Takaddamar da za a iya kauce mata da ta jawo yakin cacar baki a tsakanin Fadar Shugaban kasa da Majalisar Dokoki ta kasa a bayan nan ta kunnu ne bayan da Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a Malam Abubakar Malami (SAN) ya ki amsa gayyatar da Majalisar Dattawa ta yi masa nay a bayyana a gabanta. Kwamitin Harkokin Shari’a da Kare Hakkin dan Adam na majalisar ne ya gayyace shi game da batun gurfanar da Shugaban Majalisar Sanata Bukola Saraki da Mataimakinsa Sanata Ike Ekweremadu, wadanda aka gurfanar a gaban kotu tare da tsohon Akawun Majalisar Dokoki ta kasa Alhaji Salisu Maikasuwa da Mataimakinsa Mista Ben Efeture kan zargin yin jabun dokokin gudanar da majalisar a lokacin zaben shugabannin majalisar a watan Yunin bara.
Maimakon ya amsa gayyatar, sai Ministan ya tura mai taimaka wa Shugaba kan gabatar da masu kara a gaban kotun Mista Okoi Obono-Obla ya wakilce shi.
Kuma a cewar Obla, Majalisar dattawa ba ta da ikon gayyatar Ministan Shari’ar zuwa zaurenta tunda ba ita ta nada shi Minista ba kuma ba yana karkashinta ba ne. Majalisar a nata bangaren sai ta kori Mista Obla nan take kuma ta fara shirye-shiryen yadda za ta sa Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya ya kama shi.
Wannan abin kaico bai auku ba ne sakamakon yadda wadansu masu fatar alheri suka tsoma baki wajen bayar da hakuri ga bangarorin biyu da suka sanya zare.
kiyawar da Ministan ya yin a bin umarnin Majalisar Dattawa, abu ne mai daure kai, ganin cewa shi ne babban jami’in tabbatar da bin doka da oda ana sa ran yana da cikakkiyar masaniya kan tsarin mulki da kuma doka.
Da’awarsa ta cewa Majalisar ba ta da ikon gayyatarsa bai da madogara a doka. Sashi na 88 na tsarin mulki ya fayyace ikon Majalisar Dattawa a fili na tana iya gayatar kowane mutum gabanta, kan lamarin da ya shafi bukatun jama’a. Don haka naciyar Malami da Obla na cewa Majalisar Dattawa ba za ta iya gayyatar Malami ba, akalla kuskure ne. Baya ga haka, Ministan Shari’a ma’aikacin gwamnati ne da sai da Majalisar Dattawan ta tantance shi ta wanke shi kafin a nada shi. Saboda haka tsarin mulki da ya ba Babban Lauyan Tarayya ikon yanke shawara kan gabatar da kara ko janye ta a karkashin tanadinsa shi ne kuma ya ba majalisar nata ikon. Kuma a yayin da wannan iko ne marar iyaka, ana sa ran a rika bin ka’ida wajen aiwatar da shi tare da lura da shari’ar da kuma abin da zai zame alheri ga jama’a.
Ministan yana da ’yancin ya yi zargi kan manufar gayyatar da majalisar ta yi masa, tunda ta gina batun ne kan bukatar da ta shafi shari’ar shugabanninta. To amma abin da zai yi ba shi ne ya ki amsa gayyatar ya bayyana a gaban Majalisar Dattawan ba, kamata ya yi ya yi amfani da wannan dama wajen gabatar da duk wata hujja da yake da ita da niyyar fahimtar da ’yan Najeriya cikakkiyar manufar batun da ake magana a kai.Yana kuma iya cewa ba zai yi bayani dalla-dalla kan shari’ar ba, saboda an riga an kai ta gaban kotu.
Gurfanar da irin wadannan manyan mutane a gaban kotu ba batu ne da za a dauke shi karami ba, saboda yadda yake samun watsuwa da jawo hankalin a tsakanin ’yan Najeriya. Kuma yana kara kawo tsamin dangantaka a tsakanin Fadar Shugaban kasa da Majalisar Dokoki ta kasa, inda batun ya rika haduwa da murgude-murguden hakikaninsa a tsakanin jama’a, inda ya bar ’yan Najeriya suka kasa bambance karya da gaskiya.
Don haka wajibi ne a kan Ministan Shari’a ya yi amfani da duk wata dama da aka ba shi ya fahimtar da ’yan Najeriya kan lamarin domin amfanin kasa. kin amsa gayyatar da ya yi ya say a hana ’yan Najeriya sanin cikakken bayani kan lamarin.
Zuwa ranar Talata, Majalisar Dattawa ta bai wa Ministan awa 48 wato zuwa jiya Alhamis ya bayyana a gabanta ko ta sa ’yan sanda su kama shi. Muna kira da kada a bari lamarin ya kai ga haka. Takardar umarnin ’yan sanda su kama Ministan Shari’a mataki ne mai hadari idan aka lura da irin hakan a baya. ’Yan sanda sun saba da bin umarnin Ministan Shari’a me a kan umarnin Majalisar Dokoki, kamarb yadda takaddamar Majalisar Dokokin Jihar Kogi ta nuna. Ya kamata a yi taka-tsantsan tare da aiki da hankali a wannan al’amari. Tsarin Mulki yana da cikakkiyar shiryarwa kan ayyukan ma’aikata da jami’an gwamnati.
Takaddamar Majalisar Dattawa da Ministan Shari’a
Takaddamar da za a iya kauce mata da ta jawo yakin cacar baki a tsakanin Fadar Shugaban kasa da Majalisar Dokoki ta kasa a bayan…