✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takaddama ta barke a kan sauya kasuwar shanu a Neja

Makiyaya da masu ruwa da tsaki a harkar kasuwancin shanu a Jihar Neja sun samu kansu a cikin halin tsaka mai wuya sakamakon takaddamar da…

Makiyaya da masu ruwa da tsaki a harkar kasuwancin shanu a Jihar Neja sun samu kansu a cikin halin tsaka mai wuya sakamakon takaddamar da ta biyo bayan sauya wata kasuwar shanu da suka yi a kwanakin baya.
Aminiya ta samu labarin cewa kasuwar dabbobin wadda a baya take ci a kauyen Lambata da ke kan hanyar Suleja zuwa Minna babban birnin jihar, al’ummar Fulani makiyaya da ke kai dabbobi kai-tsaye ne, suka yanke shawarar daina kawo dabbobi kasuwar tare da umartar ’yan uwansu su rika zuwa wata sabuwar kasuwar dabbobi da suka bude a kauyen Izom wadda iat ma ke kan hanyar ta Suleja zuwa Minna, sakamakon kashe musu mutum  uku ’yan uwan juna da ake zargin wasu ’yan banga a kauyen da aikatawa ta hanyar harbinsu da bindiga kan wata jayayya a ranar kasuwa.      
Wani makiyayi da ke kai dabbobi zuwa kasuwar mai suna Abdullahi Habu ya shaida wa wakilinmu a ranar Asabar da ta gabata a  harabar kassuwar cewa, al’ummar garin na kuntata musu ta hanyar karbar haraji iri-iri ga kuma rashin mutuntasu. Shi ma Wamban Sarkin Fawan Suleja Alhaji Umaru ya ce Fulanin sun yanke shawarar ce a yayin wani babban taro da suke kira a duk lokacin da aka taba su mai suna “Fullo e Fullo” inda suka yanke shawarar komawa sabuwar kasuwar tare da barazanar daukar hukunci mai tsauri a kan duk wanda ya karya dokar, kamar yadda ya bayyana.
Bayanai sun ce Gwamnan Jihar Alhaji Sani Bello wanda ya yi ta kai kawo wajen kwantar da hankali a kan al’amarin kasancewar mazauna garin na Lambata sun kaurace wa gidajensu don gudun daukar fansa a kansu daga al’ummar Fulanin, ya samu nasarar dawo da kwanciyar hankali a garin sannan ya amince da kafa sabuwar kasuwar da ta jawo bunkasar harkoki a kauyen Izom, a yayin da harkoki a kauyen Lambata kuma wato mazaunin kasuwar a baya, suka yi rauni.
Aminiya ta samu labarin cewa ana cikin haka ne kuma, sai ga wani umarni daga gwamnatin jihar a ranar Talatar makon jiya wanda ranar cin kasuwar, inda aka bukaci jama’a su nisanci shiga kasuwar, ’yan sanda da suka yi asubanci zuwa kasuwar sun yi mata kawanya don tabbatar da cewa ba a saba wa dokar ba. Bayanai sun ce umarnin bai rasa nasaba da korafin al’ummar Lambata ga gwamnatin jihar a kan tabarbarewar hada-hada a kasuwarsu tun lokacin da masu kai shanu suka kaurace wa kasuwar. Bayanai sun ce sun bukaci gwamnatin ta sauya ranar da sabuwar kasuwar ke ci wadda ta zo daidai da tasu, ko sa samu sassaucin matsalar.
Hakan ya sa matasan garin Izom suka yi zanga-zanga a kan al’amarin inda ta kai su ga killace babbar hanyar Suleja zuwa Minna da ta wuce ta gaban kasuwar tare da kona tayoyi. Sai dai zuwan wasu shugabannin al’umma da sojoji da suka bukaci jama’a su gudanar da harkokinsu a kasuwar, kuma su bude hanyar ya kwantar da hankali tare da magance yaduwar fitinar.
Duk kokarin da wakilinmu ya yi don ganawa da shugabannin kungiyar Miyetti Allah ta kasuwar a ranar Asabar da ta gabata a harabar kasuwar bai samu nasara ba, sai dai bayanai sun ce shugabannin Fulanin sun ziyarci Gwamnan Jihar a Minna a ranar, inda suka bayyana masa rashin amincewarsu a kan sauya ranar kasuwar tare da barazanar tashi daga kasuwar zuwa yankin Abuja idan aka tirsasa musu a kan al’amarin. Gwamnan ya amince su ci gaba da harkokinsu a wajen, inji  majiyar.
A na cikin hakan ne kuma adaidai lokacin da kasuwar ta cika ta batse da misalin karfe 4 na yamma, sai hankali ya tashi inda jama’a su ka rika gudu wasu dabbobi kuma suka waste bayan kutsowar wasu jami’an tsaro na ’yan sanda cikin kasuwar  tare da harbi a iska, al’amarin ya jawo raunuka da kuma hasarar dukiya. Da a ka tuntube babban jami’in ’yan sanda na yankin Suleja ASP Abubakar Yahaya ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce ba zai yi karin bayani a kan takaddamar ba, kasancewar shi ma bai samu cikakken bayani ba zuwa lokacin.