✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tafiye-tafiyen Shugaba Buhari: yawo ko neman arziki?

Halartar taron  kasashen Afirka da kasar Sin, wato China da aka gudanar a kasar Afirka ta Kudu a makon jiya, shi ya kawo Shugaban kasa…

Halartar taron  kasashen Afirka da kasar Sin, wato China da aka gudanar a kasar Afirka ta Kudu a makon jiya, shi ya kawo Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci kasashen duniya daban-daban har 14, bayan hawansa kan karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayun da ya gabata, yau kusan wata bakwai ke nan a inuwar jam`iyyarsu ta APC. Daga cikin tarurrukan da ya halarta, akwai na Majalisar dinkin Duniya da na Tarayyar Turai, irin su Birtaniya da Jamus da Faransa da kasar Amurka. A nan nahiyarmu ta Afirka ya ziyarci kasashen da ke makwabtaka da mu irin su Jamhuriyar Nijar da Benin da Kamaru da Chadi da Ghana, baya ga na Nahiyar Asiya, irin su Indiya da Iran da sauransu, wasu a bisa ga amsa gayyatar shugabannin irin wadancan kasashe, wasu kuwa kasancewar taro ne na kasa da kasa da ya zama wajibi a ga fuskar kowane Shugaban kasa, inda wani lokaci har jawabi zai gabatar kamar taron Majalisar dinkin Duniya.
Kafin in yi batun alfanu ko rashin alfanun wadannan tafiye-tafiye ko irin makudan kudin da masu adawa da tafiye-tafiyen suke zargin ana batarwa, bari mu duba kadan daga cikin irin mawuyacin halin da Shugaba Buhari ya karbi mulkin kasar nan, kamar yadda mafi yawan ’yan kasar da ma na kasashen waje suka sani. Akwai dai batun tabarbarewar harkokin tsaro, na rikicin ’yan ta’adda masu tada kayar baya, wato rikicin kungiyar Boko Haram da ya mamaye akasarin jihohin Arewa maso Gabas, ya kuma fantsama zuwa sauran sassan kasar nan, da annobar yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa da satar shanu, ba ya ga ta’addancin fashi da makami, wasu daga cikin  bangaren tsaro ke nan.
Akwai annobar tabarbarewar tattalin arzikin kasa da a karon farkon cikin wannan jamhuriyar, ko a tarihin kasar baki daya, aka wayi gari ma’aikatu da hukumomin Gwamnatin Tarayya da na jihohi da na kananan hukumomi, suka kasa biyan albashi  da alawus-alawus da kudin fensho da suka kama daga wata 3 zuwa 9, baya ga dimbin basussukan da ake bin gwamnatoci a ciki da wajen kasar nan, gazawar da gwamnatocin suka dora ta kacokan a kan faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya . Ga karancin wutar lantarki da ta man fetur da annobar rashin aikin yi ga matasa da uwa uba annobar cin hanci da rashawa da ta zama ruwan dare a kasar, musamman tsakanin jami’an gwamnatocin da ’yan korensu, wadanda ta wannan fanni suka sace biliyoyin Naira na kasar nan, suka kai kasashen waje, suka boye.
Ta kai fagen kafin yin babban zaben bana saboda irin wadannan matsaloli da kasar nan take ciki, masana tattalin arzikin kasa da sauran kasashen duniya da kungiyoyin sun yi ta jan hankalin mahukuntan a kan lallai akwai manyan matsalolin karayar tattalin arzikin kasa da ma na zamantakewa da za su iya afka wa kasar nan a bana, musamman kasancewar bana shekarar babban zaben kasa ce, ta ma kai ga cibiyar binciken nan ta kasa da kasa, wato Brooklyn Institute, ta yi hasashen cewa, da alamu kasar nan za ta wargaje a wannan shekarar, matsalolin da gwamnati Shugaba Dokta Goodluck Jonathan ta kekasa kasa ta yi ta musantawa, bare ta dauki matakan gyara.
Mai karatu kada ka manta a wancan lokaci duniya ta san irin mawuyacin halin da kasar nan take ciki na tabarbarewar rayuwa, su kansu shugabannin manyan kasashen duniya sun tabbatar da cewa, dorewar Shugaba  Goodluck Jonathan a kan karagar mulki bayan 29 ga watan Mayun bana, za ta iya zama annoba gare su da mutanensu, wato ma’ana za ta shafe su a kan ko dai ta rasa dan dari da kwabon da suke samu da kamfanoninsu, ko kuma ta ’yan gudun hijira da za su rika kwarara zuwa kasashen, ko kuma ta irin gudummawar da za su dauko su kawo mana a sanadiyar mun shiga cikin wani halin da ba shi da dadin a fadi  (idan wata annoba ta same mu Allah Ya kiyaye), a bisa ga haka su da kungiyoyinsu na matsin lamba da namu na nan cikin gida da sauran talakawa, suka yi hobbasa, har Allah Ya kawar da gwamnatin PDP ta Shugaba Jonathan.
Abin dubawa duk kasashe 14, da Shugaba Buhari ya ziyarta zuwa yanzu idan ka yi musu duban tsaf, za ka ga wanne ne-ba-wanne ne ba? Halartar taron Majalisar dinkin Duniya ko na kasashe masu karfin arzikin masana`antu ne ko zuwa kasar Amurka ko Birtaniya da Faransa, ko na kasar Iran ne, inda aka tattauna batun kasashe masu arzikin iskar gas ko na kasar Afirka ta Kudu da kasar Sin ta gana da kasashen Afirka inda Shugaban kasar Sin Mista di Jinping ya yi musu alkawarin ba su agajin Dala biliyan 60, don inganta harkokin tattalin arzikinsu, walau a fannin noma ko kiwon lafiya da makamantansu, baya ga alwashin da ya sha na kasarsa za ta yafe musu wasu daga cikin basussukan da take bin su. kasashe irin su Amurka da Faransa da na sauran Nahiyar Turai alkawari suka yi wa kasar nan na taimaka mata da yaki da ’yan ta’adda da maido wa kasar nan makudan kudin da wasu mukarraban gwamnatocin kasar nan suka sace suka kai musu, da ma uwa uba mika wa kasar nan irin wadancan miyagu kuma azzaluman shugabani da bincike ke sa su gudu zuwa kasashensu. Ziyarar kasashen nahiyarmu ta Afirka kuwa, bazuwar rikicin ’yan tada kayar baya kawai ta isa su sa Shugaba Buhari ya ziyarce su ko su ziyarce shi don kawo karshen tarzomar.
A ra’ayina, duk wadannan tafiye-tafiyen ina ganin suna da fa’ida ga ’yan kasa, ba kuma yawo ba ne, neman arziki da zaman lafiyar kasar nan ne da mutanenta. Ga ’yan adawa kuwa ba lallai ba ne su kalle su ta wannan fuska ba, tunda su so suke su karbe gwamnati, kasancewarsu ma da irin wannan adawar aka kore su. Ga ’yan Jam’iyyar APC da suke sukar tafiye-tafiyen irin su madugan Jam’iyyar APC Sanata Bola Ahmed Tinubu, za ta iya zama gyara kayanka.
Ba ko shakka, irin halin kuncin rayuwar da ’yan kasa suke ciki da ya dauko asali daga irin yadda wannan gwamnatin ta kankame komai ba tare da ta saki kudi  cikin kasa ba, da yadda ta dukufa wajen bincika da kwato biliyoyin kudin kasar nan da jami’an gwamnatin baya suka sace, babu abin da ya rage wa wadanda take bincika da magoya bayansu da ya wuce su rika lalubo lagon Gwamnatin Buharin, su yi ta terere da ita, a zaman ta gaza. Don haka lallai lokaci ya yi da Gwamnatin Tarayyar da na jihohi su fara bijiro da ayyukan da za su tallafa wa rayuwar mutanen kasar. Amma tafiye-tafiyen Shugaba Buhari na neman arziki ne, ba na yawo ba.