A makon jiya mun kawo tarihin Sarki Usmanu Zamna-Gawa da Yaji dan Tsamiya da Bugayya dan Tsamiya da Kanajeji dan Yaji da Umaru dan Kanajeji da Dauda Abu-A-Sama dan Yaji. A yau za mu ta shi daga kan SarkiAbdullahi Barja dan Kanajeji, Sarki na 15 a jerin sarakunan Habe wanda ya mulki Kano daga 1438 zuwa 1452 Miladiyya.
Abdullahi Barja ɗan Kanajeji (1438 – 1452 Miladiyya)
Abdullahi Barja shi ma ƙane ne ga Sarki Dauda, shi kuma kane ga Sarki Umaru dukkansu ’ya’yan Sarki Ibrahim Kanajeji. Sunan mahaifiyarsa Takiɗa. Sarkin Kano Abdullahi Barja ya zauna a Unguwar Garke. Kuma shi ne Sarkin da ya naɗa jikansa ɗan shekara shida a matsayin Makaman Kano. Wannan kuwa ya faru ne saboda abubuwan al’ajabi da wannan yaro ya riƙa yi.
Sarki Abdullahi Barja ya rasu yana da shekara 67. Ya mulki Kano tsawon shekara 15. Ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya da ya yi ta tsawon kwana 20.
Dakauta dan Abdullahi Barja (1452 Miladiyya)
Sarki Dakauta shi ne Sarkin Kano na17. Shi ne babban ɗan Sarki Abdullahi Barja wanda a wancan lokaci yake riƙe da sarautar Ciroman Kano. Shi ne Sarkin da ya mulki Kano na tsawon kwana ɗaya tak! Wannan al’amari ya biyo bayan kasancewarsa bebe. A farkon al’amari jama’ar Kano sun zaɓe shi Sarki da zaton cewa in ya yi sarauta zai yi magana. Da suka ga an kwana ɗaya bai yi magana ba sai suka tuɓe shi.
Atuma dan Dakauta (1452 Miladiyya)
Atuma ɗan Dakauta shi ne Sarki na 18 a jerin sarakunan Kano. Shi ma kamar mahaifinsa, sarautarsa ba ta tsawaita ba. Bayan an naɗa shi da kwana huɗu sai Galadiman Kano na wancan lokaci ya tubure, ya tattara masu zaɓen Sarki a gidansa ya raɗa musu cewa gaskiya sun yi zaɓen-tumun-dare. Don kuwa sun zaɓo Sarkin da bai san inda ya sa gaba ba, shi a nasa tunanin yana ganin kamata ya yi a ce Wamban Kano Malam Yakubu ya kamata a naɗa. A nan jama’a suka rabu gida biyu. Wadansu suka yarda da shi wadansu kuma suka ƙi. Daga wannan rana abubuwa suka cukurkuɗe har aka yi tsawon kwana bakwai a wannan hali. Saboda haka dole ta sa aka tuɓe Sarki Atuma.
Yakubu dan Abdullahi Barja (1452 – 1463 Miladiyya)
Sarki Yakubu ɗan Barja shi ne Sarki na 19 a jerin sarakunan Kano. Sunan mahaifiyarsa Tasafe. Sarki Yakubu Sarki ne managarci, kuma ya zauna a gidansa da ke Jujin ’Yan Labu.
A zamanin wannan Sarki ƙasar Kano ta samu gagarumin ci gaba ta fuskar ƙaruwar arziki da kuma ilimi.
A zamaninsa ne Fulani suka zo ƙasar Kano daga Malle (wato ƙasar Mali a yau). Zuwan waɗannan Fulani shi ne farkon samuwar ilimin fannin Tauhidi da Lugga a Kano. Sai dai dama tun kafin zuwansu akwai fannonin ilimin Alkur’ani da Fiƙihu da Hadisi.
Ta fannin kasuwanci kuwa a zamani nasa ne cikin shekarar 1453 Miladiyya wadansu Larabawa daga kasar Gadamas suka samu isowa Kano. Da suka iso sai suka wuce fadar Sarki, Shamaki ya yi musu iso suka bayyana cewa su fatake ne suna son yin kasuwanci a garin Kano. Da Sarki ya ji haka ya yi maraba da su kuma ya sa aka nuna musu wani fili da ke unguwar Garke, wato Dandali ke nan. Bayan sun gina gidaje sun zauna sai Kanawa suka riƙa ƙiran wannan wuri da Dandalin Turawa saboda kasancewar fatar Larabawa ja ce, sannan jama’ar wancan lokaci ba sa iya bambacewa a tsakanin Balarabe da Bature. Su kawai duk wata jar fata ko fara sunanta Bature. Wannan shi ne dalili. Duba Gwangwazo (2003).
Sarki Yakubu ya mulki Kano tsawon shekara 12. Ya rasu yana da shekara 55 a duniya, bayan gajeruwar jinya.
Muhammadu Rumfa 1463 – 1499 Miladiyya
Muhammadu Rumfa shi ne Sarkin Kano na 20. Shi ne wanda aka yi wa sarautar Makaman Kano lokacin yana ɗan shekara shida a duniya. Wannan kuwa ya faru ne bayan wani abin mamaki da ya faru da shi. Shi Muhammadu Rumfa asalin sunansa shi ne Muhammadu Mansur, kuma jikan Sarkin Kano Abdullahi Barja. Abdullahi Barja ne mahaifin mahaifiyar Muhammadu Rumfa (wato ke nan shi Muhammadu Rumfa ya gaji sarautar Kano ce ta ɓangaren mahaifiyarsa).
A lokacin Sarki Abdullahi Barja, karnuka sun riƙa zuwa suna cinye wa talakawan Kano guntun tuwon da suka ci suka rage da daddare. Da al’amari ya yi ƙamari, sai talakawa suka haɗa kansu suka ɗunguma zuwa fada, da isarsu fada sai Shamakin Sarki na wancan lokacin ya tambaye su me ke tafe da su. Sai suka shaida masa cewa sun kawo ƙarar dukkan karnukan Kano ne. Daga nan sai Shamaki ya yi musu jagaba ya kai su gaban Sarki. Da isarsu gaban Sarki suka faɗi, suka yi gaisuwa sannan suka faɗi kokensu cewa karnuka ke zuwa da daddare suna cinye musu guntun tuwon da suka ci suka rage da daddare, wanda hakan ke jawo musu rashin na karin kummalo. Saboda haka suna ƙarar dukkan karnukan Kano. Da Sarki ya ji haka, sai ya ɗan yi shiru, jim kaɗan, sai ya juya ya tambayi fadawa ko da shawara. To a daidai wannan lokaci wannan jika nasa Muhammadu Mansur yana gefen karagarsa yana wasa. Sai caraf! Ya ce da Sarki, su koma kawai su je su yi rumfuna a ƙofar ɗakunansu sai su riƙa ɗora guntun tuwon har da miyar a kan rumfunan.
Talakawa suna ji, sai Sarki ya ce kai ku rabu da shirme na yara. Fada mece ce shawara? Sai Galadiman Kano, Daudu, ya kada baki ya ce da Sarki ai wannan magana ya yi ta hankali. Saboda haka sai su tafi su gwada. Sarki ya ba su umarni cewa su je su gwada duk abin da ya faru sai su dawo gobe. Talakawa suka koma suka kakkafa rumfuna a ƙofar ɗakunansu.
Sannan da dare ya yi aka ci tuwo aka rage sai suka ɗoɗɗora tuwo da miya a kan rumfuna. Da gari ya waye suka tarar da tuwonsu ba abin da ya same shi. sai suka ɗauko suka ɗumama tuwon suka ci suka yi hani’an. Sannan sai suka sake ɗunguma zuwa fada a karo na biyu. Da suka isa sai Shamaki ya yi musu iso, suka je gaban Sarki, suka sanar da sarki abin da ya gudana cewa wannan shawara ta yaro ta yi aiki. Sannan suka yi wa yaro addu’ar zamowa sarkin Kano a gaba.
Sarki Muhammdu Rumfa Sarki ne da babu kama tasa ana masa kirari da- Balaraben Sarki ya gyara kasa. A zamaninsa yaKi ya auku tsakanin Kanawa da Katsinawa shekara 11 babu wanda ya yi rinjaye Sarki Rumfa shi ne ya fara abu biyu a Kano. 1 ya gina gidan nan da ake cewa Gidan Rumfa da shekara ta kewayo ya kara birni tun daga Kofar Dagaci zuwa Kofar Mata zuwa Kofar Gyarta Wasa zuwa Kofar Kawaye zuwa Kofar Na’isa zuwa Kofar Kansakali. Da shekara ta komo ya gina gidansa shi ne ya kafa Kasuwar Kurmi, kuma ya fara Dawakin Zage domin yakin Katsina. Shi ne wanda ya fara kulle,ya fara tara Dabo da Kakaki da Takalman Jimina da Figini. Shi ne ya fara Sallar Idi a sha da koko shi ne ya fara bai wa babanni sarauta da sauransu.
Abdullahi dan Muhammadu Rumfa 1499-1509 Miladiyya
Sarki Abdullahi dan Muhammadu Rumfa shi ne Sarki na 21 a sarakunan Kano. Sunan mahaifiyarsa Lamis. Sarki ne mai himma. A zamaninsa ya yaƙi ƙasar Hausa Gabas da Yamma, Kudu da Arewa kuma ya yi nasara.
Muhammad Kisoki (1509-1565)
Sarki Kisoke shi ne na 22 a sarakunan Kano ya yi yaƙi da Sarkin Borno kuma ya gagari Sarkin Borno. Bayan da Sarkin Borno ya zo Kano ta gagare shi, sai Sarki Kisoke ya sa aka hau kan ganuwa aka rika yi masa kirari kamar haka: “Kisoke Cirata, Kisoke Borno, Kisoke Maganin Ciratawa”.
An samu yawaitar shigowar manyan malamai zuwa Kano a zamaninsa. Daga cikin waɗannan mashahuran malamai akwai, Shehu Batunashe wanda ya kawo Ashafa Kano, sai Ɗangwauron Duma. Sannan akwai Shehu Abdussalami wanda shi kuma ya kawo Mudawwana da Jami’u Sangiri da kuma Samarƙandi; dukkan waɗannan littattafan addini ne. Sannan a wannan zamani ne wani mutum wai shi Tubi ya zo daga kasar Zazzau ya yi karatu a hannun Shehu Batunashe.
Sarki Kisoke ne gina Masallacin Rumawa bayan Shehu Batunashe ya buƙaci haka. A zamaninsa ne wadansu mashahuran malamai biyu wa da ƙane suka zo daga Borno. Sunansu Shehu Kursiki da Shehu Magume. Sarki Kisoke ya nemi ya naɗa Shehu Kursiki a matsayin alƙalin Kano amma ya ƙi. Da Sarki ya buƙaci ƙanensa ya zama shi kuma sai ya yarda. Shehu Magume ya karɓi alƙalancin Kano sannan ya kafa rumfa a ƙofar fada.
Sarki Muhammadu Kisoke ya yi sarautar Kano na tsawon shekara 58. Daga nan rai ya yi halinsa.
Yakubu ɗan Kisoke (1565 Miladiyya)
Yakufu ɗan Kisoke shi ne sarki na 23 a sarakunan Kano. Sunan mahaifiyarsa Tunasa. Sarautarsa ba ta yi tsawo ba. Ya mulki Kano tsawon wata huɗu da kwana 20. Wani mutum da ake kira Gulle daga cikin zuriyar sarakunan nan Kano ya tuɓe shi. Bayan da ya tuɓe shi sai Yakubu ya fice daga garin Kano ya tafi zuwa ga wani malami a ƙauye ya yi ta karatunsa har lokacinsa ya yi. Bayan da Gulle ya tuɓe shi sai Galadima Sarkatunya ya yaƙe shi. An ɗauki tsawon kwana 40 ana gwabza yaƙi kafin Galadima ya kashe Gulle.
Dauda Abasama dan Yakubu (1565 Miladiyya)
Sarki Dauda shi ne Sarki na 24 a jerin sarakunan Kano. Bayan Galadima Sarkatunya ya kashe Gwalle, sai ya naɗa Dauda ɗan Sarki Yakubu, tunda shi Sarki Yakubu ya ƙi yarda ya koma. Shi ma kamar mahaifinsa, sarautarsa ba ta yi tsawo ba. Ya zauna a gadon mulki na tsawon wata ɗaya da kwana 20 kacal, aka tuɓe shi. Bayan an tuɓe shi sai ya tarkata ’yan uwansa ciki har da shaƙiƙiyarsa Tabuduru, da sauransu suka rankaya zuwa Kwarmashe.
Abubakar Kaɗo dan Rumfa (1565 – 1573 Miladiyya)
Sarki Abubakar shi ne Sarki na 25. Sarki Abubakar shaƙiƙin Sarki Abdullahi ɗan Rumfa ne (wato Sarkin Kano na 21). Sarki Abubakar Sarki ne mai addini. Shi ne Sarkin da ya fara sauke Ashafa. Sannan ya karantar da ’ya’yansa. Yana da ’ya’ya bakwai. Addini ya bunƙasa a zamaninsa. Ya yi mulkin Kano na shekara bakwai da wata shida. Shi ma tuɓe shi aka yi.
Mun ciro wannan rubutu daga: Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Gobernment Press, Kano.
Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna. Da kuma shafin intanet.
Za mu ci gaba.