✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taiwo Awoniyi ya fara haskakawa a Holland

Matashin dan kwallon Najeriya Taiwo Awoniyi ya samu nasarar zura kwallaye biyu a wasan sada zumunta da kulob dinsa NEC Nijimeyegen na Holland ya lallasa…

Matashin dan kwallon Najeriya Taiwo Awoniyi ya samu nasarar zura kwallaye biyu a wasan sada zumunta da kulob dinsa NEC Nijimeyegen na Holland ya lallasa na FC Klebe da ci 5-0 a karshen makon jiya.
Taiwo Awoniyi wanda kulob din Liberpool ya ba da aronsa ga kulob din NEC Nijimeyegen, ya ce ya yi murna da ya samu damar zura kwallaye biyu a wasansa na farko da ya fara yi a kulob din.  Ya ce yana fatar ci gaba da zura kwallaye masu yawa a raga a kakar wasa ta bana don ganin ya ci gaba da samun daukaka.
Shi dai kulob din NEC ya shirya wasan sada zumuntar ne a kokarin tunkarar kakar wasa ta bana da za su fara a gobe Asabar inda za su buga wasansu na farko da kulob din PSb Eindhoben a gasar rukunin Holland.
Ana sa ran Awoniyi dan shekara 19 zai haskaka a wasan da hakan zai kara daukaka martabarsa a idon duniya.