Majalisar Dattawa ta sanya ranar Talata 13 ga watan Disamba, 2022, domin nazari kan sabuwar dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) ta kayyade kudaden da jama’a za su iya cirewa a rana.
Majalisar dai ta nuna damuwa a zamanta na ranar Laraba kan sabon tsarin na CBN.
- Kamaru za mu koma muddin Peter Obi ya fadi zaben 2023 – Babachir
- NAJERIYA A YAU: Yadda Tsarin Takaita Cire Kudade Zai Shafi Zaben 2023
A karkashin sabon tsarin, mafi yawan kudin da daidaikun mutane za su iya cirewa a mako ta POS shi ne N100,000, kamfanon kuma Naira 500,000.
Sabon tsarin ya kuma kayyade dubu N20,000 a matsayin iya abin da mutum zai iya fitarwa a rana, amma ba zai cire fiye da N100,000 ba a mako.
Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Phillip Aduda, ya ja hankalin takwarorinsa kan yin taka-tsan-tsan game da sabon tsarin, domin a cewarsa, zai shafi ’yan kasa da dama, musamman kananan ’yan kasuwa.
Da yake mayar da martani kan lamarin, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya gargadi CBN kan sabon tsarin, inda ya umarci kwamitin harkokin banki ya yi aiki tare da CBN, su tattauna kan lamarin a yayin tantance Mataimakin Gwamnan CBN, wanda ake sa ran za a gudanar kafin mako mai zuwa.