A ranar Juma’ar da ta gabata ce Gwamnatin Tarayya ta bakin Ministan Watsa Labarai Alhaji Lai Mohammed ta bayyana sunayen mutum 23 daga cikin wadanda take zargi da sace dukiyar gwamnati lokacin mulkin da ya gabata, inda sakin sunayen ya jawo takaddama mai zafi a kasar nan.
Tuni wadansu daga cikin wadanda sunayensu suka fito a jerin sunayen da gwamnatin ta fitar suka fara barazanar garzayawa kotu don kalubalantar hakan, tare da bayyana cewa an yi haka ne kawai saboda dalili na siyasa da kuma kokarin bata musu suna.
Daga cikin wadanda suka ce za su tafi kotu akwai tsohon Gwamnan Jihar Neja Alhaji Babangida Aliyu wanda aka bayyana cewa ya karbi Naira biliyan daya da rabi daga Sambo Dasuki. Ya ce zai garzaya kotu bayan ya tuntubi lauyoyinsa domin tilasta Gwamnatin Tarayya ta gabatar da takardun da za su tabbatar da ya karbi wannan kudi, inda ya ce gwamnatin APC tana yin haka ne domin ta kulle masa baki saboda ya ki shiga jam’iyyar.
Ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa: “A kokarin bata min suna yanzu haka an gurfanar da ni a gaban Babbar Kotun Tarayya da kuma Babbar Kotun Jihar Neja kan wannan zargi. Wannan shi ne yadda gwamnatin ta sha alwashin karya ni, amma ba za su samu nasara ba.”
Shi ma Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa, Mista Uche Secondus, ya shaida wa Minista Lai Mohammed cewa ya zauna cikin shirin kawo hujjojinsa a gaban kotu cewa ya karbi Naira miliyan 200 daga Sambo Dasuki.
Kakakinsa Ike Abonyi ya fadi a ranar Juma’ar a Abuja, cewa manufar Ministan ita ce ya bata masa suna tare da kawar da hankalinsa daga yi wa PDP aiki, kuma ba zai samu nasara ba. “Muna sanar da jama’a Yarima Secondus bai karbi wani kudi daga Mashawarcin Shugaban kasa kan Tsaro ba, ta kowace hanya,” inji sanarwar Abonyi..
Bayan fitar da jerin sunayen Aminiya ta tattauna da Malam Auwal Musa Rafasanjani jagoran kungiyar tabbatar da rikon amana (Transparency International) a Najeriya, kuma Babban Daraktan Cibiyar Kare Hakkin Jama’a da Dokoki (CISLAC), kan dambawar da ta biyo baya, inda ya ce Gwamnatin Tarayya ta makara kan fitar da sunayen, shi ya sa wadanda ake zargin suke musantawa. Shi kuma wani fitaccen lauya da ke Abuja Barista Modibbo Muhammad Bakari ya ce, fitar da jerin sunayen ba zai yi tasiri a shari’a ko siyasar wadanda abin ya shafa ba, sai kotu ta same su da laifi.
Tuntuni ya kamata gwamnatin Buhari ta fitar da sunayen – Auwal Rafsanjani
Me za ka ce a kan dambarwar da ta biyo bayan bayyana sunayen wadanda ake zargi da sace dukiyar kasar nan da Gwamnatin Tarayya ta yi?
Wannan muhimmin al’amari ne da bai dace ya dau salon siyasar da ya dauka ba, mutanen da ake zargin sun ci amanar da aka ba su ta dukiyar kasa kamar yadda bincike ke nunawa, har wadansu daga cikinsu sun fara mayar da kudin. To tunda dai a baya kotu ta ba da umarnin a bayyana sunayensu amma gwamnati ba ta bayyana ba da kamata ya yi a ci gaban da bin wancan tsarin na mayar da kudin da ci gaba da shari’ar ba a bayyana sunayensu yanzu da ake dab da fara harkar zabe ba. Wanda ga shi hakan ya ba su damar cewa siyasa ce kawai, kuma su ma sun bi salon siyasar suna karyatawa. Kada ka manta a baya kotu ta ba da umarnin bayyana sunayen, amma gwamnati ba ta bayyana ba. Fatana gwamnati ta dauki mataki mai tsauri na yi musu shari’a sannan duk wanda aka same shi da laifi a yi masa hukunci mai tsauri don zama darasi ga na baya.
Ba ka ganin gwamnati ta yi jinkirin bayyana sunayen ne don ba da damar mayar da kudin?
Wannan ba hujja ba ce, alama ce ta gazawa da kuma sassauci a kan al’amarin kasa. Jinkirtawar ya ba su damar musantawa ne kawai kamar yadda suka fara yi a yanzu. Sannan wasu abubuwa da jami’an wannan gwamnatin suka aikata sun nuna ba da gaske take yi ba, idan ana so a nuna da gaske ake yi to a gayyaci jami’an wannan gwamnatin da ake zargi da almundahana a yi musu bincike idan aka same su da laifi a hukunta su. Haka akwai tarin wadansu da ake zargi tare da wadancan mutane, amma suka sauya sheka zuwa jam’iyyar da ke mulki, ga shi har yanzu su ba a ga an yi musu komai ba.
Mene ne hadarin barin irin wadannan al’amura a matakin siyasa kawai ba tare da zantar da hukunci a kai ba?
Ai ga shi nan muna ciki kasa ta shiga cikin wani hali, ba ayyukan yi ga talauci ga rigingimu iri-iri, ba komai ya kai mu ga hakan ba illa wannan barnar ta sace dukiyar kasa inda maimakon a yi aiki da dukiyar wajen habaka ayyukan yi da na tattalin arzikin kasa sai dai a kashe dukiyar wajen haddasa rigingimu da ruguza tattalin arziki. Sannan cin hancin nan da ke ci gaba da gudana har zuwa yanzu, shi ke hana daukar wadanda suka cancanta a al’amura sai dai ’yan gata, ga matasa sun gama makaranta amma kafin a samu aiki sai an kashe makudan kudi.
To mene ne kake ganin mafita?
Mu dai a kungiyarmu ta Transparency International da kuma CISLAC muna gani wasu miyagun almundahanar da ke gudana a cikin wannan gwamnati a yanzu haka ba lallai ba ne Shugaban kasa yana da masaniya a kai, saboda haka za mu aika masa da wasika a kan wasu munanan abubuwan da muke zargi ana aikatawa, sannan bayan mako biyu idan muka ji shiru ba tare da an dauki wani matakin gudanar da bincike a kai ba. Za ku ji abin da zai biyo baya na fasa kwai.
Bayyana sunayen ba zai yi tasiri a shari’a ko a siyasa ba – Barista Bakari
Wane tasiri kake ji bayyana sunayen barayin gwamnati zai yi a bangaren shari’ar wadanda ake zargi?
Fitar da sunan wanda ake zargi a kan wani laifi ko rashin fitarwa ba ya da wani tasiri a fagen shari’a. Saboda kotu na amfani n++e da shaidar da aka gabatar mata a kan wanda ake zargi sannan a ka kai ga matakin tabbatar da shi, babu ruwanta da abubuwan da a ke yayayatawa
Wadansu na korafin cewa daukacin wadanda aka fitar da sunayensu ’ya’yan jam’iyyar adawa ce me za ka ce?
Dama duk wani abu da ya danganci ’yan siyasa da aka kawo shi a lokaci irin yanzu da ake dab da fara hada-hadar zabe dole ne wadansu su danganta shi da siyasa. Sai dai idan zargin son kai ya tabbata na fifita wadansu masu laifi a kan wadansu a dalilin siyasa ko bangaranci ko addini, to lallai ba a yi adalci ba. Saboda a shari’ance akwai abin da ake kira daidaita matsayin al’umma ba tare da nuna fiffiko ba.
Akwai masu hanzarin cewa saboda kudin da ake bincike a kai sun fito ne daga ofishin Mashawar Shugaban kasa kan tsaro na wancan lokaci ne ya sa su ’yan jam’iyya mai mulki na yanzu ba sa ciki me za ka ce?
Dama ’yan siyasa ne ke wannan kurari, amma mu a mahangarmu ta shari’a duk wanda ake zargi ya kare kansa kawai maimakon ya rika korafi. Sai dai kuma idan aka duba lamarin a wannan mahangar dama ai ba yadda za a dauki kudin a bai wa ’yan adawa na wancan lokacin sai dai wadanda ake tare da su.
Me kake jin ya jinkirta kammala wannan shari’a a tsawon lokaci?
Dole a rika fuskantar tsaiko a shari’un cin hanci kamar kowace shari’a a kasar nan. Hanya guda da za ta samar da bambanci a bangaren ita ce a kafa kotuna na musamman da za su gudanar da shari’un. Saboda wannan shari’an sauki gare shi, kasancewar ga shi an ga kudin waje kaza ya karkata ya zo ga hannun wanda ake zargi, hurumin kare kai yanzu ya rage ga wanda ake tuhuma ko kuma a tasa keyarsa zuwa gidan kaso. Ba wanda ke gabatar da zargi ba ne za a ce dole sai ya tabbatar da inda a kudin yake. Amma a tsarin da ake tafiya a yanzu za a jima ba a kammala shari’ar ba kamar yadda muke gani yanzu haka inda wasu shari’u suka shafe sama da shekaru goma har yanzu ba a kammala su ba.
Ko akwai wani tasiri da hakan zai yi ga masu son tsayawa takarar zabe daga cikinsu?
Ba zai yi tasiri ba har sai idan an kai ga yanke hukunci a kotu a tabbatar da cewa an samu wanda ake tuhuman da laifi. To ko da na tara ce ta Naira daya kawai ko tsarewa na dan lokaci a kurkuku, ba dama mutum ya sake tsayawa wata takara saboda ya zamo tsohon mai laifi. Sai dai idan Shugaban kasa ne yafe masa kamar yadda ya faru a zamanin gwamnatin da ta gabata inda aka yi wa wani tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa yafiya ta kasa ko kuma mutum ya daukaka kara ba a kai ga yanke hukunci a matakin kotu ta gaba ba. Amma in baicin haka kowane irin zargi ake yi wa mutum to ba dama a ce ba zai tsaya takara ba har sai an tabbatar da cewa ya aikata abin da ake tuhumarsa a shari’ance.