman, masanin siyasa a Jami’ar East Anglia da ke Birtaniya, ya shaida wa BBC cewa bai yi mamakin sanarwar ba. Kuma ya ce tashin da farashin mai ke yi a baya-bayan nan, ya nuna cewa kudi za su ci gaba da shigowa ga gwamnati domin samun damar yin ayyuka da cika alkawuran da Shugaban ya dauka saboda lokacin da ya hau gwamnati ya same ta a cikin talauci. Don haka koma wane ne ba zai so ya bar gwamnati a yanzu ba.
Na biyu, shugaban ya samu lafiya sosai fiye da bara, lokacin da hankalin mutane da dama ya tashi saboda tabarbarewar lafiyarsa. Na uku, “Ina ganin shi kansa Shugaba Buhari yana ji a zuciyarsa cewa bai taka rawar a-zo-a-gani ba, don haka yana so a sake ba shi dama domin ya gyara.”
Ya ce nasarar da Buhari ya samu ba ta kai wacce ya samu a lokacin da ya shugabanci Hukumar Kula da Rarar Kudin Mai ba. “Idan har ya wuce to zai samu damar yin ayyuka ba tare da wata matsala ta siyasa irin wanda ya hadu da ita a farkon zangon mulkinsa ba,” inji shi.
Sai dai “Ba zan iya cewa zai kai labari ba tukunna domin wannan zai dogara ne kan irin shirin da ’yan adawa suka yi da yadda ra’ayin ’yan Najeriya zai karkata kafin lokacin,” inji shi.
‘Ya amsa kiran jamaá ne’
Shugabar Mata ta Jam’iyyar APC a Jihar Katsina Hajiya Safiya Daura ta ce, sun yi murna kwarai lokacin da suka ji cewa Shugaba Buhari ya bayyana zai sake tsayawa takara a karo na biyu. “Sanin jama’a ne cewa,’yan kasa ne da kansu suka yi ta neman ya sake tsayawa takara kamar yadda suka neme shi a zabubbukan baya har ya hau kujerar shugabancin kasar nan. Alhamdulillahi da ya ji rokon jama’a ya karba musu dama saboda su yake yin duk abin da yake yi,” inji ta.
Shugabar ta ce, “Masu ganin yawan shekarun da Shugaba Buhari yake da su da rashin lafiyarsa, ta ce, shin Obasanjo bai fi Buhari shekaru ba? Amma ya mulki kasar nan na shekara takwas har ya nemi yin wa’adi na uku ’yan kasa suka ki yarda. Kuma duk wanda ya ga Shugaban yanzu ya san yana cikin koshin lafiya da kuzari. Saboda haka, fatanmu Allah Ya kai mu lokacin kuma Ya ba mu nasara.”
Hajiya Safiya ta yi kira ga ’yan kasa su yi watsi da farafagandar makiya ci gaban kasar nan da a kowane lokaci kansu kawai suka sani. “Mu fito a zaben 2019 mu zabi Shugaba Buhari wanda zai kai kasar nan ga kyakkyawar makoma,” inji ta.
Alhaji Jamilu Shu’aibu na kungiyar NURTW cewa ya yi, “Mun dade muna jiran jin wannan daga bakinsa, domin muna da yakinin cewa Shugaba Buhari Allah Ya kawo mana shi ne domin ya ceci kasar nan daga cikin halin da muka samu kanmu. Duk wanda ka ji ya ce ba ya son Shugaba Buhari, to ka tabbatar barawo ne, maciyin amana da ba ya son ganin kowa ya ci gaba. Mu ajiye batun tsaro daga cikin ci gaban da muka samu, dubi irin yadda jama’a yanzu suke kokarin neman halalinsa sabanin baya da ake taho halal taho haram. Yanzu mu ne ke fitar da kayan amfanin gona zuwa kasashen waje maimakon shigo mana da su. Akwai abubuwa da dama da duk mai son ci gaban kasar ya san cewa an samu nasararsu.”
Shi kuwa Alhaji Sani Ado Kwa, Shugaban kungiyar Masu Walda ta Jihar Katsina cewa ya yi bukatarsu ce Allah Ya nufa ta biya. “A matsayinmu na masu sana’ar hannu, mun zabo wakillai daga sauran masu wasu sana’o’i inda muka kafa wani kwamiti wanda ya yi tarurruka da dama domin yin kira ga Shugaba Buhari ya sake fitowa takara a zaben 2019. Muna da kyakkyawan zato cikin ikon Allah kafin ya kammala shekara takwas sai dan Najeriya ya san matsayinsa na dan kasa mai hakki da ’yanci, maimakon yadda wadansu ’yan tsiraru suka mamaye komai suka mayar da shi nasu suka bar mu tamkar bayi.”
Buharin shekarar 2015 daban yake da Buharin 2019 – PDP a Kaduna
Da yake mayar da martani kan bayyana niyyar Shugaba Buhari ta sake tsayawa takara a zaben na badi Sakataren Jam’iyyar PDP reshen Jihar Kaduna Ibrahim Wosono cewa ya yi, batun tsake takarar Shugaba Muhammadu Buhari ya yi daidai saboda dama bukatarsu su kayar da shiý, saboda Buharin shekarar 2015 daban yake da Buharin 2019. “Buharin 2015 shi ne mutumin da mutane ke ganin idan sun zabe shi za su samu saukin rayuwa, za su samu aikin za su samu tsaro, za su wadata, abinci zai sauka, za a yi ayyuka a kasa. Idan sun zabe shi komai na rayuwa za a samu sauki. Amma Buharin 2019 shi ne Buharin da mutane suka cire wannan tunani a kansa. Domin an zabe shi amma ya kasa domin babu abin da za ka nuna a Arewa ko a Kaduna da za ka ce wannan aiki ne da Shugaban kasa Buhari ya yi,” inji shi.
Ya kara da cewa idan ka je Kano ko Sakkwato da duk jihohin Arewa babu abin da za ka nuna ka ce aiki ne na Shugaba Buhari. “Man fetur Shugaba Buhari ya same shi ne a Naira 92 amma ya mayar da Naira 145. Wannan kari ne da ba a taba yin irinsa ba a kasar nan. Buharin shi ne wanda ya kamata a ce yana tausayin talaka kuma ya fada lokacin da yake takara cewa idan aka sayar da man fetur a Naira 50 ma an cuci talaka. Yanzu ya kamata talaka ya gane cewa Buharin nan ba shi yake so ba. Sannan a maganar abinci nawa Buhari ya samu buhun shinkafa bai fi Naira dubu takwas ba amma yanzu nawa ake sayar da ita? Ta kai kusan Naira dubu 20, saukinta Naira dubu 17, inji shi.
Ya ce sai dai ya taka rawa a bangaren tsaro saboda an daina tashin bama-bamai a jihohi amma ba a daina hallaka mutane ba, musamman a Arewa maso Gabas inda har yanzu ake kai hare-hare, amma an samu sauki a Kano zuwa Kaduna. “Idan ka dubi wadannan abubuwa sai ka ga wani Buharin ake dokin tsayawarsa takara abin da ma wadansu ke tababa ko shi ke mulkin ko ba shi ba ne. Mu a wurinmu ‘yan PDP babu abin da muke ji domin babu wani abu daya da za a nuna a ce na Buhari ne a Arewa. Idan ka tuna a matsayinsa na Shugaba dan Arewa ana shigo da abinci ta kan iyakokin kasar nan ‘yan Kudu sun yi hikima saboda inganta tattalin arzikin yankinsu suka ce kawai a shigo da shi ta ruwa don a samu kudaden shiga. Kudaden shigar nan ba mu ga amfaninsu ba. Basussuka ake ci a kasar nan wadanda ba a taba cin irinsu ba. ýIdan ka dubi maganar da Tunde Bakare ya yi cewa a shekara 16 da PDP ta yi a mulkin kasar nan bashin da ta ci kawai Naira tiriliyan shida ne amma Buhari a shekara uku ya ci kusan Naira tiriliyan 11. Idan kuma ana maganar cewa tattalin arziki ya inganta a lokacin mulkin Buhari a asusu babu kudi ta ina ne ya inganta? Yanzu haka a gidana idan ka ga irin mutanen da ke zuwa neman taimako abin zai ba ka mamaki,” inji Sakataren na PDP.
Masu son kai ne kawai ke adawa da tazarcen Buhari – Umaru Dembo
Babban Daraktan Cibiyar Goyon Bayan Buhari (Buhari Support Group Centre – BSGC), Alhaji Umaru Dembo ya ce, cibiyar ta rika karfafa wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari gwiwa domin ya fito takara tun a shekarar 2013, kuma tana jaddada goyon bayanta kan kudurinsa na sake tsayawa takarar Shugaban kasa a zaben shekarar 2019. “Mu muna goyon bayan nuna aniyarsa ta zai yi takara a zaben 2019 kuma hakan ya dace don ya ci gaba da ayyukan alheran da ya faro na gina kasa,” Dembo ya shaida wa Aminiya.
dan siyasar ya kara da cewa, “Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ayyukan gina kasa da suka hada da dakile ayyukan ta’adda na kungiyar Boko Haram wadda ba ta raga wa masallatai da mujami’u da kasuwanni da tashoshin mota da makarantu kuma ba ta kyale da mai hali da talaka ba a duk fadin kasar nan. Kuma Shugaban ya dakile hanyoyin da satar kudin gwamnati, ya kirkiro asusun ajiya na bai-daya (TSA), ya kara wa kasa kafafen samun kudin shiga da ake yin manyan ayyuka kamar hanyoyi da ciyar da ‘yan makaranta da ba jihohi kudi su biya albashi, da sauransu.”
Alhaji Umaru Dembo ya ce wadanda ba su son Shugaba Buhari ya ci gaba da mulki su ne wadanda ba su son kasa sai dai kansu wadanda suka yi shekara 16 suna lalata kasa kuma sun rasa wanda za su fito da shi don ya kalubalanci Shugaba Buhari a zaben badi.
‘Kwata-kwata bai kamata ya sake tsayawa takara ba’
Justice Nafi’u Ya’u Jos, dan kasuwa, dan kwangila kuma dan siyasa a Jihar Filato ya ce ayyana sake tsayawa takara da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ba abin mamaki ne, amma bai kamata ya sake tsayawa takara ba.
“Kwata-kwata bai kamata ya sake tsayawa takara ba, duk da cewa yana da ‘yancin hakan, amma a zahirin gaskiya bai cika alkawuran da ya dauka ba, ya shugabancin kasar nan a yanzu tsawon shekara uku, amma abubuwa ba su daidaita ba, masu iya magana sun ce, an ce da kare ana biki a gidanku sai ya ce to ya gani a kasa, amma a gaskiya ‘yan Najeriya ba su ga komai ba,” inji shi.
Ya ce, ko da Buhari zai sake lashe zaben da za a yi a shekara ta 2019, to zai fuskanci babban kalubale. “Ka bar maganar shekara da lafiya, domin masu lafiya nawa suka mutu shi kuma yana nan da ransa, sannan matasa nawa ne suka mutu shi yana nan da ransa, amma dai ya gaza ne kawai,” inji shi.
Ya ce, a yanzu haka a wurin da yake babu wutar lantarki fiye da kwana 10, kuma babu abin da aka yi, Ministan Wutar Lantarki ya gaza a nan, kuma Shugaba Buhari ne ya nada shi, idan ya gaza to Buhari ma ya gaza. Ya ce, “A yadda nake gani Buhari zai sha wahala, ka ga talakawa sun shiga cikin mawuyacin hali, abinci ya yi tsada, an kara kudin man fetur da kudin makaranta, komai farashinsa ya tashi, don haka talaka ya dandana kudarsa, don haka ko ka ce ya zabi Buhari zai tsaya ya yi tunani, ba kamar a zabubbukan baya da kowa yake ganin Buhari a matsayin mai ceto ba.
‘Har yanzu ba dan takara da za a hada shi da Buhari a nagarta’
Zaharaddeen Muhammad (Turai), dan siyasa, dan kasuwa kuma Shugaban kungiyar Matasa da ke Fafutikar Tabbatar da Dimokuradiyya a Jihar Falato, ya ce shekaru da batun rashin lafiya ba za su hana Buhari neman mulki ba.
Ya ce, rashin lafiya daga Allah ne, haka kuma shekarun Buhari za su kara masa fikira wajen gudanar da mulkinsa cikin adalci.
“Ga masu cewa Buhari ya gaza ba su yi adalci ba, siyasa suka sanya a cikin batun, duk da rashin lafiyar Buhari, amma ya tsayar da batun satar dukiyar al’umma a kasar nan, ya bunkasa harkar noma, inda mutane da yawa suka koma noma hade da daina zaman kashe wando, ga batun ciyar da daliban makarantar firamare, inda hakan ya sanya yara ke kwadayin zuwa makaranta. Ga batun shirin N-Power inda ake biyan matasa Naira dubu 30 duk wata, wadansu an tallafa musu sun fara sana’o’i, ya dauki ’yan sanda dubu 10 aiki, an samu nasara a yaki da Boko Haram, an dawo da ’yan matan Dapchi da wadansu na Chibok, wannan kadai zai ba Buhari nasara yayin zaben 2019,” inji shi.
Muhammad ya ce a zahirin gaskiya yanzu babu wani dan takara da za a hada shi da Buhari wajen nagarta, domin Atiku da Kwankwaso da Lamido da dankwambo ba su kai shi ba.
‘Duk da tsadar rayuwa mutane sun gano Buhari na da kyakkyawar manufa’
Ado Abubakar Musa, dan jarida, mai sharhi a kan al’amuran siyasa a Jihar Filato, ya ce rashin lafiyar Buhari ba za ta kawo masa tarnaki wajen neman wa’adi na biyu a shekarar 2019 ba.
Ya ce, “A ra’ayina, rashin lafiyar da Shugaba Buhari ya yi a watannin baya da kuma yawan shekarunsa ba za su hana shi takara ba a shekarar 2019.”
dan jaridar ya kara da cewa dalili shi ne da alamun lafiyarsa yanzu ta fi ta baya, kuma lafiya da ran dan Adam suna hannun Allah ne. Kuma a yanzu babu wata alama da ta nuna cewa yawan shekarunsa zai hana shi gudanar da mulki.
“Bayan haka, duk da cewa ’yan Najeriya na fama da tsadar rayuwa, hakan ba zai hana Buhari samun nasara a zabe mai zuwa ba, saboda mafi yawan mutane sun gano cewa Buhari yana da kyakkyawar manufa ga Najeriya,” inji shi.
Ya ce ba zai ce babu wasu ’yan matsaloli tattare da gwamnatin Buhari ba, “To amma duk da haka akwai yiwuwar abubuwa za su daidaita nan gaba saboda kowa ya shaida babu wata gwamnati da za ta iya gyara komai a kasa da shekara hudu musamman kasa irin Najeriya da abubuwa suka tabarbare.”
‘Ya cancanci sake tsayawa saboda hakuri da natsuwarsa’
Alhaji Sulaiman Isma’ila Ajingi: Buhari ya cancanci sake tsayawa saboda hakuri da natsuwarsa wanda ba kowane mai mulki ba ne ya ke da wannan. Sannan babu yadda mulkin shekara hudu zai ba da damar aiwatar da kudurorin da ya shirya yi idan a ka yi la’akari da irin halin da ya tsinci kasar nan a ciki na rashin zaman lafiya da kudin gudunarwa. Ba kuma adalci ba ne bayan mutum ya gama sharar gona ya yi wahalar noma da komai saura girbi kawai ya rage sai ka kawar da shi ka sake dawo da wadansu mabarnata su kwashi ganima. A lokacin da ya karbi mulkin kasar nan ya same ta a birkice babu tabbacin cewa za ta ci gaba da kasancewa a dunkule. A haka ya shawo kan manyan matsalolin hare-haren bam, ya raya noma. Abin da ya rage shi ne a wadata manoma da taki, sannan su ma makiyaya a tuna da su.
Duk da kokarin Buhari akwai sauran kalubale
Malam Ibrahim Tanimu: Fatana shi ne Allah Ya zaba mana mafi alheri. Shugaban kasa Buhari yana iyakar kokarinsa, sai dai fa kalubalen kashe-kashe da ya samu kasar a kai har yanzu yana nan ba kamar yadda muka yi zato ba, bayan mun ga sakacin gwamnatin baya. Duk da dai kashe-kashen sun ragu a jihohi irin su Borno da Yobe da Adamawa abin yana nan a wasu wurare kamar Zamfara da Benuwai ga Taraba a yanzu. Ta fuskar ayyuka kuma muna dai ji ana yi ta Legas da wasu wurare, amma ni dai a hanyoyin da nake bi kamar daga nan Abuja zuwa Minna zuwa Kwantagora ko wadda ta nufi zuwa Sarkin-Fawa ta yi Kaduna da wadda ta yi Bidda, duk labarin daya ne suna nan kamar yadda suke a baya, haka abin yake a hanyar da ta tashi daga Abuja ta nufi Kaduna. Game da tsarin zaben sak, kuwa ba na jin irin wannan zaben zai sake yin tasiri a gaba ganin irin abin da hakan ya haifar a yanzu.
Na yi farin ciki sosai da ya amsa kiran jama’a
Malam Muhammad Lawal Adamu: Na yi farin ciki sosai da ya amsa kiran da aka jima ana yi masa. Ba komai ya sa ni jin dadi ba illa zullumin da rashin sanarwar ta haifar saboda irin ayyukan alheri da ya yi. Muhimm a ciki shi ne samar da tsaro da kawar da tashe-tashen bam. Hakan ya ba mu sukunin zuwa kowane yanki na kasar nan ba tare da fuskantar matsalar shingayen kan titi ba kamar yadda yake kafin ya karbi mulki wanda ke jawo tsaiko a tafiya. Sannan kasuwanninmu da a baya abokan hulda da dama suka kaurace musu a dalilin rashin tsaro ga shi yanzu sun farfado jama’a na shigowa cikin natsuwa babu fargaba, wannan ba karamar ni’ima ba ce. Sai dai game da tsarin zaben sak, ina ganin wannan karon zai yi wuya, sai dai a yi shinkafa da wake. Su kuma masu taraddadi a kan rashin koshin lafiyarsa ko cewa ya manyanta, misali guda da zan ba su shi ne, a yau ina ‘yan siyasa da dama da ya tsaya takara da su da ake ganin sun fishi lafiya ko rashin shekaru? Abu mafi muhimmanci da ake bukata a wajen Shugaba ita ce wadatar natsuwa da halin dattijantaka wanda duk Baba Buhari ya hada su.
‘Na yi farin ciki, ban yi farin ciki ba’
Alhaji Isa Abdullahi Zariya: Na yi farin ciki, ban yi farin ciki ba, saboda mabambantan dalilai. Sai dai addu’a guda ita ce idan akwai alheri a dawowarsa Allah Ya tabbatar idan kuwa babu alheri Allah Ya musanya mana da mafi alheri. Dalilin da ya sa ban ji dadin sake tsayawarsa ba kuwa shi ne, idan yadda muke gani haka mulkinsa zai ci gaba da tafiya to abin ba dadi. Koda a kan tsaro da ake ta misali da shi ba dukan kasa ba ce ke cikin halin tsaro, idan ka cire mummunan matsalar tashin bam da aka yi fama da shi a baya, musamman jihohi 3 na Arewa maso Gabas. Yanzu ga jihohi irin su Zamfara da Benuwai da Taraba na fama. Mun san irin gwagwarmayar da muka yi a lokacin zaben baya wajen fafutikar ganin ya samu nasara. Arewa mun samu dama sai dai duk wasu manufofin wannan gwamnati kamar na rufe iyaka sai bakin ruwa kawai, kowa ya san irin cutuwar da al’ummanmu ta yi. Batun tsarin sak kuwa da ake ta magana a kai, na san da gwamnatin sama ta yi abin kyau da su ma gwamnonin da suke cikin wadanda suka ci gajiyar tsarin sak dole su ma su kyautata. Ganin irin sako-sako da ita kanta Gwamnatin Tarayya ta yi ne ta hanyar barin ministocinta suna yin abin da suke so ba tare da tsawata musu ba, ya sa su ma suka bi sahu. Su kuma ’yan majalisa duk wanda ya ce ba su bai wa wannan gwamnatin hadin kai ba, to bai yi musu adalci ba, idan aka yi la’akari da adadin kudirorinta da suka amince da su sabanin na baya.
‘Buhari zai samu kuri’un ’yan Kudu a 2019 fiye da 2015’
Mataimakin Sakataren Jam’iyyar APC a Jihar Legas Mista Femi Saheed ya shaida wa Aminiya cewa Shugaba Buhari ya yi rawar gani a shekara 3 na mulkinsa idan aka dubi kalubalen da ya fuskanta a farkon shekara biyu na mulkin da suka hada da ta’addancin Boko Haram da tsagerun Neja-Delta wadanda suka rika fasa bututun mai da gas da uwa uba da barnar da Jam’iyyar PDP ta shafe shekara 16 tana tafkawa da kuma tabarbarewar tattalin arzikin kasashen duniya da a lokacin. “Amma cikin ikon Allah duk da haka Shugaba Buhari ya yi abin a zo a gani duk da ya shafe kusan shekara daya yana jinya domin a cikin dan kankanen lokaci kasarmu ta fita daga matsalar tattalin arzikin yanzu haka rumbun ajiyar kasar nan na waje ya haura daga Dala biliyan 25 da digo 20 zuwa sama da Dala biliyan 46. Kuma Minista a Ma’aikatar Man Fetur Mista Ibe Kachiku ya bayyana a ranar talatar da ta gabata cewa akwai alamun rumbun ajiyar zai kara haurawa sama zuwa Dala biliyan 50 kafin karshen bana. Wannan shi ke tabbatar da cewa yanzu kasar nan ta samu shugabanci nagari mai tsantseni da rashin darna wanda hakan zai ba da dama a cigaba da samu masu sanya hannun jari daga kasashen ketare,” inji shi.
Mista Femi Saheed ya ce Shugaba Buhari ya yi kokarin daidaita tattalin arziki, ya bunkasa harkokin noma ta yadda a yanzu noma ya yi daraja kuma jama’a da dama suka koma noma. “Shugaba Buhari ya samu karin magoya baya a jihohin Kudu musamman Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu za ka yi mamakin yawan kuri’un da zai samu a zaben badi. Kuma maganar mawuyacin hali da jama’a ke ciki hakan ya biyo bayan barnar da aka tafka a baya ne, kuma cikin ikon Allah zai zama tarihi. Ka san ba abu ne mai sauki a samu yadda ake so cikin shekara 3 bayan an dade ana darna ba, yanzu lokaci ne da Shugaba Buhari ke kan gyara kuma da sannun za a fara cin gajiyar aikin da ya dauko don haka fatana ’yan Najeriya su bai Shugaba Buhari goyon baya a zaben 2019 don kowa ya amfana da gyara da gwababan ayyukan da ya dauko,” inji shi.
Zai karasa ayyukan da ya faro in ya koma – dandamma Yabo
Alhaji Muhammadu dandamma Yabo shi ne Shugaban Jam’iyyar APC bangaren ’yan Arewa mazauna Legas da jihohin Kurmi. A zantawarsa da Aminiya ya ce sake tsayawar Shugaba Buhari takara a badi ne za ta ba shi damar karasa kyawawan ayyukan da ya faro don amfanin kasa da al’ummarta.
“Ka ga ko a yanzu ma yana da ragowar shekara daya muna kuma da tabbacin kara ingantuwar al’amurra, domin a cikin shekara biyu kacal Shugaba Buhari ya yi rawar gani idan ka kalli fuskar tsaro da noma da bunkasa tattalin arziki, don haka lamarin na Allah ne Shi ne Ya san gobe, mu mun yi murna da bayyana zai sake tsayawa takara kuma da yardar Allah ’yan Najeriya za su kada masa kuri’unsu domin ya ci gaba da ayyukan alherin da ya faro,” inji shi.
Alhaji dandamma Yabo ya ce addu’ar da ’yan Najeriya suka yi ta yi wa Shugaba Buhari ita yake bukata a wannan lokaci domin samun cikakkiyar lafiya da karfi da kwazon mulki domin ciyar da kasar nan gaba, “Don haka ina kira ga al’ummar kasar nan mu himmantu da addu’a domin ita ce mafita,” inji shi.
Gyaran Najeriya ce a gaban Buhari ba satar dukiya ba – Ikpeme
Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar APC reshen Jihar Kuros Riba, Mista Carls Ikpeme ya bayyana wa Aminiya cewa “Soki-burutsu ne kawai ’yan adawa ke yi da suke sukar tazarcen Shugaba Buhari, domin duk dan Najeriya mai son zama lafiya ya san wannan gwamnatin Buhari ta yi rawar gani ta samar da zaman lafiya, tsaro ya inganta ta ci lagon ’yan ta’addan Boko Haram.” Ya ce barnar da mulkin PDP ya yi a tsawon shekara 16 a kasar nan ba karamin jan namiji ba ne zai iya gyarawa, amma duk da haka wannan bawan Allah yana yin bakin kokarinsa don al’amura su daidaita.
Da ya juya kan shirin Shugaban na sake tsayawa takara, Ikpeme ya ce “Shawara ce da daukacin ’ya’yan Jam’iyyar APC suka hadu suka yanke na ya sake tsayawa, ’ya’yan jam’iyya sun dade suna fafutikar shawo kansa ya amince ya yi wa’adi biyu domin a jam’iyyance mun fahimci cewa Shugaban kasa ba sace dukiyar kasa ce a gabansa ba ko wani kwadayi, gyaran Najeriya ce a gabansa da son a yi adalci.”