✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taiwo Awoniyi ya koma Liberpool

Kulob din Liberpool da ke Ingila ya samu nasarar dauke dan kwallon Najeriya mai kimanin shekara 18 Taiwo Awoniyi.&nbsp Awoniyi ya koma Liberpool ne daga…

Kulob din Liberpool da ke Ingila ya samu nasarar dauke dan kwallon Najeriya mai kimanin shekara 18 Taiwo Awoniyi.&nbsp Awoniyi ya koma Liberpool ne daga kulob din Imperial Academy da ke Najeriya.
Sai dai Liberpool ta nuna za ta tura dan kwallon zuwa Jamus ne a matsayin aro don ya yi wa kulob din FSb Frankfurt kafin ya kara gogewa.
Taiwo Awoniyi ya taba yi wa kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 17 (U-17) kwallo.&nbsp Hasalima yana daga cikin ’yan kwallon da suka samu nasarar lashe kofi nm duniya a gasar cin kofin duniya na ’yan kasa da shekara 17 (U-17) da ya gudana a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a shekarar 2013.
A wata sanarwa da Awoniyi ya bayar a kafar sadarwar kulob din Liberpool (Liberpool.com) ya bayyana farin cikinsa a kan komawarsa kulob din Liberpool. Ya bayyana kulob din a matsayin kulob din da babu kamarsa a duk fadin duniya kuma tun yana yaro yake mafarkin yin kwallo a kulob din sai ga shi yanzu mafarkinsa ya zama gaskiya.
&nbsp “Zan yi kokari na ga na haskaka a kulob din FSb Frankfurt na Jamus ta yadda idan na koma Liberpool ba zan fuskanci wata matsala ba.”
Awoniyi dai yana daga cikin ’yan kwallon da koci Samson Siasia ya gayyata wadanda za su fafata a gasar wasanni ta Afirka.