Kafin bayyanar jihadin Shehu Usman dan Fodiyo babu wani abu da aka sani da suna kasar Bauchi. Abin da kawai aka sani shi ne wasu ’yan kananan garuruwa da wadansu kananan sarakuna na Habe suke mulkinsu. Mutanen suna gauraye da Fulani da Hausawan da ke zaune a yankunansu. Manyan sarakunan lokacin su ne: Sarkin Miri da na Ganjuwa da na Sum da na Lere da na Kirfi da sauransu. Kowane Sarki yana kula da jama’arsa yana kokarin tsare su daga harin makwabta. Sukan rika karbar wani abu daga jama’arsu a matsayin kudin gandu bisa ga al’ada. A cikinsu akwai masu jama’a da yawa kamar Gonsal (Jarawan Bununu). Akwai kuma manyan Hardube na Fulani a cikin kasashensu – kamar Hardon Zaranda da Hardon Bula da sauransu, sannan Fulanin Ganjuwa da Jetar da sauransu- duk suna karkashin sarakunan Habe ne a wancan lokaci.
Yadda Fulani suke a karkashin Sarakunan Habe:
Kamar yadda muka fadi a baya, akwai garuruwan fulani da suke karkashin sarakunan Habe kuma suna bin su ana zaune lafiya, idan wani abu ya dami Fulanin nan sukan kai kuka wajen sarakunan nan: Misali lokacin da wurin kiwo ya yi wa Abdullahi Dadi mahaifin Yakubu kadan a Gilliri, sai ya zo ya roki Sarkin Yuli a kan ya ba shi wurin kiwo isasshe. Sai Sarkin ’Yuli ya ki, sai Abdullahi Dadi ya kai maganar wurin Sarkin Miri (wanda shi ne babban Sarkin wannan yankin a lokacin). Sai Sarkin Miri ya kira Sarkin ’Yuli ya sa shi ya ba Abdullahi Dadi makiyayar da ya roka.
Yadda Malam Yakubu ya fara lamarinsa kafin ya tafi Sakkwato:
Malam Yakubu, Abdullahi Dadi ne ya haife shi a kauyen Tirwun (wani kauye da ke Gabas maso Arewa da garin Bauchi). Mahaifiyarsa Bagera ce, wato lokacin da Sarkin Miri ya ba Abdullahi Dadi izinin zama a fadamar Tirwun ya zo ya iske makwabtansa a wurin Gerawa ne har aure ya shiga tsakani ya haifi Malam Yakubu. A nan Tirwun aka haifi Malam Yakubu kafin bayyana da kuma jihadin Shehu Usman dan Fodiyo da ’yan shekaru. A lokacin mahaifinsa Abdullahi Dadi shi ne Sarkin Tirwun, kuma Malam Yakubu shi ne da na biyu a wurin mahaifiyarsa. Mace ce babbarsu sai maza uku da suka hada da shi Yakubu da mai bi masa Dauda da kuma Sulaiman.
Malam Yakubu tun yana yaro ya nuna yana son addini, domin duk lokacin da malaman Musulunci abokan mahaifinsa suka zo yakan fito ya zauna tare da su, wato kamar su Malam Isiyaku da Malam Adama da Malam Lawal. Shi Malam Adama ya auri kanwar Abdullahi Dadi mahaifin Yakubu. To da Yakubu ya fara datawa kamar shekara bakwai, sai mahaifinsa ya bashe shi ga Malam Isiyaku ya ce ya karantar da shi a can garinsu kauyen Jetar. Yakubu bai fi shekara 10 da haihuwa ba, suka tafi Sakkwato wurin Shehu Usman dan Fodio tare da malaminsa Malam Isiyaku. Bayan shekara shi da malaminsa sun zo duba gida suka sake komawa shi da malaminsa. Daga baya suka sake kamo hanya za su zo duba gida, sai malamin nasa ya rasu a wani gari da ake kira Yalwan danzai da ke kasar Kano. Bayan rasuwar malaminsa, sai Malam Yakubu ya ci gaba da dalibtarsa a wurin Shehu Usman dan Fodiyo har zuwa lokacin da aka ba su tutar jihadi.
Yakubu ya yi auren farko ne a kan hanyarsa ta dawowa gida, inda ya auri wata mace mai suna Yaya a Zamfara. Da ita ya haifi babban dansa Muhammadu wanda aka kashe a yakin Dass.
Malam Yakubu dan Abdullahi Dadi, yana daga cikin almajiran Shehu Usman dan Fodiyo da suka karbo tutar jihadi daga wurinsa. Shi ne ya kafa garin Bauchi cibiyar masarautar Bauchi wadda a baya ta nausa har zuwa Wase a Jihar Filato. Ya yi yake-yake 43, daga ciki har da fitaccen yakin nan da ake kira “Yakin Kanembu,” kuma autar yakinsa shi ne yakin da ya yi da Tsaure. Malam Yakubu ya kasance shamakin da ke katange kasashen Musulmi daga kafirai, wannan ne ya sa ake yi masa kirari da “Sarkin Yakin Shehu Usman dan Fodiyo ko kuma Sarkin Yakin Sarkin Musulmi.”
Yadda Malam Yakubu ya zama almajirin Shehu dan Fodiyo:
Mahaifin Yakubu, Malam Abdullahi Dadi yana da ’yar uwa da take auren wani Malami mai suna Malam Adama wanda yake zaune a wani kauye da ke Kudu da Tirwun da ake kira Jetar. Wannan ’yar uwa ta Dadi ita ce ta yaye Malam Yakubu, inda ya girma a can wurin Malam Adama. Gwaggon Yakubu ta haifi dan namiji da aka sanya masa suna Hammadi, shi ne tushen gidan Ajiyan Bauchi. Yakubu ya tashi tare da Hammadi a wurin gwaggonsa. Malam Adama yana da wani kane mai suna Malam Isiyaku wanda yake da da mai suna Lawal. Yakubu yana can wurin gwaggonsa, sai dai ya je Tirwun ya dubo mahaifansa.
Yana Jetar yana karatu a wurin Malam Adama da kuma Malam Isiyaku sai aka samu labarin bayyanar Shehu Usman dan Fodiyo. Sai Malam Isiyaku ya ce da wansa Malam Adama zai tafi wurin Shehu Usman ya gan shi ko zai karu da wani abu. Da ya yi shirin tafiya sai Malam Adama ya ce su tafi tare da babban dansa Lawal, sai Malam Isiyaku ya ce yana so su tafi tare da Malam Isiyaku. A lokacin Malam Yakubu yana yaro domin bai cika shekara tara ba. haka suka kama hanya su uku, a kwana a tashi har suka isa Sakkwato. Malam Isiyaku ya shekara biyu a wurin Shehu Usman yana karatu.
Bayan shekara biyu, sai Malam Isiyaku ya shaida wa Shehu Usman dan Fodiyo cewa suna so su koma gida, domin su dubo su, saboda sun dade rabonsu da iyalansu. Sai Shehu dan Fodiyo ya ce, to amma yana son ya bar Yakubu a wurinsa. Sai Malam Isiyaku ya ce da Shehu Usman: “Allah gafarta Malam na fi son mu koma tare da shi, saboda iyayensa. Domin in ba su gan shi ba, za su zaci ko ya mutu ne ko kuma ya bace.” Sai Shehu dan Fodiyo ya ce: “Ai yana tare da iyayensa in dai batun iyaye ne.”
Shi ke nan sai Malam Isiyaku ya taso tare da Lawal suka bar Yakubu a wurin Shehu. Yakubu ya zauna cikin almajiran Shehu dan Fodiyo yana ta yin karatu har shekara shida. A cikin shekara ta shida ce Allah Ya yi wa mahaifin Yakubu Malam Abdullahi Dadi rasuwa.
Bisa ga al’ada yadda almajiran Shehu suke yi, kullum da sassafe sai su taho su gaishe shi. Ranar sun zo gaishe shi sai Yakubu ya zo daga baya da zuwansa sai ya yi gaisuwa: Sai Shehu Usman ya ce masa: “Yakubu” Sai Yakubu ya amsa. Sai Shehu ya ce: :Jiya mahaifinka ya rasu da safe a can garinku.” Shehu ya yi masa ta’aziyya, sannan ya ce masa: “Sai ka yi niyya ka tafi gida, kuma ka tashi tun yau.”
Lokacin da Yakubu ya ji wannan labari daga Shehu ya so ya yi shakkar abin. Sai Shehu ya ce masa: “A’a, kada ka yi haka Yakubu.” Sai Yakubu ya ce: “Na tuba.” Shehu ya ce: “Je ka na yafe ka, maza ka yi niyya ka tashi. Kuma za ka je ka samu ’yan uwanka sun tara kayayyakin mahaifinka wuri daya suna jiranka. Amma in ka je kada ka dauki komai daga cikin dukiyar da ya bari, sai wani kwarinsa da yake ratayawa idan zai je shingensa (shingen shanu), akwai kibiya guda bakwai a ciki, shi kadai za ka dauka, domin zai taimake ka. (Wannan kwari shi ake kira kare-dangi.”
Da Yakubu zai tashi sai ya ce da Shehu: “To Allah gafarta Malam wata nawa zan yi kafin in komo?” Sai Shehu ya ce: “In ka tafi gida ka shekara tukun sannan ka dawo.”
Yakubu ya taso a ranar daga Sakkwato yana tafe yana yada zango har ya isa Tirwun bayan ya shafe kwana 40 a kan hanya. Bayan ya sauka ya huta, sannan suka yi gaisuwa da ’yan uwansa. Sannan suka shaida masa cewa yau rasuwar mahaifnsu kwana 41 ke nan. Lissafain rasuwar mahaifinsa ya zo daidai da ranar da Shehu Usman dan Fodiyo ya fada wa Yakubu. Da Yakubu ya ji haka, sai ya kara razana da al’amarin Shehu Usman dan Fodiyo a ransa.
Daga nan suka nuna wa Yakubu iyakacin abubuwan da mahaifinsu ya rasu ya bari. Suka ce masa “Da ma kai muke jira.” Yakubu ya ce: “Haka ne.” Sai ya san hannunsa ya dauki kwarin nan da Shehu Usman dan Fodiyo ya umarce shi, ya ce musu wannan kadai zai dauka ya kuwa ishe shi. Sauran dukiya duka ba ya son komai a ciki, su raba a tsakaninsu.
Yana nan zaune a Tirwun a tsakanin ’yan uwansa har ya cika shekara daya. Ran nan sai ya yi sallama da ’yan uwansa ya ce musu zai koma Sakkwato wurin Shehu dan Fodiyo. Suka yi ban-kwana da shi suka ce yi masa addu’a Allah Ya kai shi lafiya Ya dawo da shi lafiya kuma ya same su lafiya. Sai ya kama hanya ga shi nan tafe har Sakkwato.
Yakubu ya karbi tuta daga Shehu:
Da Yakubu ya koma Sakkwato wurin Shehu dan Fodiyo, ba sake dawowa gida ba, sai bayan shekara shida, wato dawowar da ya yi da Tutar Musulunci. Sai dai bai fito da ita fili ya nuna ba ya bar ta a boye cikin gafakarsa bai nuna wa kowa ba. Da ya iso bai zauna a Tirwun ba, sai ya zauna a kusa da gindin dutsen Warinje ya shekara biyu a wurin yana almajirancinsa yana karantarwa.
Malam Yakubu ya karbi tuta ne lokaci daya da sauran almajiran Shehu dan Fodiyo, kuma umarni daya aka ba su. Sai dai shi Malam Yakubu bayan tutar Shehu ya mayar masa da kwarin nan mai kibau 14 (Zabgai 7 da kare-Dangi 7). Kuma abin da Malam Yakubu ya tarar a tasa kasar bai zamo daya da na sauran almajiran Shehu ba, domin kasarsa ba wata babbar daula ba ce da zai yi faman rushe ta. Saboda haka aikinsa shi ne jihadin tabbatar da kafuwar daular Musulunci. Daga isowarsa gida wadanda suka fara amincewa da shi Fulani ne da kuma wadansu Habe da ba su yi yaki da shi ba. Fitattu daga cikin Fulanin na su ne: Fulanin Jahun da na Gok da na Wunti da na ’Yuli da na Ganjuwa wadanda da su Malam Yakubu ya fara jihadi da bude kasar Bauchi.
Bayan shekara biyu (tare da almajiransa), sai ya koma Sakkwato da wadansu almajiransa, amma a wannan tafiyar bai dade ba, ya komo da tutar jihadi a fili. Da zuwansa bai tsaya ko’ina ba, sai kauyen Inkil (da ke gabas kadan da garin Bauchi). A nan ya fara kafa mashinsa na jihadi. Ya zauna cikin Inkil shekara takwas. Duk kauyukan da suke kusa da Inkil ya yi jihadi da su. A lokacin kuwa yana da almajirai da yawa, daga cikinsu akwai manya guda uku, dukansu kuwa sai da ya yi musu sarauta suka zama hakimansa. Su ne Hasan da Faruku da Muhammad sai kuma wani baransa mai suna Abdu, wato shi ba almajirin Yukubu ba ne.
Bayan ya shekara takwas a Inkil, sai ya yi niyya ya koma Sakkwato wurin Shehu dan Fodiyo domin ya taimake shi da shawarar inda zai kafa garinsa na kansa ya zauna. Da ya tafi Sakkwato, ya shaida wa Shehu bukatarsa, sai Shehu ya ce masa: “To ai kai ka san kasarka, kai ya kamata ka tafi inda kake so. Ni tawa ai shawara ce.” A kan shawarar sai da Yakubu ya ambata wa Shehu wurare biyar.
Da farko Yakubu ya ce da Shehu ya fi son ya zauna a Inkil. Shehu ya ce, “Inkil akwai lafiya, sai dai in ka zauna zuriyarka za su ki addini, za su zama mawaka.” Sai Yakubu ya ce, “To tunda yake haka ne na fi son in zauna a Zaranda (kimanin ikilomita 40 yamma da Bauchi).” Shehu ya ce: “In ka zauna a Zaranda za ta yi arzikin tumaki/awaki, sai dai babu imani kuma wurin yana da yalwar abinci.” Yakubu ya ce: “To Gwauron Dutse fa wato Wase (da ke Jihar Filato a yanzu)?” Sai Shehu ya ce: “In ka zauna a wurin baranka ma sai ya yi lifidi dubu, sai dai babu imani a wurin ko kadan.” Sai Yakubu ya ce: “To Baba fa?” Sai Shehu ya ce, “Wato inda kabarin Idrisu yake ko?” Sannan ya ce: “In ka zauni wurin talakanka ma zai nomi dame dubu, amma addininka ba zai gama da Mahdi ba.”
Daga kan wannan gari sai Yakubu ya ce da Shehu ya bar masa zabi da dabara duka, sai kuma abin da ya ce. Shehu ya ce masa: “A’a duba dai.” A lokacin da suke wannan abu kuwa akwai wani tsohon baran Shehu mai suna Modegel, shi ne ke zuba ruwa a masallacin Shehu. To sai Modegel ya ce da Shehu: “Allah Ya gafarta Malam, tunda yake dai Yakubu ya samu yarda gare ka, ya yi kuma iyakar kokarinsa. Yanzu sai ka zaba masa inda ka ga ya fi kyau ya zauna.”